Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir and A'isha Babangida
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kama mutanen da take zargin 'yan Hamas ne a Rafah
A wata sabuwar sanarwa da ta fitar, rundunar sojin Isra'ilar ta IDF ta ce kama wasu mutanen da dama da take zargin 'yan Hamas ne yayin samamen da take yi a asibitin Naseer da ke birnin Rafah.
Rundunar ta nanata cewa burin "hare-harenta na kai wa ga gaci" shi ne kama 'yan Hamas da suka hada wadanda suke da hannu a harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023 a kasar Isra'ila
IDF ta ce ta tuntubi darektan asibitin ranar Talata, inda ta nemi da a kawo karshen mayakan Hamas da ta kira "'yan ta'adda .
Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce rundunar Isra'ila na tursasa yan gudun hijra
Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta shaida wa BBC cewa dakarun sojin Isra'ila na IDF na yin amfani da karfi wajen an giza keyar 'yan gudun hijra a Rafah.
Mai magana da yawun ma'aikatar, Dr Ashraf al-Qudra ya ce rundunar IDP "sun tilasta ragowar masu neman mafaka da iyalan jami'an lafiya cewa su bar asibitin Nasser da asubar yau a lokacin ana tsaka da luguden bama-bamai."
Ya ce sojojij Isra'ila sun nemi ma'aikatan asibitin da su kwashe dukkannin marasa lafiya da suka hada da wadanda suke sashen kula na musamman, zuwa wani gini na daban da ke asibitin.
An dai zargin cewa dakarun na IDF dun rushe katangar kudancin asibitin da motar rushe gine-gine tare da kai wa inda motocin daukar marasa lafiya suke hari da kuma rumfunan 'yan gudun hijra da manyan kaburburan da ke asibitin.
Ma'aikatar ta kuma ce an kashe Falasdinawa 87 sannan an jikkata fiye da 1000 sakamakon hare-haren Israila a awanni 24 da suka gabata.
Kawo yanzu wadanda hare-haren suka yi sanadin kisan su sun kai mutum 28,663, inda kuma wadanda suka jikkata suka kai 68,395.
Mene ne tukwicin zaman lafiya a yaƙin Isra'ila da Hamas?
Mutanen da suka samu mafaka a cocin Gaza 'na cikin fargaba'
Isra'ila da Gaza: Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da kai farmaki a Rafah
Asalin hoton, Reuters
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dage da cewa dakarunsa za su ci gaba da kai farmaki a kan Rafah na Gaza, inda ya ki amincewa da rokon da aka yi a waje na sake nazari kan kai hare-hare a Gaza.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron na cikin wadanda suka yi wa Netanyahu gargadi, yana mai shaida masa irin asarar rayukan da Isra'ila ta yi a Gaza ba abin da za a iya jurewa ba ne.
Amma Netanyahu ya umarci sojojinsa da su shirya kai farmaki ta kasa kan Gaza.
Falasdinawa kimanin miliyan 1.4 ne ke da mafaka a Rafah, wanda tuni aka kai harin bam.
Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da kai hari mai karfi, yana mai bayyana cewa dole ne a kawar da ƙungiyar Hamas da ke iko da Gaza daga kudancin birnin.
"Za mu yi yaƙi har sai mun sami cikakkiyar nasara kuma wannan ya haɗa da ɗaukar mataki mai ƙarfi a Rafah" in ji shi.
Shugaba Macron ya yi waya da Netanyahu a ranar Laraba inda ya ce dole ne a daina ayyukan Isra'ila a Gaza.
Ya bayyana cewa, "Kasar Faransa na adawa da harin da Isra'ila ta kai a Rafah, wanda zai iya haifar da bala'in jin ƙai mai girman gaske".
Firaministan Australia da Canada da New Zealand sun fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa inda suka nuna matukar damuwarsu kan cewa harin da sojojin Isra'ila ke shirin kai wa kan Rafah zai zama wani mummunan bala'i.
Netanyahu ya yi fatali da buƙatar Amurka ta kafa ƙasar Falasɗinawa
Falasɗinawa na fargaba gabanin hare-haren Isra'ila a Rafah
Masar ta sabunta alaƙa da Turkiyya bayan shekaru 10
Asalin hoton, Reuters
Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Masar Abdel Fattah al-Sisi sun sanar da buɗe wani sabon babi na dangantaka bayan shafe shekaru 10 suna rashin jituwa.
Ƙasashen biyu sun yanke hulda a shekarar 2013 bayan Al- Sisi, ministan tsaro na lokacin, ya hamɓarar da shugaba Mohamed Morsi, wanda ke ƙawance da Ankara.
A wani taron hadin gwiwa da suka yi a birnin Alkahira a ranar Laraba, shugabannin biyu sun ce suna son sabunta dangantakarsu.
Wannan dai ita ce ziyarar farko da shugaban na Turkiyya ya kai Masar cikin fiye da shekaru 10.
An sanya hannu kan yarjejeniyoyin ƙasashen biyu da dama yayin ganawar.
Shugabannin biyu sun kuma soki yadda Isra'ila ke gudanar da yakin da ake yi a Zirin Gaza tare da yin kira da a tsagaita wuta.
Ɓacin rai na ƙaruwa yayin da Al-Sisi ke neman wa'adi na uku a Masar
Me za a tsammata a sabon wa'adin mulkin Shugaba Erdogan?
Najeriya na kan tsini - Sultan Sa'ad
Asalin hoton, Getty Images
Mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bayyan afargabar cewa Najeriya na fuskantar barazanar tsaro bisa la'akari da yadda dumbin matasan kasar ke fama da rashin aikin yi da yunwa.
Sarkin Musulmin ya yi wadannan kalamai ne yayin da yake jawabi a wani taron majalisar sarakunan gargajiya ta arewacin Najeriya ranar Laraba a Kaduna.
Muhammad Sa'ad Abubaakr III ya ce " mun shiga wani sabon zango na shugabanci. An samu sabbin gwamnoni inda kuma wasu suka yi tazarce a karo na biyu amma har yanzu muna fama da matsalar tsaro.
Babban matsalar ma ita ce karuwar talauci. Mafi yawancin mutanenmu ba su da hanyoyin samun abin da za su ci su sha".
Ya kara da cewa idan dai har gwamnoni na son zaman lafiya a jihohinsu, dole ne su sama wa matasa aikin yi sannan dole ne su yi aiki tare da sarakunan gargajiya.
"Dole ne mu sama wa dimbin matasanmu masu zaman kashe wando ayyukan yi. Na sha fadar cewa muna wasa da bakin wuta. Saboda samun miliyoyin matasa ba tare da ayyukan yi ba sannan suna fama da yunwa, hakan na nufin muna fuskantar barazana."
Daga karshe ya ce ya yi amannar cewa za a samu mafita duk da cewa "Najeriya ba ta taba gaza samar da mafita ba illa dai kawai ba a iya aiwatarwa".
Ƙarin hauhawar farashin da aka daɗe ba a gani ba na gigita ƴan Najeriya
Abubuwan da JNI ta faɗa kan tsadar rayuwa a Najeriya
Sojojin Isra'ila na musamman sun shiga asibitin Nasser na Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta na musamman sun shiga asibitin Nasser da aka yi wa kawanya a kudancin Gaza.
Rundunar ta ce dakarun za su gudanar da aiki ba tare da kuskure ba. Ta ce mayaƙan Hamas na buya a cikin asibitin kuma gawarwakin ƴan Isra'ila da aka yi garkuwa da su ma na iya kasancewa a wurin.
Hakan dai na zuwa ne kwana guda bayan da dakarun tsaron Isra'ila (IDF) suka umarci dubban mutanen da suka rasa matsugunansu da su bar wurin.
Asibitin dai shi ne mafi girma a kudancin Zirin Gaza.
Hotunan faifan bidiyo da aka yi a baya sun nuna cewa ma'aikatan kiwon lafiya na gaggawar ɗaukar marasa a gadon ɗaukar marasa lafiya ta wani kofa da ke cike da hayaki.
Yadda Isra'ila ke shirin ƙaddamar da hari kan mafakar Falasɗinawa ta Rafah
Abun da ya kamata ku sani kan yarjejeniyar Isra'ila da Masar wadda ke fuskantar barazana
Somaliya ta hana amfani da takunkumin fuska a Mogadishu saboda tsaro
Asalin hoton, AFP
Hukumomi a Somaliya sun hana sanya abin rufe fuska a Mogadishu babban birnin kasar, saboda matsalar tsaro.
Kakakin gwamnatin Mogadishu, Salah Dheere, ya ce ana amfani da sanya abin rufe fuska don boye sirri da kuma sauƙaƙa ayyukan muggan laifuka.
An dai yi amfani da abin rufe fuska sosai yayin annobar korona.
Hukumomin ƙasar sun kuma haramta sanya hula da ɗaukar makamai a cikin motocin jama'a.
Sai dai ba a haramta amfani da hulunan gargajiya da dattawa ke sanyawa ba.
An yanke shawarar ne a wani taron tsaro na baya-bayan nan da aka yi a Mogadishu, wanda shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya jagoranta.
Ƙasar Somaliya dai ta shafe shekaru tana fama da matsalar rashin tsaro, inda babbar barazana ke fitowa daga ƙungiyar ta'addanci ta Al-Shabab.
Ƙungiyar da ke da alaƙa da al-Qaeda ta ƙara kaimi wajen kai hare-hare a wani mataki na mayar da martani tun bayan da gwamnatin Shugaba Mohamud ta kaddamar da farmaki kan ƙungiyar a watan Agustan 2022.
Akwai yiwuwar fari ya kashe mutum 43,000 a Somalia a bara - MDD
Abubuwan da ba ku sani ba game da ƙasar Somaliya
Ba za mu amince lauyoyin Birtaniya su yi aiki a Najeriya ba - NBA
Asalin hoton, Nigerian Bar Association
Shugaban ƙungiyar lauyoyin Najeriya ,NBA Yakubu Maikyau, ya ce kungiyar ba za ta bari lauyoyin Burtaniya su yi aiki a Najeriya ba.
Wannan dai na da nasaba da rattaba hannun da ake zargin gwamnatin Najeriya da Birtaniya suka yi a kan yarjejeniyar kasuwanci da zuba jari ta ETIP.
Gidan talbijin na Channels ya rawaito cewa babban lauyan ya bayyana cewa an sanya hannu kan yarjejeniyar ba tare da amincewar NBA ba, yana mai cewa kungiyar za ta ci gaba da adawa da duk wata yarjejeniya da za ta kawo cikas ga dokar ƙasar.
“Wane ƙoƙari ne gwamnatin Najeriya ta yi don ganin lauyoyin Najeriya sun sami damar yin amfani da yanayin doka a Birtaniya? Abin da ya fi ban takaici shi ne yadda aka kulla yarjejeniyar ba tare da shigar da ƙungiyar lauyoyin ƙasar kan rubutun yarjejeniyar ba,” inji shi.
Maikyau ya kuma buƙaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya kafa dokar ta-baci a cikin tabarbarewar tsaro da ya addabi kasar.
Yayin da yake kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dauki kwararan matakai na magance matsalar rashin tsaro, Maikyau ya ba da shawarar saka hannun jari ga jami’an tsaro a kasar.
Yadda rikicin El-Rufai da NBA ya ta da tsohon liƙin da ke jikin ƙungiyar lauyoyin Najeriya
Nawa ya kamata ma'aikaci ya ɗauka a matsayin albashi mafi ƙaranci a Najeriya?
'Ana shirin mayar da wasu ofisoshin NUPRC daga Abuja zuwa Legas'
Asalin hoton, @NUPRCofficial/X
Hukumar NUPRC mai sa ido kan harkokin man fetur a cikin ruwa a Najeriya ta soma shirye-shiryen sauya matsugunnin wasu ofisoshinta daga Abuja zuwa Legas.
Hakan na zuwa ne bayan matakin mayar da wasu ma'aikatan babban bankin Najeriya, CBN da sauya matsugunin hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta Najeriya - FAAN zuwa Legas.
Wasu ma'aikatan NUPRC sun bayyana matukar damuwa kan wannan yunkurin saboda a cewarsu zai shafi yadda suke gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Hukumar NUPRC ita ce ke lura da mai da iskar gas domin tabbatar da bin ƙa'idoji da dokokin da suka dace da kuma lura da wasu dokoki da suka shafi fita da shigowa da albarkatun mai cikin Najeriya.
NUPRC da a baya ake kira DPR a ƙarƙashin ma'aikatar albarkatun man fetur ta Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito tuni aka aika wa sassan hukumar na NUPRC wata wasika da ke nuna sabon matakin da ake kokarin dauka na kai wadansu ma'aikata zuwa Legas.
A yanzu haka dai ana gina wani sabon ofishin hukumar NUPRC mai hawa 10 a Abuja wanda zai kunshi dubban ma'aikata kuma ana sa ran a wannan shekarar za a kaddamar da shi.
Bola Ahmed Tinubu: Tarihin zaɓaɓɓen Shugaban Najeriya
Me ya kawo fargabar rashin tsaro a Lagos?
An kori ministan kuɗin Ghana mai fama da taɓarɓarewar tattalin arziki
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wasu 'yan Ghana na zargin Ken Ofori-Atta kan durƙushewar da tattalin arzikin ƙasar ya yi
Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo ya maye gurbin ministan kudi Ken Ofori-Atta yayin da kasar da ke Afirka ta yamma ka fama da durkushewar tattalin arziki.
Mr Ofori-Atta ya kasance minista tun 2017 kuma ya fuskanci suka saboda taɓarɓarewar tattalin arziki mafi muni da ƙasar ta taɓa fuskanta cikin shekaru.
Ana tsaka da fuskantar matsalar a 2022 ne, hauhawar farashi ta zarce kashi 50 cikin 100 sannan gwamnati ta gaza biyan bashi.
Daga bisani ta gyara yanayin basukanta da masu lamuni domin cancantar karbar tallafi daga asusun ba da lamuni na duniya IMF.
A ranar Laraba ne aka naɗa Mohammed Amin Adam wanda ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin ministan makamashi kuma ƙaramin minista a ma'aikatar kuɗi domin maye gurbin Mr Ofori-Atta.
Ana sa rai Mista Adam zai jagoranci shirin IMF na tallafin dala biliyan uku domin farfaɗo da komaɗar tattalin arzikin ƙasar.
Shugaba Akufo-Addo ya maye ministoci 12 a garambawul ɗin da ya yi wa majalisar ministocinsa ranar Laraba gabanin babban zaɓen shugaban ƙasa da za a yi cikin watan Disamba.
Ko yajin aikin ƴan kasuwar Najeriya zai samar da mafita kan tsadar rayuwa?
Dalili hudu na yawan karyewar darajar naira
Faransa za ta karɓi baƙuncin taron ba da agaji ga Sudan
Asalin hoton, AFP
Faransa ta ce za ta karɓi baƙuncin wani taro a birnin Paris a cikin watan Afrilu domin tara agaji ga Sudan da yaƙi ya ɗaiɗaita.
Ministan Harkokin Wajen Faransa, Stephane Sejourne, ya ce bai kamata a manta da mummunan halin da ake ciki na jin kai ba a Sudan.
Dubban mutane ne aka kashe tun bayan ɓarkewar yaƙin da aka yi a shekarar da ta gabata tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa kai na RSF.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da miliyan shida ne suka rasa matsugunansu, kuma fiye da rabin al’ummar Ƙasar na buƘatar taimako.
Rikicin Sudan: Ana jin harbe-harbe duk da yarjejeniyar tsagaita wuta
Waiwaye: Fara kwasar 'yan Najeriya daga Sudan da cikar 'Yar'adu'a shekara 13 da rasuwa
Na fi son yin aiki da Biden a kan Trump – Putin
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Vladimir Putin da Joe Biden sun yi haduwar karshe a Geneva cikin 2021.
Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce ya fi son yin aiki tare da Joe Biden maimakon Donald Trump bayan zaben shugaban Amurka a watan Nuwamba.
Mista Putin ya kuma ce shugaba Biden ya fi zama gogaggen dan siyasa, fiye da wanda ya gada.
Sai dai ya ce Rasha za ta yi aiki da duk wanda jama'ar Amurkan suka aminta da shi.
Shugaba Putin ya fadi haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin wani dan jarida, RshaPavel Zarubin
Ya ce "ya fi kwarewa.Ya fi hangen nesa.Tsohon dan siyasane. Amma za mu yi aiki tare da duk shugaban da Amurka suka aminta da shi.
Mr Putin ya kuma yi watsi da batun shekarun Biden da kuma lafiyar kwakwalwarsa, yana mai cewa lafiya lau ya gansa a lokacin da suka hadu shekaru uku da suka gabata.
Joe Biden dai da Donald Trump dukkaninsu sun fukanci suka da kuma bincike kan lafiyar kwakwalwarsu da cancantarsu ta shugabanci.
Donald Trump: Ba na tsoron Vladmir Putin
Batun Ukraine: Putin ya faɗa wa Biden cewa sanya wa Rasha ƙarin takunkumi zai zama babban kuskure
Mutum ɗaya ya mutu, 21 sun ji rauni a hari kan masu kallon ƙwallo a Amurka
Asalin hoton, Getty Images
'Yan sanda a birnin Kansas na Amurka sun ce an harbi mutum 22 a wani taron gangamin samun nasarar wasan kwallon kafar Amurka.
Akalla mutum daya aka tabbatar da mutuwarsa kawo yanzu yayin da wasu da dama ciki har da yara kanana
ke cikin mawuyacin hali bayan samun munanan raunuka ciki har da yara kanana
An bude wa jama’a wuta ne a harbi irin na kan mai uwa da wabi a lokacin da magoya bayan Kansas city chiefs ke murnar nasara a wasan kwallo mafi girma a Amurka.
Kawo yanzu yan sanda sun ce ba a san dalilin harbin ba amma sun ce sun sun kama mutum uku da suke zargi.
Shugaban yan kwana-kwana na Kansas City, Ross Grundyson ya ce akwai mutum takwas da muke tunanin suna cikin hali na rai kwakwai mutu kwakwai, akwai kuma bakwai da ke da mummunan raunika da kuma shida masu kananan rauni kuma an yi kokarin kai wadanda ke cikin mawuyacin hali asibiti cikin minti 10.
Da take magana da manema labarai yayin da take shirin hawa jirgi zuwa Jamus domin halartar wani taron tsaro a Munich, mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta bayyana kaduwarta.
Ta ce yau ya kamata ta kasance rana ta murna inda mutane suka hadu suna farin ciki amma kuma wata rana ce da Amurka ta shiga tashin hankali na harbin bindiga.
Rikicin bindiga ya fi halaka yara a Amurka, ba wasu cutuka ko kuma hatsarin mota, kuma wani abin da za a iya hanawa.
Magajin garin Kansas City, Quinton Lucas ya ce za su yi bincike. Ya ce ya kadu kamar kowa, kuma "za mu yi cikakken bincike, za a gurfanar da duk wanda ke da hannu tare da tabbatar da kare kanmu.
Lamarin dai ya girgiza Amurka, shugaba Biden a sanarwar da fadarsa ta fitar, ya ce tashin hankali ne ga Amurkawa da kuma wani abin kunya ga rashin daukar mataki kan tashin hankalin da ya shafi bindiga.
Harin Texas: Ɗan bindiga ya harbe mutum 21 a Amurka
Amurka ta kai harin ramuwa a kan Iraqi da Syria
Maraba!
Jama'a assalamu alaikum. Barka da kasancewa tare da mu a wannan shafi na Kai Tsaye da BBC Hausa ke kawo muku a kodayaushe.
A shafin, muna wallafa labarai da rahotanni game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran kasashe makwabta.
Akwai shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da Instagram har ma da Tuwita inda muke dora wasu labaran da ma hotunan bidiyo.