Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida and Haruna Kakangi

  1. An kama ƴan sandan Kenya kan zargin fataucin bil adama

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an tsaro sun cafke ƴan sanda huɗu a Kenya yayin kai samame wani gida da ke da tazarar kilomita 16 daga Nairobi, babban birnin ƙasar inda aka samu ƴan Habasha 37 a ciki.

    Ana zargin ƴan sandan na da hannu a safara da kuma fataucin bil'adama.

    A rahoton da gidan jaridar The Star ya fitar ƴan Habashan sun shaida wa jami'an Kenya cewa suna kan hanyarsu ta zuwa Afrika ta Kudu ne don neman rayuwa mafi inganci.

    Ana ci gaba da bincike kan mai gidan da aka samu mutanen da kuma sauran masu hannu a safarar.

    Hukumar kula da ƴan gudun hijra ta majalisar ɗinkin duniya IOM ta ce Kenya ta kasance sananniyar hanya ga ƴan ci-ranin Habasha masu son tsallakawa Afrika ta Kudu ta haramtacciyar hanya.

    Hukumar ta ce ƴan gudun hijarar waɗanda mafi yawansu maza ne da suka fito daga ɓangaren Oromia da SNNP na Habasha na shiga Kenya ta iyakar Moyale sannan su shiga Tanzania sai kuma su faɗa Afrika ta Kudu.

    • Yadda kisan wata matashiya ya fito da ƙiyayyar da ake nuna wa mata a intanet
    • Yadda ake kashe miliyoyin jakai duk shekara don haɗa maganin gargajiya
    • Fashewar gas a Nairobi ta kashe mutum uku da jikkata kusan 300
  2. Afirka ta Kudu za ta gudanar da babban zaɓe a ranar 29 ga Mayu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Cyril Ramaphosa na neman wa'adi na biyu a matsayin shugaban ƙasa

    A ranar 29 ga watan Mayu ne za a gudanar da zaɓen ƙasa da na larduna a Afirka ta Kudu, a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru 30 na samun ‘yanci da dimokuraɗiyya, in ji fadar shugaban ƙasar.

    Ta ce shugaba Cyril Ramaphosa ya tuntuɓi hukumar zaɓe game da ranar.

    Shugaban ya kuma kira taro da dukkan shugabannin larduna da hukumar domin tattauna halin da ake ciki a shirye-shiryen zaɓen.

    Masu kaɗa kuri'a za su zaɓi sabuwar majalisar dokoki ta ƙasa da kuma 'yan majalisar dokoki a kowane lardi tara na ƙasar.

    Za a bai wa jam'iyyu kujeru a cikin kujeru 400 na majalisar dokoki bisa kaso na kuri'un da suka samu a zaɓen sannan 'yan majalisar su zaɓi shugaban ƙasa.

    Ramaphosa dai na neman wa'adi na biyu a matsayin shugaban ƙasa.

    Jam'iyyarsa ta African National Congress na fuskantar zazzafar takara a zaɓukan, inda ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa jam'iyyar za ta iya rasa rinjayen da take da shi ƙasa da kashi 50 cikin 100, a karon farko cikin shekaru 30 na mulkin dimokuraɗiyyar Afirka ta Kudu.

    Afirka ta Kudu ta gudanar da zaɓukan dimokuradiyya na farko a duniya a shekarar 1994 bayan kawo ƙarshen tsarin wariyar launin fata, inda aka zaɓi Nelson Mandela a matsayin shugaban ƙasa.

    • Kotun Duniya: Me ya sa take sauraron zargin Isra'ila da kisan ƙare-dangi?
    • Yadda faɗa-a-jin Ƙasashen Yamma ke daɗa raguwa a Afirka
    • Dalilin da ya sa jam’iyyun siyasa 7 suka ƙulla ƙawance a Afrika ta Kudu domin ƙalubalantar ANC
  3. Ƙasashe sun soki matakin Amurka na hana ƙudurin neman dakatar da yaƙi a Gaza

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Ƙasashe da dama a Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi alla-wadai da matakin da Amurka ta ɗauka na hana wani ƙuduri da ya nemi tsagaita wuta cikin gaggawa a zirin Gaza.

    Amurka dai ta bayar da hujjar cewa ƙudurin zai kawo cikas ga tattaunawar da za ta kawo ƙarshen yaƙin da ake yi tsakanin Hamas da israila.

    Sai dai wakilin Falasdinawa a Majalisar Ɗinkin Duniyar, Riyad Mansour ya bayyana matakin a matsayin wani abu mai haɗari sosai.

    Ya ce rashin amincewa da wannan ƙuduri abin takaici musamman idan aka yi la'akari da cewa an shafe tsawon makonni ana tattaunawa.

    Ita ma aminiyar Amurka wato Faransa ta nuna rashin jin daɗinta a kan yadda matakin ya kasa samun amincewa idan aka yi la'akari da abin da ta kira mummunan halin da ake ciki a Gaza.

    • Yadda karancin maganin kashe radadi ke jefa mutane cikin mawuyacin hali a Gaza
    • Isra’ila ta kai mummunan hari a birnin Rafah
    • Hindu - An gano gawar yarinya ƴar Falasɗinu da ta tsinci kanta tsakiyar sojin Isra’ila
  4. Barka da Safiya!

    Masu bibiyar mu barkan ku da warhaka.

    Barka da sake saduwa a shafinmu da muke kawo muku bayanan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu a wannan rana domin ci gaba da kawo muku bayanai kai tsaye.