Burtaniya ta kashe sama da fan miliyan 300 kan harkokin tsaro a Afrika a 2023

Asalin hoton, Techeconomy
Gwamnatin Burtaniya ta ce ta zuba kudi da suka kai fan miliyan 300 a wasu shirye-shiryen magance matsalar tsaro da wanzar da zaman lafiya, domin amfanin mutanen nahiyar da itra kanta Burtaniya.
Minsitan kula da harkokin gwamnati Baroness Lucy Neville-Rolfe wadda ta zo Najeriya domin aikin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu ce ta bayyana hakan cikin sanarwar da Atinku Akande-Alegbe jami’ar da ke ofishin yada labarai ta FCDO ta fitar.
Ziyarar ta zo ne ‘yan kwanaki bayan da wani shirin haɗin gwiwar harkokin tsaro tsakanin ƙasashen biyu ya cimma yarjejeniya kan tsaron intanet, haɗin kan harkokin tsaro da yakin da ta’addanci da yancin ɗan adam da haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da fararen hula.
A Arewa maso Gabashin Najeriya kudin da Burtaniya ta zuba sun taimaka wa sama da mutum 500 da suka gujewa rikicin aka ba su wuraren zama.
Tataimaka wajen koyar da sana’o’in hannu da harkokin addinai da wayer da kan al’umma kan harkokin shaye-shaye.
















