Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Ahmad Tijjani Bawage and Ibrahim Yusuf Mohammed
Sojojin ruwan Maroko sun ceto baƙin haure ƴan Afirka 141
Asalin hoton, Royal Moroccan Armed Forces/X
Sojojin ruwan Maroko sun ceto bakin haure 141 ‘yan Afirka da ke cikin kwale-kwale da suka gamu da matsala yayin da suke tafiya daga Mauritania zuwa tsibirin Canary na Spain.
An ceto mutanen ne a ranar Lahadi, kimanin kilomita 274 kudu maso yammacin Dakhla a cikin hamadar yammacin sahara.
'Yan baƙin hauren sun tashi ne daga gabar tekun Mauritaniya a ranar 10 ga watan Fabrairu, kamar yadda rahotanni daga sojojin ruwan Morocco suka ruwaito a kamfanin Dilancin labaran reuters.
A bara, tsibirin Canary ya karƙi kusan baƙin haure 32,000, wanda ya zama mafi yawan adadin da aka samu tun shekara ta 2006.
A watan Janairu, hukumomin Spain sun ba da rahoton ci gaba da ƙaruwar bakin haure zuwa tsibiran, inda aƙasarin jiragen ruwa suka fito daga Mauritania.
Bakin-haure 626 sun makale a kan teku
Abin da ya sa ba ma so mu koma gida — ‘Yan gudun hijira
'Sakin' Murja Kunya ya bar baya da ƙura a Kano
Asalin hoton, Murja Kunya/Facebook
Al'umma a jihar Kano na ci gaba da ce-ce-ku-ce kan rahoton da ke nuna fitacciyar ƴar Tiktok ɗin nan, Murja Ibrahim Kunya - da a baya-bayan nan kotu ta tasa ƙeyarta zuwa gidan yari ta shaƙi iskar ƴanci.
A makon da ya gabata ne kotun shari'ar musuluncin da ke Gama ta bayar da umarnin a tsare Murja a gidan gyaran hali na Kurmawa bayan da Hukumar Hisbah ta kama ta bisa zargin nuna rashin ɗa'a da yunƙurin jefa ƴanmata cikin karuwanci.
Kotun dai ta nemi a tsare ƴar Tiktok ɗin ne har zuwa ranar Laraba 27 ga watan Fabarairu sai dai bayanai na cewa an bayar da belin ta, lamarin da ya fusata wasu al'ummar jihar.
Mutane da dama a shafukan sada zumunta sun yi ta bayyana ra'ayinsu kan yadda ake cewa Murja Kunya ta samu beli duk da cewa kotu ta bukaci a tsare ta har ranar Laraba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito kakakin kotun, Muzammil Ado Ibrahim Fagge na cewa bai san da faruwar lamarin ba.
Ya ce "mun kuma ji cewa an sake ta daga gidan yari. Alƙalin kotun ya ce zai yanke shawara kan ko ya ba ta beli ko a a, a ranar 20 ga watan Fabarairu. "Ba mu san abin da ya faru ba. Ba za a iya sauya abin da ya faru a kotu ba musamman kan wannan yarinyar da ba wannan ne karon farko ba."
A nashi ɓangaren, mai magana da yawun hukumar gidan gyaran halin, Musbahu Kofar Nassarawa ya ce an sake ta ne bayan samun umarni daga kotu.
Ya ce hukumar gidan gyaran halin na tafiya ne bisa tsarin doka kuma tana aiki ne kamar banki, "takardu ke shigar da kai, irin takardun kuma ke fitar da kai."
"Dole ne alƙali ya sa hannu a tura ka gidan yari, haka nan idan za a sake ka."Kan batun Murja, babu wanda ya tsere daga gidan yari. Idan ka hau katanga a ƙoƙarin tserewa, daidai yake da a ɗauki matakin harbe mutum kuma muna da ƙofofi da jami'ai ke tsaronsu.
Wani jami'i a hukumar hisbah da ke Kano wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ba zai shafi ayyukan jami'ansu ba saboda ba za su naɗe hannu ba a yaƙi da baɗala a jihar Kano.
Tuhumar da ake yi wa Murja:
A wata tattaunawa da manema labaru bayan kama ƴar tiktok ɗin, kwamandan Hizba a jihar Kano, Sheikh Ibrahim Daurawa ya ce tuhume-tuhumen da ake yi wa Murja Kunya sun haɗa da: Razana al'umma, ayyukan baɗala, tayar da hatsaniya, tayar da hankalin al'umma, kawo ɓatagari cikin unguwa, iƙirarin cewa ita ce shugaban karuwai da ƴan kwalta.
'Masu garkuwa na amfani da macizai domin tsoratar da mu'
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wasu mutanen da suka samu tsira sun nemi maganin dafin macizai bayan da suka kuɓuta daga hannun 'yan bindigar
Mutanen da suka shaƙi iskar ‘yanci daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su sun
bayyana cewa mutanen da suka sace sun a amfani da macizai masu dafi domin
tsorata su.
Wasu a cikinsu da suka bayyana halin
da suka tsinci kansu a ciki a hirar da suka yi lokuta daban-daban da kamfanin
dillancin labarai na NAN sun ce akwai macizai masu tarin yawa a cikin dajin da ‘yan
bindigar suka mamaye.
Sun ce
macizan suna yawan sarar masu garkuwar da mutanen da aka sace.
Ɗaya daga
cikin mutanen da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa NAN cewa masu garkuwar
sun jefa su cikin matattarar macizai.
“Masu
garkuwar sun san wuraren da macizai suke kuma suna ajiye mutanen da suka sace a
nan.
“Da zarar sun
ga macizai, masu jin tsoronsu sai su yi ta neman guduwa. Ganin macizan na
tsoratar da su.
“Lokacin
ne waɗanda aka sace suke neman ‘yan uwa da abokan arziki su sayar da komai –
gida da fili da motoci da kayan gida da takalma, komai ma – kawai don a haɗa kuɗin
fansa.”
Binciken
da NAN ya yi ya gano dazukan da ke da mafi yawan macizai suna Birnin Gwari a
jihar Kaduna da Kala-Balge kusa da tafkin Chadi a jihar Borno.
Wasu
yankunan sun haɗa da Shaki a jihar Oyo da Borgu da Kagara a jihar Neja sai
Karim Lamido a Adamawa da Lau a jihar Taraba.
Wasu
cikin mutanen da suka kuɓuta daga hannun ‘yan bindigar sun shaida wa NAN cewa
lamarin ya ƙazanta a yanzu ganin yanayin zafin da ake ciki yayin da macizan ke
barin ramukansu da nufin neman abinci da shan iska.
An kama wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Taraba
Mutanen da ƙungiyar Hamas ke garkuwa da su tsawon shekaru
Barka da Safiya
Masu bibiyar mu barka da wannan lokaci da
fatan an tashi lafiya.
Muna fatan kasancewa da ku a wannan yini, domin kawo muku labarai da
rahotanni kai tsaye daga sassan duniya.