Shugabannin kasashen kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma, Ecowas za su yi taron gaggawa a gobe Asabar domin
tattauna muhimman batutuwan da suka shafi makomar kungiyar, a karo na biyu
bayan kasashen Nijar da Mali da Guinea da kuma Burkina Faso sun sanar da
ficewarsu daga kungiyar, yayin da a bangare guda kuma shugaban kasar Senegal,
Macky Sall ya dage zaben kasar.
Taron shugabannin na zuwa ne daidai lokacin da tsohon shugaban Najeriya na mulkin
soji kuma shugaba ɗaya tilo da ya rage cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar ta Ecowas, Janar Yakubu
Gowon, ya yi kiran gaggauta ɗage duk wani takunkumin da aka ƙaƙaba wa
ƙasashen Guinea da Burkina Faso da Mali da Nijar.
Ana sa ran taron kungiyar zai mayar da hankali wajen tunkurar matsalolin da
suka shafi makomar kungiyar.
Taron, kamar yadda wata sanarwar da kungiyar ta wallafa
a shafinta na intanet ta nuna, taro ne na musamman da ya kunshi `yan kwamitin
shiga-tsakani da majalisar tsaro a matakin ministoci, wanda sanarwar ta ce za
su yi zama da nufin tattaunawa a kan halin da yankin Afirka ta yamma ya samu
kansa a ciki ta fuskar tsaro da wasu matsaloli da suka jibanci siyasa.
Tun a ranar 28 ga Janairu ƙasashen Mali da
Burkina Faso da Kuma Nijar suka sanar da aniyar ficewa ƙungiyar Ecowas.
Kuma daga baya ƙasashen uku da dukkaninsu
sojoji ne ke jagorantarsu bayan kifar da gwamnatin farar hula, sun jaddada
matakin ficewa daga Ecowas kafin taron ƙungiyar.
Mali da Burkina Faso da Nijar sun fice ne
sakamakon takunkuman kariyar tattalin arziki da Ecowas ta kakaba ma su bayan
juyin mulki da sojoji suka yi.
Ƙasashen
Mali dai nsun yi zargin cewa babu abin da zamansu a Ecowas
ya tsinana musu. Kuma yanzu dole sai Ecowas ta saurari wasu bukatun shugabannin
sojin ƙasashen idan har tana son su dawo cikin ƙungiyar.
Masana harkokin diflomasiyya na ganin ya kamata shugabannin kungiyar su yi kaffa-kaffa, su mai da hankali wajen lalamar 'ya'yan kungiyar idan ba haka ba garin gyaran gira a rasa ido.
Haka
nan ma, masu sharhi na ganin cewa hakan zai ƙara kawo barazana tare da daƙushe
yunƙurin ƙungiyar na magance matsalolin yawaitar juyin mulki da yankin ke
fuskanta da kuma barazanar zaman lafiya da haɗin kan ƙasashen ƙungiyar 15.