Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida and Haruna Kakangi

  1. A daina saka wayar da ta faɗa ruwa cikin shinkafa - Apple

  2. Nijar ta karɓi baƙuncin tawagar Iran

    ...

    A jiya Laraba ne Firaministan Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine ya karbi baƙuncin tawagar Iran ƙarƙashin jagorancin mataimakin ministan harkokin tattalin arziki na Iran, Mehdi Safari a ma'aikatar harkokin wajen ƙasar.

    Gidan talabijin na ƙasar Tele Sahel ya bayar da rahoto cewa tattaunawar ta kasance game da aiwatar da yarjeniyoyi da za su amfani ɓangarorin biyu.

    "Mun shirya yin hadin gwiwa da Nijar a fannin ɗanyen mai da matatun mai da tashoshi da kuma ma'ajiyarsu" in ji Safari

    Nijar na sake fasalin manufofinta na ketare, inda ta ƙara kusantar Rasha bayan takun saka tsakaninta da Faransa da sauran ƙawayenta na Yamma kan juyin mulkin ranar 26 ga Yulin 2023.

    • Ecowas ba ta yi mana adalci ba – Firaministan Nijar
    • Idan lokaci ya yi za mu saki Bazoum - Firaministan Nijar Lamine Zeine
  3. Gwamnatin Libya ta ce ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai za su fice daga birninTripoli

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da ke riƙe da birnin Tripoli sama da shekaru goma sun amince su bar babban birnin ƙasar Libya.

    Ministan harkokin cikin gida Imad Trabelsi ya ce bayan tattauna mai tsawo an cimma yarjejeniyar cewa ƴan sanda gwamnati sune za su dinga tabbatar da tsaro

    Ya shaida wa manema labarai cewa za a samu ‘yan sandan gaggawa da jami’an birnin da kuma masu binciken laifuka kadai daga wurinsu.

    Matakin ya biyo bayan kazamin faɗan da aka yi a baya-bayan nan.

    Ƙasar Libya dai ta fuskanci ƙalubalen tsaro tun bayan hamɓarar da gwamnatin Muammar Gaddafi a shekara ta 2011, inda ƙasar ta rabu tsakanin gwamnatin yammacin ƙasar karkashin jagorancin Abdul Hamid Dbeibah da kuma gwamnatin gabashin ƙasar karkashin jagorancin Khalifa Haftar.

    Ya ce da zarar ƙungiyoyin sun fice daga babban birnin ƙasar wasu biranen za su bi baya, yana mai cewa "ba za a sake samun shingayen binciken ababen hawa ba, da kuma sauran kungiyoyi masu dauke da makamai" a kan tituna ba"

    Yarjejeniyar za ta sa akalla kungiyoyi biyar ɗauke da makamai su bar birnin Tripoli a karshen watan Ramadan a ranar 9 ga watan Afrilu, ciki har da wanda ke da sansani a yankin da aka kashe mutane 10 a karshen mako.

    Ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ake magana a kai sun haɗa da rundunar tsaro da rundunar tsaro ta Musamman da Birgediya 444 da Brigade 111 da kuma Hukumar Tallafawa Zaman Lafiya - suna da muggan makamai tare da raba yankuna da dama a tsakaninsu.

    Sai dai sau da yawa sun kasance suna fafatawa da junansu, ciki har da wani lamari da ya faru a watan Agusta wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 55 tare da jikkata kusan 150.

    Ba sa ƙarƙashin ikon gwamnatin Libya kai tsaye, amma suna samun tallafin jama'a. An ba su 'yancin gudanar da ayyukansu ne ta hanyar matsayi na musamman da gwamnati ta ba su a cikin 2021.

    • Libya: Me ya sauya bayan shekara 10 da kashe Mu'ammar Gaddafi?
    • An sace makamashin uranium da ake haɗa makamin nukiliya da shi a Libya – MDD
  4. Wani asibitin Amurka ya dakatar da haɗa ƙwan halitta bayan hukuncin kotu

    ..

    Asalin hoton, CARLOS DUARTE

    Babban asibitin Alabama ya dakatar da yin aikin da ke haɗa ƙwan-halitta don haihuwa da ake kira IVF, bayan hukuncin kotun ƙolin Amurka da ya ce ɗan tayen mutum yana a matsayin ƙaramin yaro ne a tanadin doka.

    Asibitin ya ce ya ɗauki matakin ne saboda kaucewa yanayin da zai sa likitoci ko marasa lafiya su faɗa tarkon fuskantar shari’a.

    A makon jiya ne kotun ta yanke hukuncin cewa doka tana amincewa da matsayin ɗan Adam ne daga ranar da aka ɗauki cikin sa.

    Ƙungiyar masu rajin samun haihuwa ta hanyar yin aikin haɗa ƙwan-halitta ta ce wannan hukunci zai hana wasu asibitoci a sassan Amurka gudanar da irin wannan aiki ga masu buƙata.

    Ta bayyana hukuncin, da kuma matakan da asibitoci suka fara ɗauka a kai, a matsayin wani babban lamari da ke nuni da mawuyacin halin da wasu za su shiga a sassan Amurka.

    Gabby Goidel, wata da ke fatan ganin an yi mata aikin haɗa ƙwan-halitta domin ta samu haihuwa, bayan ta yi ɓarin ciki har sau 3 ta bayyana ra’ayinta a kai.

    "Na yi matuƙar baƙin ciki a lokacin da na samu labarin hukuncin kotun, don kuwa wannan wani mataki ne da zai hana ni, da sauran mutane iri na damar cika burinmu na haihuwa ta wannan hanya. Akwai buƙatar mutane su sani cewa wannan halin da nake ciki, hali ne da ma’aurata da dama ke ciki, kuma kai tsaye wannan mataki zai gurgunta burinsu na samun iyali da cimma nasarar rayuwa.

    Buƙatata kawai a kare ƴancina na samun haihuwa."

    Wannan dai, ɗaya ce daga cikin ɗimbin Amurkawa da ke da wannan fata, waɗanda kuma wannan hukunci ya shafa kai tsaye.

    • Tagwaye manne da juna da aka fitar da ran za su rayu na bai wa duniya mamaki
    • Yadda karancin maganin kashe radadi ke jefa mutane cikin mawuyacin hali a Gaza
    • Shin ko maganin gyaran jiki na Collagen na hana motsewar fata?
  5. Issoufou ya musanta hannu a kifar da gwamnatin Bazoum

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon shugaban jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou ya yanke shawarar shigar da ƙara a gaban kotu bayan zargin sa da aka yi da hannu a juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar bara.

    Tsohon jakadan Faransa a Nijar ne ya yi wannan zargi sai dai lauyan Mahammadu Issoufou ya bayyana zargin a matsayin maganar da ba ta da tushe kuma wani yunƙuri na shafa masa kashin kaji.

    Issoufou ya musanta zargin inda ya ce ganawar da Sylvain Itte ya ce ya yi da Tchiani ranar 28 ga watan Yuli, ba za ta zama hujjar zargin sa da hannu a juyin mulkin da aka yi a ƙasar ba.

    Game da takun-saƙar da ake cewa akwai tsakanin shugaba Bazoum da Mahamadou Issoufou kan naɗin babban daraktan sabon kamfanin dillancin man fetur a kasar, lauyan na Issoufou ya ce zancen na ƙanzon kurege ne.

    Lauyan ya kuma ƙara da cewa babu wata rashin jituwar da ke tsakanin ministan man fetur na ƙasar da Bazoum sai dai ma ra'ayinsu da ya zo ɗaya game da sabon kamfanin.

    Lauyan ya kuma jaddada cewa Mahamadou Issofou ba shi da wata alaƙa da hamɓarar da gwamnatin da aka yi a don haka hujjojin da Sylvain Itte ya gabatar gaban hukumar tsaro ta ƙasa da kuma sojojin majalisar Faransa kawai yarfe ne.

    A cewar lauyan, girman zarge-zargen da aka yi ne ya sa tsohon shugaban Nijar ɗin zai je kotu domin a yi masa adalci.

    • Issoufou na da hannu a cire Bazoum daga mulki – Tsohon jakadan Faransa
    • Ko taron Ecowas a Abuja zai samar da mafita ga Nijar?
    • Me ya rage wa Nijar, Mali da Burkina Faso bayan ficewa daga Ecowas?
  6. Salam Alaikum

    Muna yi muku barka da wannan lokaci.

    Da fatan za ku bibiye mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da ma wasu sassan duniya.

    Akwai shafukanmu na sada zumunta da za ku iya garzayawa domin karanta ƙarin labarai da kallon bidiyo.