Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Yan bindiga sun kashe fiye da mutum 10 tare da sace 15 a Zamfara

    .

    Asalin hoton, .

    'Yan bidiga sun kai hare-hare a garin Nasarawar Godel na yankin karamar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamfara.

    Wannan dai shi ne karo na farko da 'yan bindigar ke kai hari wannan gari, kamar yadda wani mutumin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa BBC.

    ''Muna cikin halin farbaga da tashin hankali, inda ta kai ga wasu ba sa iya kwana a gidajensu, abin da ya faru jiya baƙon al'amari mu dai wajenmu, saboda ba mu taɓa fuskantar irin wannan hari ba'', in ji mutumin.

    Ya ce maharan sun auka wa garin cikin gungunsu ɗauke da muggan makamai, inda suka kashe aƙalla mutum bakwai, tare da kashe wasu mutum uku a ƙauyen Dillashe mai maƙwabtaka da garin.

    Mutumin garin ya shaida wa BBC cewa maharan sun kuma yi garkuwa da mutum aƙalla 15.

    Maharan sun kuma ƙona gidajen mutanen garin tare da farfasa shaguna da ƙwashe dukiyoyi masu tarin yawa.

    BBC ta kuma tuntuɓi kakakanin rundunar 'yansanda da ɓangaren gwamnatin jihar Zamfara game da wannan harin, sun kuma ce za su bincika su sake kiranmu, amma har ya zuwa yanzu ba mu daga gare su ba.

  2. Wane ne Alexei Navalny?

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Alexei Navalny ya shiga gangamin da aka gudanar a Moscow a 2020

    Alexei Navalny, mai shekara 47 ya kasance fitaccen mai sukar manufofin shugaban Rasha Vladimir Putin.

    Ya shafe fiye da shekara 10 yana fallasa cin hanci da rashawa a gwamnatin Rasha.

    Miliyoyin mutane ne suka kalli bidiyoyin bincikensa da ya wallafa a shafukan intanet.

    Kasancewarsa mutum mai farin jini, Mista Nanalny ya buɗe ofisoshin yaƙin neman zaɓe a sassa daban-daban na ƙasar, saboda aniyar tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2018 domin karawa da shugaba Putin, to amma haƙarsa ba ta cimma ruwa ba, domin kuwa an haramta masa yin takarar.

    A shekarar 2020, an sanya masa wani abu a abinci a Siberia a wani abu da ɗakunan gwaji na ƙasashen Yamma suka tabbatar da cewa guba ce.

    An yi masa magani a ƙasashen waje, inda kuma aka ɗaure shi tun bayan komawarsa ƙasar a watan Janairun 2021, lokacin da aka kama shi.

    Kafin a ɗaure shi yana zaune a birnin Moscow tare da matarsa Yulia da 'ya'yansu biyu.

  3. Biden ya zargi Putin da kitsa kisan Navalny

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Joe Biden ya zargi Vladimir Putin da alhakin kashe madugun ƴan adawar Rasha Alexei Navalny a gidan yari.

    Mista Biden ya ce mutum ne mai basira da aƙida, wanda kuma ya jajirce wajen ganin ya gina Rasha, mai bin doka ne da kuma ƙa'ida.

    Sauran shugabannin ƙasashen Yamma sun yi irin wannan zargi, inda suka jinjinawa Mista Navalny kan jajircewa tare da tsayawa tsayin daka wajen adawa da manufofin Putin.

  4. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa, Abdullahi Bello Diginza ke muku barka da wannan lokaci.

    Fatan kun wayi gari lafiya, barkanku da shigowa shafinmu kai-tsaye, domin sanin halin da duniya ke ciki.

    Kar ku manta da bayyana ra'ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta da muhawara