Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Sojojin Ukraine sun janye daga Gabashin birni Avdiivka

    b

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya sake rokon goyon bayan kasashen ketare sakamakon janyewar dakarun Ukraine daga Gabashin birni Avdiivka. Mista Zelensky ya kara da cewar sojin sun ja da baya ne don kaucewa asarar rayuka. Wani kunshin taimako na miliyoyin daloli ya makale a majalisar dokokin Amurka.

    Amma mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta ce kyamar siyasa ba za ta hana taimakawa Kyiv ba. Kungiyar EU ta bayyana cewar za ta iya bayar da rabin makamai miliyan daya da ta yi alkawarin aikawa a watan Maris.

  2. An shiga rudani game da inda gawar Alexei Navalny

    g

    An shiga rudani game da inda gawar jagoran adawa na Rasha, Alexei Navalny gawarsa ta ke.

    Tun da farko mahaifiyarsa da lauyansa sun isa cibiyar ajiyar gawarwaki da ke kusa da kurkukun Arctic inda ya mutu a ranar juma'a amma jami'ai suka sanar da su cewar gawar ba ta tare da su. Mahukunta sun shaida wa iyalan Mista Navalny cewar ba za a mika musu gawar ba har sai am kammala bincike. To sai dai guda daga cikin makusantan jagoran adawar Kira Yarmish ta zargi mahukunta da ƙoƙarin ɓoye sakamakon binciken bayan ta ce babu shakka kashe shi aka yi. A ranar Juma'a ma'aikatar gidajen kurkuku ta sanar da cewar Mista Navalny mai shekary 47 ya mutu bayan ya gudanar da tattakin akalla kilomita dubu biyu a Arewacin Moscow

  3. Shugaban Somalia yace sai an haɗa hannu za a iya magance matsalr tsaron nahiyar

    m

    Shugaban Somalia Hassan Sheik Mohamud ya bayyana cewa babu yadda za a yi nasara a yaƙin da ake yi da masu ikirarin jihar har sai an hada ƙarfi da ƙarfe.

    Ya bayyana haka ne yayi taron kungiyar Afrika ta AU karo na 37 da ke gudana a Addis Ababa babban birnin Habasha.

    Shiek Hassan ya ce matuƙar ana son zaman lafiya to sai an sauya dabarun da ake amfani da su wajen yakin da matsalar tsaro a nahiyar.

    Ya ce matakin da Habasha ta ɗauka na yarjejeniya da yankin Somaliland ya saba da doka, kuma ba za su yarda da hakan ba.

  4. Najeriya na cikin halin "ni-'ya-su" akwai buƙatar a cece ta - Tambuwal

    s

    Asalin hoton, Tambuwal X

    Tsohon gwamnan Sokoto kuma Sanatan da ke wakiltar Kudancin Jihar Aminu Waziri Tambuwal ya ce, Najeriya na cikin mummunan halin da take buƙatar a kai mata ɗaukin gaggawa.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito Tambuwal na ce akwai buƙatar haɗa hannu tare domin ceto Najeriya daga halin da take ciki.

    Da aka tambaye shi game da hakin da ƙasar ke ciki, Tambuwal sai ya ce "da na tafi hutun magana da manema labarai. Ina sane na gwammace na yi shiru kimanin wata tara kan halin da muke ciki.

    "Yana da na shiga na shiru, yanayin da zuciyata take ciki kenan, Kawai na hakura da magana ne. Idan ka tsinci kanka cikin abu, kuma wani yanayi da ba a yi tsammani ba ya faru, dole ka yi shiru.".

    Amma a cewarsa duk mai son ya ji yanayin da Najeriya ke ciki ya je ya tambayi mutanen ƙasar.

    Ya ce ba sai mutum ya je nesa ba, kamata ya yi ya tambayi kansa yanayin da ake ciki. "Najeriya na cikin mawuyacin hali. Tana buƙatar ɗaukin gaggawa. Wannan nauyinmu ne babu magnar jam'iyyar siyasa ko addini ko yare wajen aikin ceto ƙasarmu".

    Tsohon kakakin ƙasar ya shawarci 'yan jarida da su riƙa gayawa shugabanni gaskiya kan yanayin da Najeriya ke ciki.

  5. Ra'ayi Riga: Kan tashin farashin dala a Najeriya

  6. Burtaniya za ta ɗauki mataki kan mutuwar Navalny

    b

    Sakataren harkokin wajen Burtaniya ya ce Burtaniya "za ta ɗauki mataki" kan mutuwar jagoran 'yan adawar Rasha Navanly a gidan yarin Rasha.

    Da yake magana a wajen taron harkokin tsaro da ke gudana a Muncich, Cameron ya ce "dole sau an dauki mummunan mataki" kan mutuwar ɗan siyasar, wanda ake tsare da shi a gidan yarin Rasha tun 2021 kuma kawai domin dalilai na siyasa.

  7. An ɗaure wata mata bayan kai wata yarinya 'yar Burtaniya Kenya don yi mata kaciya

    b

    An aike da wata mata gidan yari kan laifin ɗaukar wata yarinya 'yar Burtaniya zuwa Kenya domin a yi mata kaciyar mata.

    Amina Noor mai shekara 40 ta fito ne daga gabashin Landan inda ta je Kenya a 2006, ta kai yarinyar wabi keɓaɓɓen gida domin a yi mata kaciyar, kamar yadda kotu t ce.

    A Old Bailey an ɗaure Noor a gidan yari na tsawon shekara bakwai.

    Ita ce mutum ta farko da aka ɗaure saboda taimawa wajen yin kaciyar mata.

    Ta shaida wa kotun Old Bailey cewa abu ne na al'ada, kuma ita ma an taba yi mata a baya.

    Yayin zaman yanke hukuncin mai shari'a Bryan ya ce "da wannan mummunan aiki an lalata wa yarinyar rayuwarta kuma ba za ta taba komawa kamar yadda take a baya ba".

  8. An gudanar da gagarumar zanga-zanga a Senegal

    v

    Dubban masu zanga-zanga sun taru a Dakar babban birnin Senegal, inda suka rika kiran a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar ba tare da ɓata lokaci ba.

    Wannan ce zanga-zanga ta farko da hukumomin ƙasar suka bari aka yi, tun bayan matakin ɗage zaɓen ƙasar shugaban ƙasar da Macky Sall ya sanar mako biyu da suka gabata.

    Magoya bayan jam'iyyun adawa da suka shiga zanga-zanagar sun riƙe kwalayen da ke ɗauke da saƙonni daban-daban da suka haɗar da '' Muna son 'yancin Senegal'' da ''Ba ma son tauye kundin tsarin mulki''.

    A ranar Alhamis kotun tsarin mulkin ƙasar ta ce abin da Macky Salla ya yi ya saɓa wa doka.

    Inda shi kuma ya yi alƙawarin tattaunawa da masu ruwa da tsaki don saka sabuwar ranar zaɓen.

    Ƙungiyar Ecowas da ƙasashen Yamma sun nuna damuwarsu kan matakin jinkirta zaɓen a ƙasar da ake kallo a matsayin mai ɗorewar dimokraɗiyya a yankin Yammacin Afirka.

  9. Bikin ranar masoya a yayin takaicin cin zarafin mata cikin hotunan Afirka

  10. Za a bayar da gawar Navalny idan an kammala bincike - Rasha

    .

    Asalin hoton, Shutterstock

    Masu bincike a Rasha sun ce ba za a miƙa gawarsa ga 'yan uwansa ba har sai an kammala bincike, kamar yadda mai magana da yawun ɗan gwagwarmayar, Kira Yarmysh ya bayyana.

    Misis Yarmysh, ta ce shaida wa BBC cewa kawo yanzu makusantan marigayin ba su son inda aka ajiye gawarsa ba.

  11. Mutuwar fuju'a Navalny ya yi - Gidan yari

    Hukumomin gidan yarin da mista jagoran adawar Rasha ya mutu, sun shaida wa mahaifiyarsa cewa ɗan nata ya yi mutuwar fuju'a ne, kamar yadda ɗaya daga cikin makusantansa ya bayyana.

    Wani abokin minsta Navalny mai suna Ivan Zhdanov ya wallafa a shafinsa na X cewa har yanzu makusantan marigayin na jiran a ba su gawarsa.

    Makusantan Navalny sun yi iƙirarin cewa kashe shi ka yi, inda kuma suka zargi hukumomin Rasha da ci gaba da riƙe gawarsa, saboda ''hana bincike''.

  12. Makusantan Navalny sun ce hukumomi sun ɓoye gawarsa

    .

    Makusantan Alexei Navalny sun yi ikirarin cewar gwamnatin Rasha na ci gaba da riƙe gawarsa.

    Mai magana yawun mista Navalny, Kira Yarmysh, ta shaida wa BBC cewa makusantan jagoran adawar na Rasha sun yi amanna cewa shugaba Putin ne ya kitsa kisan ɗan gwagwarmayar siyasar, wanda ya kasance fitaccen mai sukar manufofin shugaban na Rasha.

    Ta ce "Mun sani cewa ba mutuwa ce ta Allah da annabi ba, kashe shi aka yi''.

    "Suna ƙoƙarin daƙile duk wani bincike, shi yasa suka hana makusantansa gawar, suke ci gaba da ɓoye ta don hana su ganin gawar''.

    Misis Yarmysh ta ce babu wanda ya san inda gawar mista Navalny take, ko kuma yaushe za a bai wa 'yan uwansa ita.

    Ta ci gaba da cewa dokokin Rasha sun yi tanadin cewa, idan fursuna ya mutu, za a bai wa 'yan uwansa gawar cikin kwanaki biyu da rasuwarsa.

    Tun da farko ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce ta yi watsi da bayanan da ba ''na gaskiya ba'' da Birtaniya ta fitar kan dalilin kisan nasa.

  13. Gwamnan Rivers ya karrama golan Najeriya

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnan jihar River Siminalayi Fubara ya karrama golan Najeriya, Stanley Nwabali sakamakon bajintar da ya nuna gasar kofin ƙasashe Afirka ta Afcon da aka kammala makon da ya gabata.

    A bikin da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar, gwamna Fubara ya bai wa golan - wanda ɗan asalin jihar ne - kyautar zunzurutun kuɗi naira miliyan 20.

    Haka kuma gwamnan ya karrama shi da lambar yabo ta DSSRS, lambar yabo ta biyu mafi daraja da ake bai wa wadanda suka yi bajinta a fannoninsu, da manyan 'yan siyasa a jihar.

    Gwamnan ya kuma bai wa tawagar Super Eagles da ta samu wakilcin kocin tawagar Jose Peseiro da Finidi George kyautar naira miliyan 30, sakamakon bajintar da ƙungiyar na nuna a gasar.

    Najeriya dai ta ƙare gasar a matsayi na biyu, bayan da ta sha kashi a hannun Ivory Coast mai masaukin baƙi da ci 2-1 a wasan ƙarshe.

  14. An karrama 'yan sanda huɗu saboda ƙin karɓar cin hancin miliyan 8.5 a Taraba

    .

    Asalin hoton, police

    Rundunar 'yansandan jihar Taraba ta karrama wasu jami'anta huɗu, saboda ƙin karɓar cin hancin naira miliyan 8.5 dagha wasu da ake zargin 'yan bindiga ne a lokacin da suke aiki a wani shingen binciken ababe hawa.

    Kwamishinan 'yansandan jihar, David Illoyalonomo ne ya karrama jami'an huɗu a shalkwatar rundunar 'yansandan jihar.

    Mista Illoyalonomo ya ce jami'an sun nuna halin dattako, da ɗaga darajar aikin ɗansanda a idonduniya.

    Kwamishinan 'yansanda ya ce zai gabatar da jami'an huɗu ga babban sifeton 'yansanda na ƙasar, Kayode Egbetokun, domin yi musu ƙarin girma da kuma duba yiyuwar karrama su da lambar yabo.

  15. Gwamnatin Najeriya ta sake buɗe kantin Sahad na Abuja bayan rufe shi

    .

    Asalin hoton, Sahad Stores Web

    Hukumar da ke Kare Muradan Masu Saye ta Najeriya FCCPC ta sake buɗe katafaren kantin kayar da kayayyaki na Sahad Stores, bayan rufe shi.

    A ranar Juma'a 16 ga watan Fabrairu ne hukumar ta garƙame babban kantin, saboda zargin yadda ake cuwa-cuwar sanya farashin kayayyaki a kantin.

    Hukumar ta yi zargin cewa masu gudanar da katafaren kantin na ƙara wa abokan hulɗarsu kuɗin kaya fiye da farashin da ke maƙale a jikin kayan.

    FCCPC ta ce hakan na tilasta wa kwantomomi biyan kuɗaɗe masu tsada don sayen kayayyaki.

    To sai dai cikin wata sanarwa da mai riƙon muƙamin mataimakin shugaban hukumar, Adamu Abdullahi, ya fitar ya ce an sake buɗe kantin domin ci gaba da cinikayya.

  16. Gane Mini Hanya: Kan tsarin gwamnati mai firaminista

    A cikin wannan makon ne gungun wasu ‘yan majalisar wakilai su kusan 90 suka soma wani yunkuri, domin ganin an sauya tsarin mulkin Najeriya a shekara ta 2031.

    Manufar 'yan majalisar shi ne a kawar da tsarin mulki na shugaba mai cikakken iko, a koma bin tsarin gwamnati mai firaminista.

    A filinmu na Gane Mani Hanya na wannan makon, Buhari Muhammad Fagge ya tattauna da Barsita Muhammad Bello Shehu, wanda aka fi sani da MB Shehu, ɗaya daga cikin 'yan majalisar da ke kokarin ganin a sauya tsarin mulkin, inda ya soma da bayani kan abin da ya ja hankalinsu a wannan lokacin.

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  17. Mutuwar Navalny ta janyo zanga-zanga, alhini da kuma kame a duniya

    .

    Asalin hoton, Shutterstock

    Mutuwar jagoran adawar Rasha Alexei Navalny a gidan yari ta janyo ɓarkewar zanga-zanga da alhini a faɗin duniya.

    Magoya bayan ɗan gwagwarmayar siyasar, sun taru a wajen ofisoshin jakadancin Rasha a ƙasashen waje da sauran wurare a faɗin duniya, ciki har da biranen Landan da Paris da Geneva da kuma New York.

    .

    Asalin hoton, Shutterstock

    A birnin Berlin na ƙasar Jamus dandazon mutane sun yi ta faɗin cewa 'A kai Putin Kotun Duniya', haka a a ofishin jakadancin Rasha da ke birnin Landan masu zanga-zangar sun riƙe kwalayen da ke nuna cewa ''Navalny ne gwarzonmu''.

    Fiye da mutum 100 ne kuma suka tsaya a gaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Geneva, inda suka riƙe hotunan Navalny tare da ajiye furanni.

    Haka ma an gudanar da zanga-zanga a Rasha.

    Hotunan da aka yaɗa a shafukan sad zumunta sun nuna yadda mutane ke ajiye furanni a biranen Moscow da Saint Petersburg domin nuna alhininsu ga rasuwar jagoran adawar.

    Rahotoni sun ce fiye da mutum 100 aka tsare sakamakon zanga-zangar a biranen Rasha.

    .

    Asalin hoton, Reuters

  18. 'Yansanda sun kama mutum takwas da suke zargi da sace ɗaliban Ekiti

    ..

    Asalin hoton, x/Nigerian Police

    Rundunar 'yan sandan jihar Ekiti ta ce ta kama mutum takwas da suka yi garkuwa da wasu ɗalibai da malaman makarantar Apostolic Faith a Emure-Ekiti, da ke jihar.

    Kwamishinan 'yansandan jihar CP Adeniran Akinwale, ne ya bayyana haka lokacin da yake holen masu garkuwar a shalkwatar rundunar da ke birnin Ado-Ekiti, ranar Juma'a.

    Mista Akinwale ya ce an kashe ɗaya daga cikin masu garkuwar a lokacin musayar wuta da jami'an 'yansanda.

    Kwamishinan ya ƙara da cewa maharan su ne kuma suka yi garkuwa da shugaban jam'iyyar APC na jihar, Hon. Paul Omotoso a shekara 2023

    ''Binciken farko ya nuna cewa Sumo Karami, tare da yaransa ne suka sace tare da yin garkuwa da ɗaliban nan da malamansu a Emre-Ekiti ranar 29 ga watan Janairu'', in ji kwamishinan.

    Ya ƙara da cewa “Mun gano wayar da masu garkuwar suka yi amfani da ita wajen kira domin neman kuɗin fansa don sakin ɗaliban da malaman a hannun maharan''.

    “Haka kuma an gano wasu abubuwa tare da maharan, daga ciki har da bindiga ƙirar AK-47 da wata ƙaramar bindiga da harsasai biyar a cikinta, sannan kuma da abun kurtun AK-47 21 maƙare da harsasan, sa sauran abubuwa'', in ji mista Akinwale.

  19. Ra'ayi Riga: Kan tashin farashin dala a Najeriya

    Shirin Ra'ayi Riga na wannan makon ya duba batun tashin farashin dala mafi girma a tarihin Najeriya.

    Hakan ne kuma ya sanya darajar kuɗin ƙasar, wato naira ta yi faɗuwar da ba a taɓa gani ba.

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  20. Rijiyar da ta haura shekara dubu a jihar Gombe

    Rijiyar 'Buzurdalla' wata rijiya ce a garin Wawa da ke ƙaramar hukumar Kaltungo ta jihar Gombe, arewacin Najeriya.

    Tarihi daga mazauna garin ya nuna cewa ana amfani da rijiyar tun fiye da shekaru 1000 da suka gabata.

    Dagacin garin na Wawa, Abubakar Sadik Lawal ya ce wata goɗiyar doki ce ta gano rijiyar.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon