Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir and A'isha Babangida

  1. An sake komawa tattaunawar tsagaita wuta a Gaza yayin da Isra'ila ke kai hari a Rafah

    An koma kan teburin tattaunawa kan yadda za a cimma tsagaita wuta a Gaza, a birnin Alƙahira na ƙasar Masar, kamar yadda kafofin watsa labaru na Masar suka ruwaito.

    Manyan jami'an Amurka da Isra'ila da Masar da kuma Qatar ne ke yin ganawar, yayin da Isra'ila ke fuskantar ƙarin matsin lamba da ta daina ruwan bama-bamai a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.

    Kimanin mutane 1.5 miliyan ne ke cunkushe a ƙaramin garin da ke bakin iyaka, cikin fargabar hare-haren da Isra'ilan ke kaiwa ta ƙasa.

    Firai ministan Isra'ilan ya yi watsi da tayin tsagaita wutar da ya kira ta "yaudara" da Hamas ta yi a makon jiya.

    Benjamin Netanyahu ya ce "an kusa samun gagarumar "nasara" ta ƙarshe a Gaza a cikin ƴan watanni.

    Inda daga bisani ya umarci dakarunsa da su faɗaɗa hare-haren da suke kaiwa ta ƙasa, yana mai cin alwashin sai ya ga bayan mayaƙan Hamas da ke Rafah.

    Amma shugaban hukumar kare haƙƙin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya ce duk wani harin da za a kai birnin zai "munana" kuma akwai yiwuwar kashe mutane da dama."

    Shugaban Amurka, Joe Biden ya yi kira da a kare rayukan fararen hular da ke yankin.

    Birnin na Rafah ya fuskanci zafafan hare-hare ta sama a cikin kwanakin nan daga Isra'ila, inda aka bayar da rahotannin rasa rayuka.

  2. 'Ƴan bindiga sun kashe ƴansanda da garkuwa da mutane 40 a Zamfara'

    Masu garkuwa da mutane sun kashe ƴansanda biyu da wasu fararen hula tare da garkuwa da mutane kimanin 40 a ƙauyen Kasuwar-Daji da ke ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a jihar Zamfara.

    Wani mazaunin ƙauyen ya tabbatar wa BBC cewa ƴan bindigar sun kai harin ne da sanyin safiyar yau Talata inda suka riƙa yin harbin mai-uwa-da-wabi.

    Hakan na zuwa ne kimanin mako biyu bayan da gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare ya ƙaddamar da rundunar Askarawan Zamfara, waɗanda za su taimaka wajen yaƙi da matsalar tsaron da jihar ke fuskanta.

    Zamfara na daga cikin jihohin da suke fama da matsalar tsaro, inda ƴan bindiga ke far wa ƙauyuka suna kashewa da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

    Gwamnatin Tarayya, wadda ita ce kundin tsarin mulki ya ɗora wa alhakin tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar, na cewa tana ɗaukan matakan da suka kamata wajen shawo kan lamarin.

    A tattaunawarsa da BBC cikin kwanakin baya, ƙaramin minstan tsaro na Najeriya Bello Matawalle ya ce ana ɗaukar matakan kawar da matsalar baki ɗaya.

    Sai dai duk da haka ana ci gaba da samun kashe-kashen al'umma da garkuwa da su domin neman kuɗin fansa.

  3. Ana zargin dakarun gwamnatin Ethiopia da kisan kiyashi

    Aƙalla fararen hula 45 aka kashe a lokacin da sojojin gwamnatin Ethiopia suka kai wani samame gida-gida a watan jiya a garin Merawi da ke arewacin ƙasar, a cewar ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama.

    Waɗanda suka shaida lamarin sun ce wata mace mai juna biyu na daga cikin waɗanda aka harbe.

    Kafin daga bisani ta cika a asibiti, a cewar masu bayar da kulawa ga marasa lafiya.

    Sai dai gwamnatin ƙasar ba ta ce komai ba a kan kisan, yayin da gwamnatin Amurka da ƙungiyar Tarayyar Turai suka yi kira da a yi bincike mai zaman kansa.

    Tashin hankalin shi ne mafi muni da aka taɓa fuskanta a yankin Amhara tun bayan na watan Agusta lokacin da wata ƙungiya mai ƙarfi ta masu ɗauke da makamai ta Fano ta yi wa gwamnatin bore.

    Kafin sannan dai ƙungiyar ƙawa ce ga dakarun gwamnatin, inda suke haduwa suke yaƙar TPLF abokiyar gabarsu da ke makwabciyar yankin Tigray.

    Bayan cimma yarjejeniya a Tigray ne aka amince a karɓe makaman Fano da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

    Amma Fano ba ta son a karɓe mata makamai saboda tsoron kada makwabtansu su dinga kawo musu hari.

    .

  4. 'Ba ni da masaniyar biyan masu sa ido a zaɓe $6m da Emefiele ya yi'

    Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha, ya ce bai san batun wata takarda ba da tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, CBN, Godwin Emefiele ya yi amfani da ita wajen biyan sama da dalar Amurka 6.2 miliyan ga masu sanya ido a zaɓe na ƙasashen waje.

    Boss Mustapha ya bayyana hakan ne a gaban wata babbar kotu da ke Abuja a ranar Talata.

    Tsohon sakataren gwamnatin wanda yana daga cikin shaidu a ƙarar da ake tuhumar mista Emefiele, ya ce a tsawon shekarun da ya yi yana rike da wannan muƙamin ba shi da masaniya kan takardar.

    Kafar yaɗa labarai a cikin ƙasar, channel TV ta ce mista Mustapha ya kuma bayyana wa kotun cewa, ba daga ofishinsa ta fito ba kuma ba daga fadar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari takardar biyan kuɗaɗen ta fito ba.

    Tsohon sakatren gwamnatin tarayyar ya kuma shaida wa kotun cewa babu ruwan gwamnatin tarayyar da biyan masu sa ido na ƙasashen wajen kuɗaɗe.

    Mista Emefiele na fuskantar tuhume-tuhume 20 a shari'ar, waɗanda suka haɗa da cin hanci da rashawa, haɗa baki domin aikata laifi, da cin amana da ungulu da kan zabo da kuɗaɗen da suka kai dalar Amurka $6,230,000.

    Ana zargin tsohon shugaban na CBN da yin amfani da sa hannu na jabu domin karɓar kuɗaɗen ba bisa ƙa'ida ba.

    Masu sa ido a babban zaben ƙasar da aka yi a shekarar 2023 na ƙasashen waje ake ikirarin an biyan kuɗaɗen.

  5. ASUU ta gargaɗi gwamnatin Najeriya kan buƙatunta

    Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU ta bayyana rashin jin daɗinta kan abun da ta kira halin-ko-in-kula da gwamnatin ƙasar ta nuna kan buƙatunta.

    Shugaban kungiyar reshen jihar Kano, Farfesa Abdulkadir Muhammad, ya ce ƙungiyar na jan hankalin gwamnati ne a yanzu gabannin ɗaukar mataki.

    Ƙungiyar ta ce shekara ɗaya ke nan da ta shiga yarjejeniya da gwamnatin kan dalilan da suka kai malaan jami'oin ƙasar shiga yajin aiki, amma gwamnatin ba ta cika ko ɗaya daga cikin yarjejeniyoyin da suka kulla ba.

    Inda ta koka cewa hatta albashin watan Janairu da ya wuce, gwamnatin ƙasar ta biya malaman ne da manhajar IPPIS, saɓanin cire su da ƙungiyar ta buƙaci a yi.

    A baya dai ƙungiyar ta shiga wani dogon yajin aiki na wata da watanni, wanda bayan shiga tsakani aka samu maslaha ta janye yajin aikin bisa alkawarin biya musu bukatun.

  6. Hisbah ta kama ƴar Tiktok Murja Kunya

    Rundunar Hisbah a jihar Kano ta ce ta kama shahararriyar ƴar TikTok din nan Murja Ibrahim Kunya da laifin wallafa wasu abubuwan da ba su dace ba da kuma waɗanda ba na Musulunci ba a shafin sada zumunta na TikTok.

    Makwanni biyu da suka gabata, Hisbah ta ƙaddamar da farautar wasu ƴan Tiktok guda shida waɗanda suka ce suna saɓa wa ka’idojin musulunci a kullum wajen amfani da kafafen sada zumunta.

    Kakakin Hisbah Lawal Fagge ya shaida wa BBC cewa an kama Murja Ibrahim Kunya da sanyin safiyar Talata, tare da saurayinta.

    "Jami'anmu sun kama ta ne da karfe 1:00 na rana a gidanta tare da saurayinta, wanda shi ma yana tare da mu."

    “A baya dai, makwabtanta sun kawo mana korafi game da halinta. A yanzu haka muna kan bincike kafin daukar mataki na gaba,” inji shi.

    Ana zargin Murja da yin amfani da kalaman ɓatanci da rashin kunya a cikin bidiyonta, wanda dubban mutane ke kallo.

    Ba ta ce uffan ba kan wannan zargi, amma an gan ta a wani faifan bidiyo da ba a tantance ba yana yawo a shafukan sada zumunta tun bayan kama ta.

    A bidiyon, an jiyo ta tana cewa ba ta saci komai ba, kuma ta gode wa Allah a kan hakan.

    Kano dai na da mafi yawan al'ummar Musulmi kuma tsarin shari'a na Musulunci yana aiki tare da tsarin doka a jihar.

  7. Habasha da yankin Tigray sun amince da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya

    Gwamnatin ƙasar Habasha da yankin Tigray da ke arewacin ƙasar sun amince da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da suka rattabawa hannu a shekarar 2022 domin kawo karshen yaƙin basasa na tsawon shekaru biyu, kamar yadda gidan talabijin na Dimtsi Weyane ya ruwaito a jiya.

    Shugaban yankin Tigray Getachew Reda ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai bayan tattaunawa da firaminista Abiy Ahmed da majalisar ministocinsa.

    Getachew Reda ya ce an cimma matsaya kan mayar da mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa gidajensu da kuma mutunta hadin kan yankin Tigray da kuma bayyana amincewa da kungiyar masu rajin kare haƙƙn ƙabilar Tigray wato TPLF a matsayin jam'iyyar siyasa," in ji Dimtsi Wayane TV.

    Mutanen da suka rasa matsugunansu a yankin na Tigray sun kasa komawa gidajensu sakamakon takaddama da yankin Amhara da ke makwabtaka da su.

    A ‘yan watannin nan dai an yi ta zarge-zarge a tsakanin ɓangarorin biyu dangane da cika alkawarin da aka dauka na aiwatar da yarjejeniyar, musamman kan matsayin yankunan da ake takaddama a tsakanin yankunan Tigray da Amhara.

    Gwamnatin tarayya da kungiyar TPLF sun sanya hannu kan yarjejeniyar a Afirka ta Kudu a watan Nuwamba 2022.

  8. Tinubu ya karrama yan wasan Super Eagles da lambar girmamawa ta kasa

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya karrama dukkan yan wasan Super Eagles da lambar girmamawa ta MON saboda kokarin da suka yi a gasar cin kofin Afirka ta 2023.

    Shugaba Tinubu ya yi haka ne bayan ya karbi bakuncin yan wasan da yan tawagar kungiyar A Fadarsa da ke Abuja, bayan komawarsu gida daga gasar ta Afcon da aka yi a Ivory Coast.

    Shugaba Tinubu ya yaba wa kungiyar ta Super Eagles saboda yadda suka bai wa jama'ar Najeriya kwarin gwiwa.

    Ya ce ba abu ne mai sauki jurewa rashin nasara ba amma Super Eagles ta nuna kwarewa a wasanninsu da kuma nuna dabi'ar rashin gazawa.

    Tinubu dai ya bayyana cewa yana matukar alfahari da su.

    Najeriya dai ta tsallaka zuwa zagayen karshe na gasar inda ta zo ta biyu a gasar bayan da Ivory Coast mai masaukin baki ta doke ta da ci biyu da daya.

  9. An harba wa manoman Indiya masu zanga-zanga hayaki mai sa hawaye

    'Yan sanda a arewacin Indiya sun harba hayaki mai sa hawaye domin hana gomman manoman da ke neman saukin farashi ga kayan amfanin gona yin zanga-zanga a Delhi, babban birnin kasar.

    An kewaye babban birnin da wayoyi da bululluka tare da katange wurare uku domin hana tasirin zanga-zangar.

    Gwamnati na fargabar ka da a samu maimaicin tashin hankalin da aka yi a 2020 inda gommai suka mutu a zanga-zangar da aka shafe shekara daya ana yi wadda ta zo karshe bayan ministoci sun amince su soke dokokin aikin gona da suka janyo cece-kuce.

    Sai dai shekara uku bayan nan, manoman sun ce ba a biya sauran bukatunsu ba.

    Manoman Indiya na da tasiri sosai a zaben kasar kuma masu sharhi sun ce gwamnatin Firaiminista Narendra Modi za ta yi taka tsan-tsan wajen nuna musu wariya. Jam'iyyarsa ta BJP na neman mulki karo na uku a babban zaben da za a yi bana.

    Manoma da akasarinsu sun fito daga Punjab sun ce suna son tsallaka wa Haryana zuwa Delhi cikin lumana amma ba su samu damar yin haka ba.

    An ruwaito rikici tskanin 'yan sanda da masu zanga-zanga a kan iyakar Shambhu kuma lamarin ya kazanta.

  10. Amurka ta amince da fitar da dala biliyan 95 don taimaka wa kawayenta

    Majalisar dattawan Amurka ta amince da wani kwarya-kwaryar kasafi na dala billion 95 domin tallafa wa kawayenta.

    Za dai a yi amfani da kudaden ne wajen taimaka wa kasashen da suka hada da Ukraine da Isra'ila da Taiwan.

    Kafin amincewar dai, kudirin ya fuskanci tirjiya a zauren majalisar duk har yanzu ana cewa kudirin na fuskantar suka daga 'yan jam'iyyar Republicans da ke zaure.

  11. Ministan tsaron Liberia ya yi murabus bayan zanga-zangar da matan sojoji suka yi

    A jiya ne sabon ministan tsaron kasar Laberiya ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon zanga-zangar da matan aure da zawarawan sojojin da suka rasu suka yi na nuna adawa da nadin nasa, kamar yadda Shafin intanet mai zaman kansa na Daily Observer ya ruwaito.

    Murabus ɗin Price Charles Johnson ya zo ne kwanaki biyu bayan da matan suka bai wa shugaba Joseph Boakai wa'adin sa'o'i 24 da ya kori ministan sakamakon cin zarafin da ya yi wa sojoji a lokacin da yake shugabantar sojoji tsakanin shekarar 2018 zuwa farkon wannan shekara.

    Matan da zawarawan sun yi nuni da karancin albashi da rashin tsaro da karancin wutar lantarki da kuma almundahana a tsakanin sojoji.

    A cikin wasikar murabus din, ministan ya ba da misali da "rikicin siyasa da na jama'a da ke faruwa a halin yanzu sakamakon zanga-zangar da matan suka yi.

    An nada Johnson a farkon wannan watan ne.

  12. Mun biya albashin ma'aikata na Janairu - Gwamnatin Najeriya

    Gwamnatin Najeriya ta ce ta biya dukkan ma’aikata albashinsu na watan Janairu.

    Manyan jami’ai a Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (OHoCSF) da zaɓaɓɓun ma'aikatu da hukumomi na gwamnati ne suka shaida wa jaridar Daily Trust hakan, inda suka ce sun yi mu’amala da wasu ma'aikata da abokan aikinsu kuma suka tabbatar musu da cewa sun ga albashinsu.

    Ɗaya daga cikinsu ta ce ta karbi albashinta a daren Lahadi, kuma tun da karfe 11:00 na safiyar Litinin, ba ta jin labarin wani wanda bai karɓi albashinsa ba.

    Kuma,daraktan yaɗa labarai da hulda da Jama’a na Hukumar ta OAGF, Bawa Mokwa, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa ofishin ya sa ido a kan yadda lamarin ya faru kuma zai iya tabbatar da cewa duk ma'aikatu da hukumomi da ba su ƙarbi albashinsu ba na watan Janairu sun karɓa yanzu.

    Mokwa ya bayyana fatansa cewa ba za a samu irin wannan jinkirin nan gaba ba.

    An daura alhakin jinkirin albashin watan Janairu a kan matsalar fasaha na tsarin biyan albashi na bai ɗaya na gwamnati.

  13. Sakon da Sarkin Kano ya bai wa Remi Tinubu ta fada wa mijinta

    Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya bai wa matar shugaban Najeriya, Sanata Remi Tinubu sako zuwa mai gidanta wato shugaba Bola Ahmed Tinubu.

    Sarkin ya nemi mai dakin Tinubu da ta isar da sakon da masarautar ta samu daga al'umma ga shugaba Tinubu cewa al'umma na fama da yunwa sakamakon tsadar kayan masarufi da ake fama da ita a wannan lokaci.

    "Kayan abinci ya yi tsada. Mutane na shan wahala. Muna samun sakonni daga al'umma da muke shugabanta. Duk da cewa ba abu ne da ya fara yanzu ba. Amma tunda ku Allah ya dorawa shugabancin alhakin warware matsalar ya rataya a wuyanku," in ji Sarkin Kano.

    Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi wannan magana ne a jiya Litinin a fadarsa yayin da matar shugaban kasar ta ziyarci fadar a birnin Kano.

    Sarkin ya kara da cewa "sai kuma abu na biyu. Matsalar tsaro na addabar jama'a duk da cewa shi ma wannan ba lokacinku ya fara ba amma kasancewar su suke shugabanci to su ne Allah ya dorawa nauyin."

    Daga karshe mai martaba Sarkin na Kano ya nemi da gwamnatin tarayya ta waiwayi batun dauke wani sashe na babban bankin kasa da hukumar da ke sanya ido kan tashi da saukar jirage ta kasa daga Abuja zuwa birnin Legas.

    "Muna kira ga shugaban kasa da a waiwayi wadannan batutuwa idan akwai kuskure sai a gyara". In ji Alhaji Aminu Ado Bayero.

    Sarkin ya ce sakon zai fi saurin zuwa kuunuwan shugaban kasancewar uwargidansa aka bai wa.

    • Abubuwan da JNI ta faɗa kan tsadar rayuwa a Najeriya
    • Yadda farashin kayan masarufi ya tashi a lokacin mulkin Tinubu
  14. Afrika ta Kudu za ta tura sojoji 2,900 zuwa DR Congo

    Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya bayar da umarnin tura sojoji 2,900 zuwa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango domin ba da agaji a yaƙin da ake yi da kungiyoyin 'yan tawaye masu ɗauke da makamai a gabashin ƙasar.

    Za a jibge sojojin ne a matsayin wani ɓangare na tawagar kudancin Afirka a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (SAMIDRC), wanda kungiyar ƙasashen yankin ta amince da shi a watan Mayun bara.

    Malawi da Tanzaniya su ma za su ba da gudummawar dakaru a aikin.

    Tawagar dai tana maye gurbin dakarun yankin gabashin Afirka, wadanda suka bar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a watan Disambar da ya gabata, bayan da gwamnatin ƙasar ta dauki tawagar a matsayin ba ta da wani tasiri.

    Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce, tura sojojin kasar Afirka ta Kudun zai ci kuɗin ƙasar Rand biliyan 2 wato dala miliyan 105 kenan kuma zai ci gaba da aiki har zuwa watan Disamba na wannan shekara.

    Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza ƙazamin fada da ya yi sanadin raba dubun- dubatar mutane da muhalansu, wanda ya ƙara kan kusan mutane miliyan bakwai da aka tilastawa barin gidajensu a DR Congo saboda tashe-tashen hankula da dama.

    • Shugaban El Salvador ya tura dubban dakaru domin yakar kungiyoyin miyagu
    • Wace nasara shugabannin Afirka suka cimma a ziyarar sasanta Ukraine da Rasha?
  15. Wani fursuna ɗan ƙasar China ya tsere daga asibitin Ghana

    Wani fursuna ɗan ƙasar China da ke zaman gidan yari na shekara guda bisa samun sa da laifin sata a Ghana, ya tsere a lokacin da yake jinya a wani asibiti da ke Accra, babban birnin kasar.

    Ana dai tsare da Wang Xiao ne a gidan yarin Nsawam da ke kudancin kasar.

    An ba da rahoton cewa a ranar Larabar da ta gabata ne ya ce ba shi da lafiya kuma an kai shi wani asibiti da ke kusa.

    Amma ya kuɓuta daga hannun jami’an gidan yarin da suka yi masa rakiya zuwa asibitin.

    Hukumar kula da gidajen yari ta Ghana ta bayar da sanarwar sake kama Xiao wanda ke fuskantar shari'a a wata shari'ar.

  16. Ƴan farar hula za su yi gangamin adawa da dage zaben Senegal

    Shugaba Macky Sall na kasar Senegal na fuskantar ƙarin matsin-lamba daga ƙungiyoyin fararen hula, waɗanda gamayyarsu ta kira wani gangami a yau, domin nuna rashin amincewa da ɗage zaɓen shugaban ƙasar da a baya aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabarairu.

    Gamayyar ƙungiyoyin sa-kai masu rajin kare dimokuraɗiyya ta sanar da fara wani gangami a sassan Senegal daga ranar Talata, bayan ɗage ranar zaɓen shugaban ƙasar.

    An yi ƙiyasin cewa ƙungiyoyi 170 ne za su shiga zanga-zangar lumanar, wadda kuma za ta zamo mafi girma tun bayan sanarwar ɗage zaɓen.

    Hukumomi dai sun sanar da tsaurara matakan tsaro gabanin zanga-zangar.

    A zanga-zangar baya da aka yi, an kashe wasu matasa uku maza.

    Ƙungiyoyin shiyya irin su Ecowas na fuskantar irin tasu matsin-lambar daga masu ruwa da tsaki, waɗanda ke kiran su gaggauta shiga tsakani don kada yanayin da ake ciki a Senegal ya rikiɗe zuwa tashin hankali.

    • Senegal na dab da shiga ruɗani bayan ɗage zaɓe
    • ƙasashe shida da dakarun Ecowas suka taɓa kai wa yaƙi
  17. Ba za mu sake komawa kungiyar ECOWAS ba – Shugaban sojin Nijar

    Shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya sha alwashin cewa babu ɗaya daga cikin ƙasashen Sahel uku da suka yanke shawarar ficewa daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma wato ECOWAS da za ta koma cikin ƙungiyar.

    Janar Tchiani ya yi wannan jawabin ne a wata hira da ya yi da tashar labarai ta RTN a Yamai babban birnin ƙasar ranar Litinin.

    Hukumomin soji a Burkina Faso da Mali da kuma Nijar a ranar 28 ga watan Janairu, sun sanar da ficewa daga kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka cikin gaggawa.

    Shugabannin kasashen uku sun fitar da wata sanarwa, inda suka ce "shawarar da suka ɗauka ta barin ƙungiyar mai girma ce kuma ba tare da bata lokaci ba".

    “Saboda mu ‘yan kungiyar ne ya sa aka daina samar mana da abinci da magunguna. An kuma katse wutar lantarki kuma an hana mu taba kudadenmu. Don haka, muka tuntubi abokanmu na yankin Sahel kan ficewa daga kungiyar saboda inganta rayuwar 'yan kasashenmu da cewa mu janye daga kungiyar da ke bin ra'ayoyin kasashen waje.Saboda haka mun janye mambanmu daga kungiyar kuma ba za mu taba komawa cikin kungiyar ba." In ji Janar Tchiani.

    Da yake mayar da martani kan sakamakon janyewar ƙasashen daga ƙungiyar Ecowas a kan harkokin tsaro da kasuwanci da zamantakewa, Tchiani ya kara da cewa “yanzu duniya a cure take wuri guda saboda haka ba sai da Ecowas kaɗai za mu rayu ba, don haka, Allah zai ciyar da kowane ɗan adam da ya halitta."

    Dangane kuma da batun hambararren shugaban kasar, Mohamed Bazoum, sai Janar Tchiani ya ce "ba za mu taba sakin Bazoum ba. Sakin Bazoum ya yi daidai da daɓa wa kanmu wuka a ciki wanda hakan zai cutar da 'yan Nijar".

    Kungiyar ECOWAS dai ta sha nuna rashin amincewarta da ficewar kasashen, inda ta nemi da su bi hanyoyin da kungiyar ta shimfida na ficewa daga Ecowas bisa ka'aida kasancewar dukkan kasashen sun rattaba hannu kan yarjejeniyar.

    • Yadda ficewa daga Ecowas zai shafi Mali da Nijar da Burkina Faso
    • Ko taron Ecowas a Abuja zai samar da mafita ga Nijar?
  18. A daina caccakar Iwobi kan rashin nasarar Najeriya a Afcon – Ahmed Musa

    Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ya jagoranci kiraye-kiraye na a kawo karshen cin zarafin da ake yi kan dan wasan tsakiya, Alex Iwobi.

    Wasu magoya bayan kwallon kafa sun yi ta caccakar Iwobi a shafukan sada zumunta inda suke dora alhakin rashin nasarar da Najeriya ta yi a wasanta da Ivory Coast a kan dan wasan mai shekara 27.

    Iwobi ya buga kwallo a wasan na tsawon minti 79 kafin a sauya shi da Alhassan Yusuf.

    Sukar da ake masa a intanet ya sa Iwobi goge duka hotunansa a shafinsa na Instagram.

    Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa da wasu yan Najeriya sun fito domin kare Iwobi inda suka yi allah-wadai da sukar da ake yi wa dan wasan.

    Sun ce ba daidai bane a dora laifin rashin nasarar da Najeriya ta yi a kan mutum daya.

    Ahmed Musa ya bukaci magoya baya da su daina caccakar Alex Iwobi kasancewar rashin nasara a wasa ba abu ne mai dadi ba kuma a cewarsa Iwobi ya yi bakin kokarinsa a wasan kamar yadda sauran yan wasan kungiyar suka yi.

    Zuwa yanzu dai Iwobi bai ce komai ba game da caccakar da ake yi masa.

    • Dukkan kyautukan da aka lashe a Afcon 2023 a Ivory Coast
    • Ivory Coast ta lashe kofin Afirka bayan cin Najeriya
  19. Manyan jami'ai daga Amurka da Qatar da Masar za su gana kan Gaza

    Ana sa ran manyan jami'ai daga Amurka da Qatar da Masar za su ci gaba da tattaunawa domin tabbatar da cewa an tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.

    Za a dai gudanar da tattaunawar ne a birnin Alkahira da ke Masar.

    Shugaban hukumar leken asiri ta CIA, da takwaransa na Masar, da firaministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al Than na daga cikin wadanda za su halarci tattaunawar.

    Shugaba Joe Biden ya ce gwamnatinsa tana aiki dare da rana don ganin an cimma yarjejeniyar da za ta saki mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma zai kai ga tsaigaita wuta na akalla makonni shida.

  20. Biden ya ce dole ne Isra'ila ta kare fararen hula a Rafah

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce fararen hular da ke samun mafaka a Rafah da ke zirin Gaza masu rauni ne kuma dole ne a kare su.

    Ya ce dole ne Isra'ila ta yi ƙoƙarin kare Falasdinawa sama da miliyan ɗaya da ke mafaka a kudancin birnin Gaza.

    Rafah dai ta fuskanci ƙazamin hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a cikin 'yan kwanakin nan, inda aka samu asarar rayuka da dama.

    Wani Likitan Falasdinawa ya shaida wa BBC cewa mutanen Rafah na rayuwa cikin tsoro.

    A makon da ya gabata ne firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa, ya umarci sojojin da su shirya domin fadada ayyukansu na ƙasa zuwa Rafah.

    Ya sha alwashin fatattakar ‘yan bindigar Hamas da ke boye a birnin.

    Babban jami'in kare haƙƙin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Türk ya ce duk wani hari zai kasance "mai ban tsoro" kuma za a kashe yawancin fararen hula.

    Fiye da rabin al'ummar Zirin Gaza mai mutane miliyan 2 da dubu 300 a yanzu haka sun cunkushe a cikin birnin da ke kan iyaka da Masar, wanda ke da mutane dubu 250 kacal kafin yaƙin Isra'ila da Hamas ya ɓarke a watan Oktoba.

    Dayawa daga cikin mutanen da suka rasa matsugunansu suna zaune ne a wasu matsugunai ko tantuna a cikin mawuyacin hali, tare da ƙarancin ruwan sha ko abinci.

    A ranar Lahadin da ta gabata ne rundunar sojin Isra'ila ta ce an kubutar da wasu maza biyu 'yan Isra'ila-Argentina da aka yi garkuwa da su a wani samame da suka kai a Rafah.

    • Falasɗinawa na fargaba gabanin hare-haren Isra'ila a Rafah
    • Netanyahu ya yi fatali da buƙatar Amurka ta kafa ƙasar Falasɗinawa