Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza

  1. Ba gudu ba ja da baya a sauye-sauyen da za mu kawo – Tinubu

    ...

    Asalin hoton, BOLA TINUBU/FACEBOOK

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ganin an aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki a ƙasar duk da ƙalubalen da mutane da dama ke fuskanta.

    Shugaban ya kare sauye-sauyen gwamnatinsa, yana mai cewa babu gudu babu ja da baya.

    A yayin ganawarsa da wata tawaga daga ƙungiyar kasuwanci ta CCA ƙarkashin jagorancin shugabarta Florizelle Liser, shugaba Tinubu ya jaddada aniyarsa ta ganin ya cimma burinsa na bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da kuma kawo kwanciyar hankali a ƙasar.

    A yayin rantsar da shi ne Tinubu ya bayyana cire tallafin man fetur wanda ya kai ga hauhawar farashin man fetur da sauran wasu sauye-sauye da suka janyo darajar kudin ƙasar naira ta yi hasarar darajarta.

    Waɗannan sauye-sauyen dai sun haifar da tsadar rayuwa a Najeriya irin wadda ba a taɓa ganin irinta ba abin da ya haddasa zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin ƙasar da yajin aiki da dai sauransu.

    Amma duk da waɗannan ƙalubale da kuma abubuwan da ke faruwa, Tinubu ya ce ba zai ja da baya ba.

    “Na yi farin ciki da cewa ƙungiyar CCA na sha’awar sassa daban-daban na tattalin arzikin Najeriya. Muna cikin tsaka mai wuya da fuskantar ƙalubale na sake fasalinmu. Muna da fata, babu shakka, amma ba za mu koma ba,” in ji Tinubu ta bakin mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale.

    "Muna fuskantar ƙalubale, kuma mun yi imanin za mu shawo kan waɗannan ƙalubalen. Ina da hali na 'zan iya cimma wani abu' wanda dole ne a fassara shi zuwa halin wajibi na cimma abin da nake so'. Muna da tawaga mai kyau da kuma tasiri, kuma dole ne mu ci gaba da mai da hankali don cimma burin da aka sa a gaba,” in ji shugaban Najeriyar.

    Tinubu ya sha yin kira ga al'ummar ƙasar da su yi hakuri domin a bar sauye-sauyen nasa su yi tasiri, yana mai cewa za su taimaka wajen jawo jarin ƙasashen waje, amma matakan nasa na ci wa ‘yan Najeriya tuwo a ƙwarya.

    Tinubu ya kuma yaba da nasarar da aka samu a kwanan baya na samar da wayar ƙarƙashin teku mai tsawon kilomita 45,000 da ta kawo intanet a jihar Akwa Ibom, wanda zai haɗa yankin Kudu-maso-Kudancin Najeriya da Turai da sauran sassan Afirka.

    Shugaba Tinubu ya bayyana muhimmancin wannan nasarar, inda ya bayyana cewa idan aka samar da ingantattun manufofi da haɗin gwiwa da azama, Najeriya za ta iya shawo kan matsalolin da ta daɗe tana fuskanta.

    Ya tabbatar da ƙudurinsa na samar da yanayi mai ba da damar kasuwanci don bunƙasa, tare da mai da hankali kan saka hannun jari a muhimman sassa kamar su noma da makamashi da lafiya da fasaha.

    “Za mu ƙara kaimi kan harkar tsaro da saka hannun jari a fannin ilimi, domin mun yi imanin cewa ilimi shi ne babban makamin yaƙi da talauci. Muna maraba da abokan hulɗa kamar CCA, kuma za mu ƙarfafa haɗin gwiwarmu don cimma burinmu,” inji shugaban.

    A nata martanin, CCA ta bayyana ƙudurinta na tallafawa ci gaban tattalin arzikin Najeriya ta hanyoyin da gwamnatin shugaba Tinubu ta ba da fifiko.

    • Har yanzu zafin shan kaye ne ke damun Atiku - Tinubu
    • Sa'insar Atiku da Tinubu, rufe kasuwannin canji a Abuja da Kano
    • Babu hujjar da ke nuna cewa takardun digirin Tinubu na bogi ne
  2. Yadda gobara a dogon gini ta halaka mutum huɗu a Spaniya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin bayar da agajin gaggawa sun ce aƙalla mutum huɗu ne suka mutu, wasu 19 suka yi ɓatan dabo bayan wata gobara da ta tashi a wani dogon gini a birnin Valencia da ke Spaniya.

    Gobarar ta laƙume ginin mai hawa 14 a Campanar inda kuma ta yaɗu zuwa wani gini mai maƙwabtaka.

    Masu kashe gobara na ta kai kawo domin kuɓutar da mutane da ke cikin ginin.

    Gine-ginen dai na da ɗakuna 138 kuma gida ne ga mutum 450, kamar yadda jaridar El Pais ta ruwaito.

    Kimanin mutum 14, ciki har da jami'an kwana-kwana shida da wani taro ne suka jikkata.

    Fiye da jami'an kashe gobara 20 ne suka yi faɗi tashin kashe wutar wadda ke ruruwa saboda kaɗawar iska.

    An dai buƙaci mutane su kaucewa wurin da lamarin ya faru.

    • Wasu ƙasashen duniya na fama da tsananin zafin da ba a taɓa yi ba
    • Yadda wasu 'yan Najeriya suka makale a bindin jirgin ruwa zuwa Spain
    • Gobara ta ƙona kimanin shaguna 50 a kasuwar Singa
  3. Shugaban Senegal ya ce zai sauka daga kan mulki a watan Afrilu

    ..

    Asalin hoton, AF

    Shugaban Senegal Macky Sall ya ce zai sauka daga shugabancin ƙasar a ƙarshen wa'adinsa a ranar 2 ga Afrilu, sai dai bai bayyana ranar da za a gudanar da zaɓen wanda zai gaje shi ba.

    Mr Sall dai na fuskantar matsin lamba ya sanar da ranar zaɓen sabon shugaban ƙasa bayan yunƙurin ɗage zaɓen a farkon watan nan.

    Matakin ya jefa Senegal cikin rudanin siyasa – ƙasar da ake ganin ta fi tsayuwa da ƙafarta ta fuskar dumokuradiyya a Afrika.

    A wani jawabi da ya gabatar ta talabijin, Mr Sall ya gaza cika fatan al'ummar Senegal na saka ranar da za su kaɗa ƙuri'a kan wanda zai gaje shi.

    Ya kuma yi alƙawarin ya sauka daga shugabanci bayan cikar wa'adin mulkinsa. A cewarsa, zai duba yiwuwar sakin ɗan hamayyar ƙasar Ousmane Sonko wanda tsare shi ya janyo zanga-zangar gama-gari a shekarar da ta gabata.

    Mr Sall ya ce ba ya tunanin za a iya gudanar da zaɓe kafin 2 ga watan na Afrilu lokacin da ya tsara zai yi murabus.

    Babu masaniya kan wanda zai jagoranci ƙasar na wucen gadi. Masu sukar Mr Sall sun zarge shi da ƙoƙarin ƙin sauka daga kan mulki. Akwai fargabar da ake cewa rikicin siyasa a Senegal na iya dagula lamura a yankin da ya sha fama da juyin mulki cikin shekara huɗu da ta gabata.

    • Yan takara a Senegal sun buƙaci a yi zaɓe cikin mako 6
    • Ɗage zaɓen Senegal ya saɓa wa ƙundin tsarin mulkin ƙasar - kotu
    • Senegal na dab da shiga ruɗani bayan ɗage zaɓe
  4. Barka da Hantsi

    Barkan mu da shigowa shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a wannan hantsi.

    Da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya kuma a yau ma za mu kawo muku rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Sai ku tara.