Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo karshen labarai da rahotonin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
CBN na son kwastam ta daidaita chanjin dala a kudin fito da na sayo kaya daga waje
Asalin hoton, CBN
Babban Bankin Najeriya CBN ya yi kira ga hukumar hana fasa kauri ta kasar, wato Kwastam ta daidaita chanjin farashin dala da take ake bai wa masu sayo kaya daga waje da kudin fiton da hukumar ke karba a hannun maso sayo kayan.
Cikin wata sanarwa da CBN din ya fitar ranar Juma'a mai dauke da sa hannun daraktan sashen kasuwanci da chanji na bankin, Hassan Mahmud, bankin ya ce yawan kudin fiton da hukumar kwastam ke karba a hannun maso sayo kaya na kara haddasa tashin farashin kayayyaki a kasar.
Lamarin da Babban Bankin kasar ya ce na kara ta'azzara tsadar kayayyaki a kasuwannin kasar.
CBN din ya kuma bukaci hukumar kwastam ta rika amfani da chanjin da aka bai wa masu sayo kaya don karbar kudin fito a hannun masu sayo kayan.
An dauki matakin ne da nufin magance sabanin da ake yawan samu na sabunta bayanai da kwastam din ke yi a shafinsa dangane da chanjin kudin kasashen waje.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Hukumomin Rasha na barazanar binne Navalny a gidan yari - Makusantansa
Asalin hoton, Reuters
Mai magana da yawun jagoran adawar Rasha Alexei Navalny, ta ce mahukunta na musu barazar cewa za a binne gawar jagoran adawar Rashar a gidan yarin da mutu.
Kira Yarmysh, ta ce an bai wa mahaifiyar Mr Navalny wa'adin sa'o'i uku domin ta amince a binne shi a asirce ko kuma a gidan kason da ya mutu.
Mai magana da yawun Mr Navalny, ta ce Ludmila Navalny, ta ki yar da a yi wata tattaunawa da ita, sannan kuma ta bukaci a bata gawar danta.
A jiya Alhamis ne mahaifiyar Mr Navalny, ta ce an bar ta ta ga gawar dan nata baya shafe kusan mako guda da sanar da mutuwarsa.
An kammala rajistar masu zabe a Afirka ta Kudu
Kasar Afirka ta Kudu za ta bai wa 'yan kasar hutu a ranar 29 ga watan Mayu domin kada kuri'unsu a babban zaben kasar.
Shugaban kasar Cyril Ramaphosa ne ya bayyana hutun bayan tabbatar da ranar zaben.
Hakan na nufin cewa yau a an kawo karshen rajistar masu zabe a kasar.
Sai dai akwai fargabar cewa miliyoyin wadanda suka cancani kada kuri'a ba su samu yin rajistar a kan lokaci ba.
Cutar kwalara mafi muni a Zambiya ta kashe kimanin mutum 700
Asalin hoton, ReutersCopyright
Kungiyar Likitoci ta Duniya, 'Médecins Sans Frontières' (MSF) ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara ya kai kimanin 700
Cutar - wadda ta barke a kasar tun cikin watan Oktoban bara - ita ce kwalara mafi muni da ta barke a kasar a tarihi.
Cutar ta fara ne daga Lusaka babban birnin kasar sai kuma daga baya ta bazu zuwa sauran lardunan kasar, inda fiye da mutum 19,000 suka kamu.
MSF ta ce ana iya saurin shawo kan cutar kwalara ta hanyar karin ruwa, to sai dai cutar kan kashe mutum idan bai samu kulawar da ta dace cikin hanzari ba.
Shan ruwan da ya gurbace na daga cikin abubuwan da ke haddasa cutar, don haka samun taftataccen ruwan sha na da matukar muhimmanci wajen dakile yaduwar cutar.
EFCC ta kama mutum 27 kan zargin zamba ta intanet a Bauchi
Asalin hoton, X/EFCC
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Najeriya ta EFCC ta kama mutum 27 bisa zarginsu da aikata zamba ta intanet a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin kasar.
Cikin wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce jami'an hukumar shiyar Gombe ne suka kama mutanen a ranar Alhamis 22 ga watan Fabrairu.
Hukumar ta ce jami'anta sun kama mutanen ne a wani otal da ke garin Yelwa a jihar Bauchi, bayan samun bayanan sirri kan zargin mutanen da aikata laifukan intanet.
Asalin hoton, X/EFCC
EFCCn ta kuma kwato wasu abubuwa a wajen mutanen da suka hada da karamar mota kirar BMW, da wayoyin iphone da kwamfutoci da sauran manyan wayoyi.
Hukumar ta ce za ta gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.
Ecowas za ta yi taro a Abuja kan siyasa da tsaron yankin Yammacin Afirka
Asalin hoton, Ecowas/Youtube
Shugabannin kasashen kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma, Ecowas za su yi taron gaggawa a gobe Asabar domin
tattauna muhimman batutuwan da suka shafi makomar kungiyar, a karo na biyu
bayan kasashen Nijar da Mali da Guinea da kuma Burkina Faso sun sanar da
ficewarsu daga kungiyar, yayin da a bangare guda kuma shugaban kasar Senegal,
Macky Sall ya dage zaben kasar.
Taron shugabannin na zuwa ne daidai lokacin da tsohon shugaban Najeriya na mulkin
soji kuma shugaba ɗaya tilo da ya rage cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar ta Ecowas, Janar Yakubu
Gowon, ya yi kiran gaggauta ɗage duk wani takunkumin da aka ƙaƙaba wa
ƙasashen Guinea da Burkina Faso da Mali da Nijar.
Ana sa ran taron kungiyar zai mayar da hankali wajen tunkurar matsalolin da
suka shafi makomar kungiyar.
Taron, kamar yadda wata sanarwar da kungiyar ta wallafa
a shafinta na intanet ta nuna, taro ne na musamman da ya kunshi `yan kwamitin
shiga-tsakani da majalisar tsaro a matakin ministoci, wanda sanarwar ta ce za
su yi zama da nufin tattaunawa a kan halin da yankin Afirka ta yamma ya samu
kansa a ciki ta fuskar tsaro da wasu matsaloli da suka jibanci siyasa.
Tun a ranar 28 ga Janairu ƙasashen Mali da
Burkina Faso da Kuma Nijar suka sanar da aniyar ficewa ƙungiyar Ecowas.
Kuma daga baya ƙasashen uku da dukkaninsu
sojoji ne ke jagorantarsu bayan kifar da gwamnatin farar hula, sun jaddada
matakin ficewa daga Ecowas kafin taron ƙungiyar.
Mali da Burkina Faso da Nijar sun fice ne
sakamakon takunkuman kariyar tattalin arziki da Ecowas ta kakaba ma su bayan
juyin mulki da sojoji suka yi.
Ƙasashen
Mali dai nsun yi zargin cewa babu abin da zamansu a Ecowas
ya tsinana musu. Kuma yanzu dole sai Ecowas ta saurari wasu bukatun shugabannin
sojin ƙasashen idan har tana son su dawo cikin ƙungiyar.
Masana harkokin diflomasiyya na ganin ya kamata shugabannin kungiyar su yi kaffa-kaffa, su mai da hankali wajen lalamar 'ya'yan kungiyar idan ba haka ba garin gyaran gira a rasa ido.
Haka
nan ma, masu sharhi na ganin cewa hakan zai ƙara kawo barazana tare da daƙushe
yunƙurin ƙungiyar na magance matsalolin yawaitar juyin mulki da yankin ke
fuskanta da kuma barazanar zaman lafiya da haɗin kan ƙasashen ƙungiyar 15.
Matakai takwas da za ku bi don sayen shinkafar kwastam mai rahusa
Asalin hoton, Facebook/Nigeria Custome
Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya kwastom ta fara sayar da shinkafa kan farashin mga 'yan kasar.
Matakin na daga cikin ayyukan rage radadin tattalin arzikin da 'yan NAjeriya ke fuskanta
Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Maiwada ya shaida wa BBC cewa shinkafar da hukumar ke sayarwa, shinkafa ce da jami'an hukumar suka kama a lokacin da aka shigar da ita kasar ba bisa ka'ida ba.
Ya ce hukumar ta kai shinkafar kotu inda suka samu sahalewar kotu domin sayar da ita ga talakawan kasar.
Abdullahi Maiwada ya ce an fara sayar da sayar da shinfara ne a yau Juma'a a jihar Legas, a matsayin gwaji kafin daga baya hukumar ta fadada aikin zuwa sauran jihohin kasar da take da irin wadannan kaya da ta kama.
Kakakin hukumar ya ce suna sayar da buhu mai nauyin kilogiram 25 na shinkafar a kan kudi naira 10,000.
Matakan da hukumar ke bi wajen sayar da shinkafar
Abdullahi Maiwada ya ce hukumar na bin wasu matakai na tantancewa kafin ta sayar da shinkafar ga al'umma kamar haka.
Amfani da NIN - Ya ce hukumar na amfani da lambar da ke jikin katin dan kasa ta NIN wajen tantance mutanen da take sayar wa shinkafar, don haka dole sai wanda ke da lambar NIN zai samu damar sayenta.
Mutanen da ke kusa da inda hukumar ta kama kaya- Abdullahi Maiwada ya ce hukumar na sayar da shinkafar ne kawai ga mutanen da ke kusa da inda ta kama shinkafar, ''don haka duk mutmin da ya zo daga nesa ba zai samu sayen shinkfara ba'', in ji shi.
Masu sana'ar hannu - Kakakin hukumar Kwastam din ya ce daga cikin rukunin mutanen da hukumar ke sayar wa shinkafar su ne masu sana'ar hannu. Ya ce an yi hakan ne domin tallafa musu wajen bunkasa sana'o'insu.
Malaman makaranta - Hukumar ta ce malaman makaranta na daga cikin rukunin mutanen da za su amfana da sayen da sayen shinkafar da hukumar kwastam ke sayarwa.
Masu sharar titi - Abdullahi Maiwada ya kara da cewa su ma mutanen da ke sharar titi na daga cikin rukunin mutae da hukumar ba domin sayar musu da shinkafar.
Mutanen da suka fi tsananin bukata - Kakakin hukumar ya shaida wa BBC cewa dama makasudin sayar da shinkafar shi ne rage wa al'immar radadin tsadar rayuwa da ';yan kasar ke fuskanta, don haka ya ce suka fi bayar da fifiko kan mutanen da ke cikin tsananin bukata.
Mata - Wasu rukunin mutanen da za su amfana da shinkafar kwastam din mai cike da rahusa su ne mata, musamman marasa karfi, wadanda ke rike da kananan yara.
Kungiyoyin addini - Kungiyoyin addini na daga cikin al'umomin da za su amfana da wannan sayar da shinkafa da hukumar kwastam ke yi, kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook.
Hukumar ta kuma gargadi 'yan kasar da ke da aniyar sayar da shinkafar ga 'yan kasuwa, da su guji yin hakan.
Abdullahi Maiwada ya ce duk wanda ya yi haka zai fuskanci fushin hukumar, sannan kuma ya ce hukumar za rika sanya idanu a kasuwanni domin ganin ko 'yan kasuwa za su sayi shinkafar domin sayarwa.
Hotunan yadda hukumar kwastam ke sayar da shinkafa a farashi mai rahusa
Asalin hoton, Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kaddamar da sayar da kayan abincin da aka kama musamman shinkafa a farashi mai rahusa a jihar Legas.Hukumar ta ce ta yi hakan ne domin sauƙaƙa wa al'ummar Najeriya halin ƙunci da suke ciki.
Asalin hoton, Nigeria Customs Service
Asalin hoton, Nigeria Customs Service
Asalin hoton, Nigeria Customs Service
Asalin hoton, Nigeria Customs Service
Ƴan adawa a Senegal sun yi fatali da tayin shugaban ƙasar kan taron tsayar da ranar zaɓe
Jam'iyyun adawa a Senegal sun yi fatali da shiga tattaunawar da shugaban ƙasar Macky Sall ya gabatar ta yin taron tsayar da sabuwar ranar zaɓen shugaban ƙasar bayan da ya sanar da ɗage zaɓen a farkon wannan wata.
Da alama dai rikicin siyasar ƙasar Senegal bai kare ba bayan da ƴan takarar shugaban kasa 16 daga cikin 19 na adawa suka ce ba za su shiga tattaunawar ba, wadda aka shirya gudanarwa a farkon mako mai zuwa.
Kungiyoyin farar hula da dama su ma sun yi fatali da batun tattaunawar.
Wannan ya biyo bayan jawabin da shugaba Macky Sall ya yi ta talabijin a daren ranar Alhamis, inda ya yi alƙawarin yin murabus a ƙarshen wa'adinsa, ranar 2 ga Afrilun 2024, sai dai bai bayyana sabuwar ranar da za a gudanar da zaɓen ba.
Mista Sall, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Abuja domin halartar wani babban taro na kungiyar ECOWAS, na fuskantar matsin lamba kan ya sanya sabuwar ranar zaɓe, tun bayan da majalisar ƙoli ta shari'a ta ƙasar ta bayyana ɗage zaɓen a matsayin haramtacce.
Yunƙurin ɗage zaɓen ya samu kakkausar suka daga ƙasashen duniya, waɗanda ke kallon Senegal a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe masu tafiyar da mulkin dimokuradiyya kan tsari mai kyau, yankin da ake fama da juyin mulkin a yankin Yammacin Afirka.
Kotu ta bayar da belin tsohon gwamnan Kwara
Asalin hoton, Abdulfatah Ahmed/Facebook
Babbar kotun tarayya da ke brnin Ilorin a jihar Kwara ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar, Abdulfattah Ahmed kan kudi naira miliyan 50 tare da sharadin mutum biyu da za su tsaya masa wadanda suka mallaki fili a birnin Ilorin.
Haka kuma cikin sharadin belin tsohon gwamnan zai ajiye fasfo dinsa na tafiye-tafiye da sauran sharuda.
Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan ne a ranar Juma’a, biyo bayan gayyatar da hukumar ta yi masa domin amsa tambayoyi a ranar Litinin.
Sai dai kuma an hana ‘yan jarida shiga kotun.
Hukumar EFCC ta kama Ahmed a ranar Litinin inda ake yi masa tambayoyi kan hada-hadar biliyoyin naira a lokacin da yake gwamnan jihar.
Ahmed ya kasance gwamnan jihar Kwara tsakanin watan Mayun 2011 zuwa Mayu 2019 kafin ya mikawa Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq.
An taba yi masa tambayoyi a watan Mayun 2021 a hedikwatar EFCC da ke unguwar Jabi a Abuja, babban birnin kasar, kan zargin karkatar da kuɗade kusan Naira biliyan 9 daga asusun jihar.
Kotu ta tursasa a sauya sunan zakunan da aka yi wa laƙabi da abin bautar Hindu
Asalin hoton, Getty Images
Kotu a ke Indiya ta umarci wani gidan yari da ke jihar West Bengal ya canza wa wasu
zakuna suna bayan wata ƙungiyar mabiya addinin Hindu ta yi koken cewa hakan saɓo
ne ga addininsu.
Zakanya
ta farko, tun asali an laƙaba mata suna wanda ya samo asali daga abar bautar
mabiya addinin Hindu da ake kira Sita, sai kuma zakin da ake kira Akbar wanda
shi ma ya samo asali daga wani jagora na daular Mughal a ƙarni na 16.
Ƙungiyar
mabiya Hindu ta Vishwa Hindu Parishad ce ta ƙalubalanci hakan a kotu, kan cewa sunan
da aka bai wa zakanyar saɓo ne a addinin Hindu.
A
ranar Alhamis, kotun ta ce a daina sanya wa dabbobi sunayen abin bautar Hindu
ko na annabawan Musulunci ko manyan malaman Kiristoci da na mutanen da suka lashe
kyautukan Nobel da kuma na ƴan rajin ƙwatar ƴanci.
Hatsaniya ta janyo dakatar da harkokin kasuwanci a Legas
Harkokin kasuwanci sun tsaya cak a kasuwar Oluwole da ke Ogba a ƙaramar hukumar Ojodu da ke jihar Legas sakamakon wani rikici da ya ɓarke tsakanin Yarabawa da Hausawa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rikicin ya soma ne ranar Alhamis da daddare lokacin da wani mutum da ake kira Abbey ya sasanta taƙaddama tsakanin wasu Hausawa biyu da ake zargin wani mutum da ba a san ko wane ne ba ya daba masa wuƙa tare da yasar da shi kwance cikin jini.
A cewar shaidu, Abbey ya yi ta zubar da jini kafin daga bisani rai ya yi halinsa lamarin kuma ya janyo faɗan ramuwar gayya tsaknin Yarabawa da Hausawan yankin.
Harin ya janyo lalata kayan abinci da na gwari da Hausawa ke sayarwa.
A cewar bayanai, akwai jami'an ƴan sanda da ke rangadi a kasuwar a ƙoƙarin kwantar da tarzoma.
Sai dai ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin ba.
Biden ya sanar da ƙarin takunkumai fiye da 500 kan Rasha
Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta sanar da ƙaƙaba takunkumai fiye da ɗari biyar a kan Rasha saboda mamayar da ta yi wa Ukraine da kuma mutuwar madugun adawar ƙasar, Alexei Navalny.
Takunkuman sun shafi mutanen da ke da hannu a tsare Navalny da kuma yaƙin da Rasha take, kamar yadda Shugaba Joe Biden ya sanar.
Za a sa takunkumin hana fitar da kaya kan kusan kamfanoni ko mutane 100.
Tarayyar Turai ta kuma sanar da wasu takunkuman da Rasha ta mayar da martani ta hanyar haramta wa jami'an Tarayyar Turai shiga ƙasarta.
Babu ƙarin bayani kan tasirin da takunkuman za su yi a kan tattalin arzikin Rasha.
Cikin wata sanarwa, Shugaba Biden ya ce takunkuman za su tabbatar shugaban Rasha Vladmir Putin ya ɗanɗana kuɗarsa saboda kama-karyar da yake a cikin gida da kuma fito na fiton dayake da ƙasashe.
Takunkuman na zuwa ne mako ɗaya tun mutuwar fuju'a da Navalny a wani kurkuku da ke yankin Arctic mai tsananin sanyi. Mista Biden ya ce babu tantama kan zargin shugaban na Rasha.
Suna kuma zuwa a jajiberin cika shekara biyu na mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
"Shekara biyu da ta gabata, ya yi ƙoƙarin ɓatar da Ukraine daga taswira. Idan Putin bai ɗanɗana kuɗarsa ba saboda mutuwarsa da ɓarnar da ya yi, zai ƙara ƙaimi ne," in ji Mista Biden cikin wata sanarwa.
Tarayyar Turai ta sanar da sa takunkumi kan kusan kamfanoni da mutane ɗari biyu da ake zargin sun taimaka wa Rasha wajen samun makamai da kuma hannu a garkuwa da yaran Ukraine, wani abu da Rasha ta musanta.
A martaninta, ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce ta faɗaɗa jadawalin sunayen jami'an EU da ƴan siyasar da ta haramta wa shiga ƙasarta.
Shugaba Ivory Coast ya yi afuwa ga fursunonin da aka kulle saboda rikicin zaɓe
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Fiye da mutum dubu uku aka kashe a rikicin da ya ɓarke bayan zaɓe kamar yadda ƙungiyar Human Rights Watch ta bayyana
Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya yi wa fursuna 51 afuwa waɗanda aka tsare su saboda lifin tayar da hatsaniya bayan zaɓen da aka yi a ƙasa a shekarar 2010.
Ivory Coast ta tsunduma cikin tashin hankali bayan da Laurent Gbagbo ya ƙi amincewa ya miƙa mulki ga Mista Ouattara wanda hukumar zaɓe ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓe karo na biyu mai cike da taƙaddama.
Lokacin rikicin da aka soma daga Nuwamban 2010 zuwa Afrilun 2011, fiye da mutum dubu uku ne aka kashe sannan mata sama da 150 aka ci zarafinsu kamar yadda wani rahoto da ƙungiyar Human Rights Watch ta wallafa.
Cikin fursunonin da aka yi wa afuwa akwai Janar Brunot Dogbo Ble wanda babban jami'in soji ne a ƙarƙashin Mista Gbagbo.
Ya jagoranci wata kungiyar tsaro ta Republican Guard da aka zarga da kashe-kashe da dama.
Matakin na yi wa mutanen afuwa wani ɓangare ne na ƙudurin shugaba Ouattara na yin aiki tuƙuru domin tabbatar da zaman lafiya, in ji kamfanin dillancin labarai na AFP.
Liberia: Kurkukun da fursunoni ke fuskantar karancin abinci da kayan sa wa
Abin da ya sa fursunoni ke yunkurin tserewa daga gidajen yarin Najeriya
An kama ɗaliban Najeriya kan zargin zamba ta intanet
Asalin hoton, EFFC/X
Hukumomi a Najeriya sun kama mutum 50 da ake zargi da aikata almundahana ta intanet, akasarinsu ɗaliban jami'ar jihar Kwara.
Hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa arzikin ƙasa zagon ƙasa cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis ta ce an kama ɗalibai 48 da wasu mutum biyu a maɓoyansu daban-daban sakamakon kwanakin da aka shafe ana sa ido.
EFCC ta ce ta gano wasu motocin ƙasaita tara sai kwamfutocin laptop 24 da kuma wayoyin hannu daban-daban a hannun mutanen da ake zargi, waɗanda aka ce suna rayuwa ta facaka.
Hukumar ta kuma ce jami'anta sun bazama domin fitar da ƙasar daga ƙangin rashawa da sauran miyagun laifuka da ƴan yahoo ke yi.
Asalin hoton, EFCC/X
Hukumar a shafinta na X ta wallafa hotunan kayayyakin da ta ƙwace daga hannun mutanen da ake zargi da tafka almundahanar da intanet.
A cewar EFCC, ba da daɗewa bane za a gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
FBI ta kama wasu 'yan Najeriya da laifin zamba a intanet
EFCC ta gano makarantar koyar da zamba ta intanet
Mai rajin kare ƙabilar Yarabawa Sunday Igboho ya koma Najeriya
Asalin hoton, FACEBOOK/SUNDAY ADEYEMO IGBOHO FOUNDATION
Mai rajin kare ƙabilar Yarabawa a Najeriya, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho ya koma Najeriya kusan shekara uku bayan da ya fice daga ƙasar zuwa jamhuriyar Benin.
Wata sanarwa da kakakin Igboho, Olayomi Koiki ya fitar ta tabbatar cewa mai rajin kare ƙabilar ta Yarabawa yana Najeriya domin halartar jana'izar mahaifiyarsa da za a yi a Igboho da Ibadan.
A wani bidiyo da aka wallafa a ntanet, an ga Mista Adeyemo yana ɗaga wa mutanen garin Igboho hannu yayin da yake shiga garin domin zuwa wurin jana'izar mahaifiyarsa.
Mahhaifiyarsa ta mutu ne a a shekarar 2023 lokacin da ya tsere zuwa Jamhuriyar Benin.
Igboho ya bar Najeriya a 2021 bayan fito na fiton da aka yi tsakanin masu taimaka masa da jami'an hukumar tsaro ta farin kaya DSS waɗanda suka yi wa gidansa ƙawanya a yankin Soka da ke birnin Ibadan a jihar Oyo.
Sunday Igboho wanda ke neman samarwa ƙabilar Yarabawa ƴanci ya gudu zuwa Benin bayan da hukumar DSS ta ayyana tana neman sa ruwa a jallo.
An tsare Igboho a Jamhuriyar Benin a Octoban 2021 lokacin da yake ƙoƙarin tafiya Jamus.
An tuhume shi da yin mu'amala da miyagu sai dai ya samu ƴanci a baya-bayan nan bayan shafe shekara biyu a gidan yarin Benin.
Da gaske an saki Sunday Igboho mai rajin kare ƙabilar Yarbawa?
Sunday Igboho: Gwamnatin Benin tana bincike kan mai fafutikar kafa kasar Yarabawa
Hotunan jana'izar tsohon gwamnan Ondo, Akeredolu
Bayanan hoto, A yau Juma'a ne ake jana'izar marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu wanda ya mutu a watan Disamban 2023 bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Bayanan hoto, A cikin watan Janairu ne aka dawo da gawar marigayin Najeriya.
Bayanan hoto, Mai ɗakinsa Betty Anyanwu-Akeredolu da ƴaƴansa na daga cikin waɗanda suka tarbi gawarsa a filin jirgin sama
Bayanan hoto, Babajide Sanwo Olu, gwamnan jihar Legas na cikin manyan mutanen da suka halarci taron jana'izar
Bayanan hoto, Ana gudanar da jana'izar ne a birinin Owo da ke jihar
Bayanan hoto, Tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje
Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya rasu
Yadda aka yi jana'izar Kiristocin da 'yan bindiga suka kashe
Arziƙin cikin gida na Najeriya ya samu bunƙasa mafi ƙanƙanci a 2023
Asalin hoton, Google
Bunƙasar tattalin arziƙin Najeriya na cikin gida ya samu mafi ƙanƙantar tagomashi idan aka kwatanta da sauran shekarun baya, tun bayan zuwan annobar korona, wadda ta jefa tattalin arzikin ƙasar cikin garari.
A cikin sanarwar da hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta fitar, tattalin arziƙin Najeriyar na cikin gida ya samu bunƙasa da kashi 2.74 cikin 100 a 2023 saɓanin kashi 3.10 da ya kai a 2022.
Rashin aikin yi kuma ya ƙaru da kashi 4.2 cikin 100 zuwa kashi 5 cikin 100 idan aka kwatanta shekarun biyu.
NBS ta ce an samu bunƙasar ɓangaren noma da kashi 2.10 cikin 100 daga ƙaruwar kashi 2.05 cikin 100 da ya yi a rubu'i na huɗu na 2022.
Shin samamen jami’an tsaro a kasuwannin canji zai farfaɗo da darajar naira?
Yadda aka rufe kasuwar ƴan canji a Abuja
An hukunta iyayen da ke tura yaransu bara a Uganda
Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a Uganda ta yanke wa wasu mata fiye da 100 hukuncin hidimta wa al'umma bayan da suka amsa laifi kan tuhumar da ake musu na tura yaransu bara a Kampala, babban birnin ƙasar.
Kotun ta kuma haramta wa matan komawa birnin tare da bayar da umarnin a tasa ƙeyarsu zuwa mahaifarsu Napak a arewacin Uganda, kamar yadda jaridar Daily Monitor ta ruwaito.
Matan sun nemi a yi masu sassauci inda wasu suka ce sun rasa mazansu, wasu kuma ba sa tare da mazan nasu, in ji jaridar New Vision.
"Na ji kokensu kuma yanke musu hukuncin zaman gidan yari ba zai dace ba. Dole na ɗauki matakin da zai zama wa'azi... Zan yanke musu hukuncin yi wa ƙasa hidima. Idan ka saɓa, za ka yi zaman gidan gyaran hali na wata ɗaya," in ji alƙalin kotun, Edgar Karakire.
Tura yara bara ya saɓa wa dokokin kare ƙananan yara na Uganda kuma laifi ne da ke ɗauke da hukuncin zaman gidan yari na wata shida.
An kama matan a watan da ya gabata lokacin da aka ƙaddamar da shirin fatattakar masu bara daga babban birnin gabanin wasu tarukan ƙoli uku na duniya da aka yi a ƙasar.
An kai yaran zuwa wurin rainon yara na Masulita a tsakiyar ƙasar - garin da ke karɓar yaran da aka ceto.
Kungiyar Musulmi na son a yi dokar hana bara a Najeriya
Kotu ta yanke wa Dani Alves hukunci ɗaurin shekara huɗu