Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Habiba Adamu

  1. Yadda yara ke farautar abinci a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    A wasu wuraren kuma a wasu lokutan kasancewa a raye wani abun jin daɗi ne ga yaro - bare kuma a ce a kullum sai ya fita don samo abincin da zai ci shi da iyalinsa don kaucewa matsananciyar yunwa.

    Yayin da kayyakin agajin da ke isa zirin Gaza ke ƙara raguwa, ana samun rahotannin ƙaruwa matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki.

    Mohammed Zo'rab, ɗan shekara 11, a kullum safiya yana fita zuwa birnin Rafah da ke kudancin Gaza don cimma wani muradi.

    Ya kan ɗauke kwanon roba ya nufi makarantun da suka juye zuwa sansanonin wucin gadi a gefen tituna, inda mutane ke shan wahala kamar na shi iyalin, amma ana fatan samun wani abu don ciyar da yaran baƙi.

    Mohammed na kuma zuwa asibitoci, inda ako da yaushe ake kai waɗanda suka samu raunuka, da kuma duk inda ya san ake ɗora tukunya a murhu.

    "Idan na koma gida ga iyalina da wannan abincin suna farin ciki matuƙa kuma muna zama mu ci tare," in ji shi.

    "Wasu lokutan kuma na kan koma ba komai, kuma bana jin daɗi."

    Mohammed shi ne ɗa na fari a cikin ƴaƴa huɗu a gidansu, kuma suna zaune tare da mahaifansu a wata shemar da aka yi da leda da robobi.

    Mahaifinsa Khaled na yawo a Rafah don neman ɗan aikin da zai yi ya samu shekel biyar kuɗin zirin don sayen ƙunzugu ga jaririyarsa Howaida ƴar wata biyu.

    Mohammed ɗaya ne daga cikin dubban yaran da suka zama masu farautar abinci don ciyar da iyalansu.

    "Idan ina cikin layi mai cunkososn mutane, na ga mutum kamar ɗari a gabana, sai na kurɗa ta cikin mutane na je gaba, " yana bayanin irin hikimar da yake bi ba tare da yin faɗa ba.

    Da ya koma gida sai ya mika kwanon da waken ke ciki ga mahaifiyarsa, Samar wadda ita kuma ke raba musu. Duk ta kyamushe ba ta iya cin abinci sosai ita kanta.

    Tace tana fama da cutar sankara, abin da yasa idan ka ganta sai ka yi tsammani tana da shekara 60 ne a duniya, nan kuwa shekarunta 31 ne.

    • Dole a bar Falasɗinawa su zauna a Gaza - Blinken
    • Halin da yaran Gaza ke ciki: An raunata su kuma an kashe iyayensu
    ,,,
  2. EFCC ta ƙwato naira biliyan 60 a cikin kwana 100 - Olukoyede

    ....

    Asalin hoton, EFCC

    Shugaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta EFCC, a Najeriya, Mista Ola Olukoyede, ya ce a cikin kwana 100, ofishinsa ya samu ƙorafe-ƙorafe 5,000 da suka danganci almundahana, kuma ya samu ƙwato N60bn.

    A cewar shugaban, hukumar ta samu ƙwato wasu $10m, a wannan tsawon lokacin, kamar yadda wasu jaridun ƙasar suka ambato.

    Haka kuma a cewar shugaban EFCC, hukumar ta samu nasarar yankewa mutane 700 hukunci, kan batutuwan da suka shafi kuɗaɗen da aka ƙwato, a ƙasa da watanni huɗu.

    Inda ya ƙara da cewa haɗa hannu wuri guda da al'umma na da muhimmanci, domin a cewarsa batun na da girma sosai ta yadda hukumarsa kaɗai ba za ta iya ba, sai al'umma sun taimaka wajen bayar da bayanai idan sun ga wani abu.

    Mista Olukoyede ya bayyana cewa "idan har zan iya ƙwato naira biliyan 60 a ƙasa da kwana ɗari, me kake tunani game da yawan dukiyar da ake sacewa. "

    • Yadda EFCC ta ƙwato biliyoyin naira cikin shari'a 3,000 da ta yi nasara a 2022
    • An kai wa jami'an EFCC hari a Abuja da Imo
  3. Soja ya cinna wa kansa wuta a gaban ofishin jakadancin Isra'ila

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Washington sun ce wani soja ya cinna wa kansa wuta a gaban ginin ofishin jakadancin Isra'ila ranar Lahadi.

    Mutumin wanda ba a tantance ba, an bayyana cewa yana cikin mawuyacin hali a asibiti.

    Mai magana da yawun sojin Amurka ta tabbatar da faruwar lamarin.

    Wakilin BBC ya ce wannan dai ba shi ne karon farko ba da hakan ke faruwa a bakin ofishin jakadancin Isra'ila ba a Amurka tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin Hamas da Isra'ilar.

    Ko a watan Disambar bara wani ya aikata hakan a jihar Georgia.

    Wani bidiyo ya ɓulla a shafukan sada zumunta inda a ciki aka ga mutum na ihu da cewa "A ƴanta Falasɗinu" yayin da yake ƙonewa, kamar yadda rahoton kafofin yaɗa labaran Amurka ya ce.

    An tura jami'an sashen kwance bom zuwa wurin kan fargabar da aka yi game da wata mota da ake iya alaƙantawa da mutumin.

    Daga bisani an bayyana cewa ba a gano wasu abubuwan hadari ba a cikin motar.

    Ba a sami wani ma'aikacin ofishin jakadanci ba da ya ji rauni, kamar yadda mai magana da yawun ofishin jakadancin ta shaida wa jaridar New York Times.

    Cikin wata sanarwa, ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce ma'aikatan ofishin jakadancin ba su san mutumin ba.

    Ƴan sanda sun ce mutumin ya yi amfani da fetur sannan an ga tutar Falasɗin a wajen da lamarin ya faru.

    • An yi alla-wadai da waƙe-waƙen sojojin Isra'ila a cikin masallaci
    • Yanayi na aƙuba da ake jefa yaran da ake harbi a Amurka
  4. Ƴan kasuwan Qatar da Najeriya za su yi ganawa kan zuba jari

    ,,,

    Ofishin jakadancin Qatar a Najeriya ya tabbatar da cewa za a yi taron kasuwanci da zuba jari tsakanin ƴan kasuwar ƙasar da na Najeriya a ranar Lahadi mai zuwa.

    Tabbacin ya biyo bayan wata wasiƙa da ta ɓulla, wadda ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta aikewa Najeriya, ta ce ganawar ba za ta yiwu ba, domin babu wata yarjejeniya ta bunƙasa zuba hannun jari tsakanin ƙasashen biyu.

    Sai dai mai taimaka wa shugaban Najeriya kan harkokin watsa labarai, Malam Abdulaziz Abdulaziz ya ce ɓata gari ne suka yaɗa takardar, kuma bayanta an tabbatar da cewa za a yi ganawar.

    Inda ya ƙara da cewa ƴan kasuwan Najeriya ne suka buƙaci a yi taron don yin amfani da damar ziyarar da shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu zai kai ta kwanaki biyu a Qatar.

    A yayin ziyarar ta ranar Asabar da Lahadi mai zuwa, ana sa ran Shugaban Najeriya zai yi tattaunawa ta kololuwa da hukumomin Qatar kan yarjejeniyoyi da batutuwan tattalin arziki.

    • Bayanai kan gawurtacciyar Masarautar Qatar da ɗumbin arzikin ƙasar
    • Qatar ta aika da gidajen tafi-da-gidanka 10,000 zuwa Turkiyya da Syria
  5. An buɗe masallaci mafi girma a Afirka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An kashe fiye da dala miliyan ɗari takwas wajen gina masallacin

    Shugaban Algeriya Abdelmadjid Tebboune ya ƙaddamar da masallaci mafi girma a Afirka a birnin Algiers.

    Shi ne kuma na uku mafi girma a duniya bayan masallatai masu tsarki na birnin Makkah da Madina.

    An gina katafaren masallacin mai suna 'The Great Mosque of Algiers' kan kadada saba'in sannan mutum dubu ɗari da ashirin ne za su iya yin ibada cikin sa lokaci guda.

    Masallacin na da hasumiya mafi tsawo da ake amfani da ita wajen kiran sallah.

    An gina masallacin cikin shekara bakwai inda kuma aka kashe sama da dala miliyan ɗari takwas wajen gina shi.

    Ana sa ran za a riƙa gudanar da salloli a lokacin watan Ramadan da ake shirin farawa nan da mako biyu masu zuwa.

    Masallacin wani aiki ne na tsohon shugaba Abdelaziz Bouteflika wanda ya sauka daga kan mulki a 2019 bayan yunƙurinsa na neman wa'adi na biyar ya janyo gagarumar zanga-zanga.

    • Yunƙurin rushe masallaci mai shekara 700 a China ya jawo zanga-zanga
    • 'Dole a hukunta wadanda suka kai hari ta sama a jihar Kaduna'
    • Haji Malang: Wurin ibadar Sufaye da mabiya addinai ke jayayya a kansa a Mumbai
  6. Hedikwatar tsaro ta yi watsi da jita-jitar juyin mulki a Najeriya

    ..

    Asalin hoton, @DefenceInfoNG/X

    Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta yi fatali da zargin da wata kafar yaɗa labarai ta intanet ke yaɗawa kan iƙirarin cewa an sanya masu tsaron fadar shugaban ƙasa a shirin ko-ta-kwana bayan zarge-zargen da ake yi kan fargabar kifar da gwamnati.

    Wata sanarwa da muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron, Brigadiya Janar Tukur Gusau ya ce an ankarar da su game da wani rahoto da aka wallafa a intanet a ranar 25 ga watan Fabarairun 2024 da ke iƙirarin cewa masu tsaron fadar shugaban ƙasa na cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon wasu alamu da ke janyo fargabar yin juyin mulki a Najeriya.

    "Rahoton ya kuma ce zargin ya janyo yin taron gaggawa tsakanin shugaba Bola Tinubu da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa.

    Hedikwatar tsaron ta ƙaryata labarin inda ta ce an tsara masu tsaron fadar shugaban ƙasa su kare fadar da kuma babban birnin tarayya da kewayenta.

    A cewar hedikwatar tsaron, a kullum jami'an tsaron da ke fadar shugaban ƙasa na cikin shiri kodayaushe domin sauke nauyin da aka rataya a wuyansu.

    Hedikwatar ta kuma yi waiwaye kan yadda babban haftsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya sha nanata ƙudurin jami'an sojin Najeriya na kare martabar dimokradiyyar ƙasar.

    A don haka hedikwatar tsaron ta yi kakkausar suka kan zargin inda ta buƙaci jama'a su yi watsi da shi.

    Hedikwatar ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukan mataki kan jaridar da ta wallafa labarin saboda mataki ne na rashin nuna kishin ƙasa.

    • Gargaɗin DSS ga NLC da fatalin cire tallafin lantarki
    • An jahilci manufar samar da ƴansandan jihohi a Najeriya - Uba Sani
    • Matsalar hare-haren ƴan bindiga ta ɗauki sabon salo a jihar Zamfara
  7. Ƙungiyar sanatocin Arewacin Najeriya za ta tura tawaga Nijar

    ,,,

    Ƙungiyar sanatocin jihohin Arewacin Najeriya ta ce za ta tura wakilanta jamhuriyyar Nijar, domin ganawa da shugabannin mulkin sojin ƙasar, kan yadda za a mayar da mulki ga farar hula.

    Ƙungiyar ta ɗauki wannan matakin ne, bayan sanar da janye takunkuman da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙabawa Nijar da Mali da kuma Burkina Faso waɗanda sojoji ke jan ragamar mulkin su.

    Kakakin ƙungiyar sanatocin, Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce ƙungiyar zata tura tawagar ba tare da ɓata lokaci ba.

    Janye takunkuman da ECOWAS ta yi zai sake buɗe harkokin cinikayya da zai taimaka wajen warware matsalar ƙarancin abinci da magunguna da sauƙaƙa al'amura ga ƙasashen na Najeriya da Nijar da ke makwabtaka da juna.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wata ƙungiyar malaman mususlunci ta Najeriyar ta yi kira da sojoji a Nijar da Mali da Burkina Faso da su koma cikin ƙungiyar ta ECOWAS.

    • Abun da ya sa Ecowas ta ɗage wa Nijar da Mali da Burkina Faso takunkumai
    • Yaƙi ba mafita ba ne ga Nijar a rikicinta da su Ecowas - Masana
    • Mece ce makomar tsaron Nijar idan dakarun Faransa suka fice?
  8. Assalamu Alaikum

    Daga nan BBC Hausa muke yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon yinin yau domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu.