An gudanar da zanga-zangar nuna adawa da ƙasashen yamma a gabashin DR Congo

Mazauna birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a jiya sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da kasashen yammacin duniya da suka zarga da ƙara tabarbarewar matsalar tsaro a yankin da ke fama da tashe-tashen hankula, inda kungiyoyin da ke ɗauke da makamai ke kai hare-hare, in ji gidan rediyon Faransa RFI.
RFI ta ce an ƙona tutoci da dama da suka haɗa da na Amurka da Faransa.
Hukumomin ƙasar dai sun haramta zanga-zangar, suna masu cewa hakan bai dace ba, kuma suna cikin kasadar “kautar da hankalin hukuma” daga “yaƙin da aka dora musu”.
Masu gudanar da zanga-zangar sun ce ƙasashen da aka ƙona tutocinsu na aiki ne tare da ƙasar Rwanda, wadda ake zargi da goyon bayan 'yan tawayen M23.
Patrick Ricky Paluku na ƙungiyar matsin lamba ta Veranda Mutsanga ya ce "Su ne ke bai wa abokan gabanmu kudi."
Masu zanga-zangar sun kuma yi watsi da yiwuwar tattaunawa tsakanin gwamnatin Kongo da 'yan tawayen M23 a nan gaba.
Jami'an Congo sun ce sojojin ƙasar na samun gagarumar nasara a kan 'yan tawayen a daidai lokacin da ake gwabza faɗa a garin Sake mai tazarar kilomita 20 daga Goma.
- Adadin wadanda suka rasu sakamakon arangama a sansanonin MDD a Dimokraɗiyar Congo ya kai 19
- 'Da za mu yi zaɓe da mun zaɓi zaman lafiya a Dimokuraɗiyyar Kongo'




