Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Usman Minjibir and Abdullahi Bello Diginza

  1. An katse hanyoyin sadarwa yayin zaɓe a Pakistan

    ...

    Pakistan ta katse hanyoyin sadarwa da suka hada da kiraye-kirayen waya da na intanet yayin da miliyoyin mutane ke fita rumfunan zaɓe don ka da kuri'a a sabuwar gwamnati.

    Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gida ya ce matakin sun dace, yana mai nuni da abubuwan da suka faru na ta'addanci a kasar.

    Zaɓen na zuwa ne kusan shekaru biyu tun bayan da aka hambarar da firaminista Imran Khan dan wasan kurket wanda ya zama dan siyasa a zaben da aka kada.

    Yanzu haka dai, Nawaz Sharif, wanda ya yi firaministan ƙasar har sau uku ya sake tsayawa takara.

    An daure Khan ne bisa zargin cin hanci da rashawa a bara kuma an hana shi tsayawa takara.

    Da yawa daga cikin masu kada kuri'a a birnin Lahore sun shaida wa BBC cewa katsewar intanet na nufin ba za su iya neman tasi ta intanet don zuwa wajen zaɓen ba, yayin da wasu kuma suka ce ba za su iya tattaunawa da sauran 'yan uwa ba domin hada kai a lokacin da za su je rumfunan zaɓe.

    • Yadda siyasa ke raba kan iyali a Pakistan gabanin zaɓen firaminista
    • Me ya sa Iran ta kai hare-hare kan ƙawayenta?
  2. Yadda 'yan Najeriya su ka yi murnar buge Afirka ta Kudu

  3. MDD ta gayyaci shugabannin sojin Sudan kan shigar da agaji

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dinkin Duniya ta gayyaci shugabannin bangarorin sojan kasar Sudan da ke rikici da juna a wani taro a birnin Geneva, domin tattaunawa kan ayyukan agaji a cikin halin da ake ciki a kasar kamar yadda shafin intanet na Sudan, Tribune da ke birnin Paris ya ruwaito a jiya.

    "A cikin makonni biyu da suka gabata, na tuntuɓi kwamandojin sojoji biyu, kwamandan sojojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, da kwamandan dakarun RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, 'don cika alkawarinsu' game da kai kayan aikin agaji,” in ji Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai Martin Griffiths.

    Ya yi nuni da cewa, an gayyace su ne zuwa wani taro da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya tsakanin wakilan bangarorin biyu da ke rikici da juna a Sudan domin tattauna batun isar da kayayyakin jin kai ga al'ummar Sudan.

    Kokarin da kungiyar kasashen yankin - Igad ta yi a baya na shirya taron Burhan da Dagalo bai yi nasara ba.

    • 'Gwamnatin kasarmu ta wofintar da mu a Sudan'
    • 'Mu na cikin mawuyacin hali a Sudan'
  4. Sojin Habasha sun ‘kakaba dokar hana fita’ a kudu maso yammacin Somaliya

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Sojojin Habasha da ke yankin Gedo a kudu maso yammacin Somaliya sun kakaba dokar hana fita bayan da yan bindiga suka kashe yan Ethiopia a baya-bayan nan.

    Shafin Ethio Forum ya ruwaito cewa "Dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin Gedo sun sa dokar hana fita kuma suna rangadi daga Balad zuwa Hawo zuwa Dolow [garuruwa a yankin Gedo], kamar yadda majiyoyi daga yankin suka bayyana,"

    Rahoton ya ce babu tabbaci ko rangadin na Habasha ya samu goyon bayan jami'an tsaron Somaliya ko dakarun wanzar da zaman lafiya daga wasu kasashen.

    Wani rahoto a ranar 5 ga watan Fabarairu ya nuna cewa wasu yan bindiga sun kashe farar hula yan Habasha bakwai a garin Balad Hawo. Lamarin ya faru daidai lokacin da dangantaka ta yi tsami tsakanin Habasha da Somaliya game da yarjejeniyar da Habasha ta kulla da yankin Somaliland a farkon shekarar nan.

    • Yaƙin Tigray: Ana zargin sojojin Eritrea da yi wa mata fyaɗe duk da yarjejeniyar zaman lafiya
    • Anya tallafi na kaiwa ga 'yan Ethiopia kuwa?
  5. An fara taron ministocin harkokin wajen ƙasashen Ecowas

    ..

    Ministocin harkokin wajen kasashen mambobin kungiyar Ecowas sun fara taro a yau Alhamis a Abuja, karon farko bayan kasashen Nijar da Mali da Burkina sun sanar da ficewarsu daga kungiyar, yayin da a bangare guda kuma shugaban kasar Senegal, Macky Sall ya dage babban zaben kasar.

    Taron Ministocin zai iya zama sharar-fage ga taron da shugabannin kasashen kungiyar za su yi don tunkurar wadannan matsalolin.

    Taron, kamar yadda wata sanarwar da kungiyar Ecowas din ta wallafa a shafinta na intanet ta nuna, taro ne na musamman da ya kunshi `yan kwamitin shiga-tsakani da majalisar tsaro a matakin ministoci, wanda sanarwar ta ce za su yi zama da nufin tattaunawa a kan halin da yankin Afirka ta yamma ya samu kansa a ciki ta fuskar tsaro da wasu matsaloli da suka jibanci siyasa.

    Tun a ranar 28 ga Janairu ƙasashen Mali da Burkina Faso da Kuma Nijar suka sanar da aniyar ficewa ƙungiyar Ecowas.

    ..
    ..
    ..
    ..
  6. Za mu ci gaba da yaƙin neman zaɓe – Yan adawar Senegal

    ...

    Yan adawa a Senegal sun sha alwashin ci gaba da gudanar da yakin neman zabensu kwanaki uku bayan kuri’ar da aka kada a majalisar kasar da ta dage zaben kasar har zuwa nan da wata 10.

    Yan adawar na dunkulewa su hada kai duk da bambancin da ke tsakaninsu.

    Kusan sama da yan takara 11 cikin 20 a zaben Senegal sun yanke shawarar haduwa su tafi tare.

    Sun yi kira ga kungiyoyin kwadago da shugabannin addini da kungiyoyin fararen hula su fito su nuna adawa da matakin dage zaben kasar.

    Daya daga cikin yan adawar Yewwi Askan Wi, ya ce lauyansa zai shigar da kara a yau alhamis domin kalubalantar matakin, sannan yan adawar sun yi kira ga dukkanin al’ummar Dakar da sauran manyan biranen Senegal su fito domin gudanar da gagarumar zanga-zanga.

    Sun ce kudirin dokar da ya kai ga dage zaben ya saba wa kundin tsarin mulki, don haka ba za su lamunci tafiya cikin sabawa tsarin kasa ba.

    • Senegal na dab da shiga ruɗani bayan ɗage zaɓe
    • 'Yan Senegal ma na zaben shugaban kasa
  7. Mali da Burkina Faso sun buƙaci gaggauta ficewa daga Ecowas

    ..

    Asalin hoton, ECOWAS

    Kasashen Mali da Burkina Faso sun bukaci gaggauta ficewa daga kungiyar ta Ecowas, lamarin da ke kara dagula dangantaka tsakanin kasashen Sahel da kungiyar kasashen yammacin Afrika.

    Kasashen biyu da Nijar sun fice daga ƙungiyar a ranar 28 ga watan Janairu, saboda rashin goyon bayan ƙungiyar ga yaƙi da ta'addanci da tsoma bakin kasashen waje.

    Sai dai hukuncin zai dauki shekara guda kafin a amince da shi, wanda suka ki amincewa.

    Ma'aikatar harkokin wajen Mali ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, "Gwamnatin Jamhuriyar Mali ba ta da iyaka da karancin lokaci da aka ambata a cikin sashe na 91 na yarjejeniyar da aka yi wa kwaskwarima da hukumar Ecowas ta yi magana a kai."

    Burkina Faso ta fitar da irin wannan sanarwa a jiya kuma ta ce ba za ta sauya ra'ayinta ba kan matakin da ta dauka na ficewa daga Ecowas.

    Kasashen biyu sun soki takunkumin da kungiyar Ecowas ta kakaba mata a matsayin martani ga juyin mulkin da sojoji suka yi.

    Sanarwar ta ce "Ta hanyar kafa matakan dakile tattalin arziki da na kudi a kan mambobinta, Ecowas ta himmatu wajen kin amincewa da yarjejeniyar da aka yi mata."

    A watan Satumban shekarar da ta gabata ne dai sojojin kasashen uku suka kafa kawancen kasashen Sahel, sakamakon matsin lamba da suka yi na mayar da mulkin farar hula.

    • Me ya rage wa Nijar, Mali da Burkina Faso bayan ficewa daga Ecowas?
    • Ko taron Ecowas a Abuja zai samar da mafita ga Nijar?
  8. Buƙatun Hamas kan tsagaita wuta ƙofa ce ta ƙulla yarjejeniya – Blinken

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren harakokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce bukatun Hamas kan bukatar tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin fursunoni wata kofa ce da ke kara samar da damar yiyuwar cimma yarjejeniya.

    Sai dai kuma kalaman Mr Blinken sun ci karo da na Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu wanda ya ce bukatun Hamas na yaudara ne tare da alwashin murkushe kungiyar a Gaza.

    Yayin da yake bayyana bukatun Hamas a matsayin bayyanannu, Mista Blinken ya ce zai ci gaba da tattaunawa. Sannan ya ce ya matsa wa Isra'ila ta tabbatar da kare fararen hula a Gaza.

    Mista Blinken ya ce Amurka ta yi amanna cewa akwai tasiri a bukatun Hamas na kokarin cimma yarjejeniya.

    "Mun yi nazari sosai kan abin da ya fito daga Hamas kuma komai a bayyane yake daga abin da ta gabatar, kuma muna ganin akwai damar ci gaba da tattaunawa daga abin da ya dawo domin burin cimma matsaya. kuma abin da muke nufin yi. Zan tattauna da Isra'ila da duk wadanda suka kamata.

    Sai dai kalaman na Mr Blinken sun ci karo da na Isra'ila inda Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya yi watsi da bukatun tare da shan alwashin murkushe Hamas.

    Tal Heinrich, ita ce mai magana da yawun Mr Netanyahu, ta shaida wa BBC cewa Isra'ila na kan manufofinta.

    Ta ce "ba za mu fice da dakarunmu gaba daya ba a Gaza daga bangaren yarjejeniyar sakin fursunoni. Za mu cimma muradunmu na wannan yakin kamar yadda muka tsara, wato kubutar da wadanda aka kama da kuma tabbatar da kawar da duk wata barazana daga Gaza ga Isra'ila da kawar da Hamas.

    Sakataren harakokin wajen Amurka dai ya kai ziyara gabar yamma da kogin Jordan inda ya gana da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas inda ya jaddada goyon bayan Amurka na tabbatar da kasar Falasdinu.

    • Dole a bar Falasɗinawa su zauna a Gaza - Blinken
    • 'Yaƙin Gaza zai iya ɗaukar ƙarin watanni ana gwabzawa'
  9. Shugaba Ramaphosa zai yi jawabi ga ƴan Afrika ta Kudu gabanin zaɓe

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa zai gabatar da jawabinsa na karshe ga al'ummar kasar kafin zaɓe mai zuwa.

    Ana sa ran Ramaphosa zai yi wa al'ummar kasar bayani kan yanayin tattalin arziki da siyasa da kuma muhimman batutuwan cikin gida da suka faru tun bayan jawabinsa na karshe.

    Kawo yanzu dai babu tabbas ko shugaban zai yi tsokaci kan ƙarar da gwamnatinsa ta shigar kan harin da sojojin Isra'ila suka kai a Gaza.

    Kuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuni da cewa jam'iyyar ANC mai mulkin ƙasar za ta rasa rinjayen 'yan majalisar dokoki a babban zabe mai zuwa.

    Wani bincike na baya-bayan nan ya gano cewa farin jinin ANC ya ragu zuwa kaso 38 cikin 100 a shekarar 2024 idan aka kwatanta da kaso 57.6 cikin 100 a shekarar 2019, kamar yadda Business Live mai zaman kansa ya ruwaito a shafinsa na intanet.

    Kafofin yaɗa labaran cikin gida sun yi hasashen cewa shari'ar kotun ƙasashen duniys (ICJ) da ake yi wa Isra'ila za ta zama tushen yaƙin neman zaben ANC.

    'Yan adawa sun yi ikirarin cewa ANC na amfani da shari'ar ICJ da kuma labarin "canjin mulki" don neman kuri'un jin kai daga 'yan Afirka ta Kudu.

    Ana sa ran shugaban kasar zai bayyana ranar da za a gudanar da babban zaben kasar nan da kwanaki 15 masu zuwa.

    • Shugaban ƙasa 'mai gaskiya' da ke fuskantar zargin cin hanci
    • Wace nasara shugabannin Afirka suka cimma a ziyarar sasanta Ukraine da Rasha?
  10. An Kashe sojoji uku da ƴan sa-kai biyu a wani hari a Nasarawa

    ...

    Asalin hoton, other

    An kashe sojoji uku da ƴan sa kai biyu a wani hari da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai a ƙaramar hukumar Toto ta jihar Nasarawa.

    Kwamishinan ayyuka na musamman na tsaro da ke jihar, Timothy Kasuwa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa mutane biyar sun rasa rayukansu a lamarin.

    "Gaskiya ne sun kashe sojoji uku da 'yan sa kai biyu," in ji kwamishinan.“

    "Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi musu kwanton bauna a lokacin da sojojin suka je aikin share fage yayin da suke dawowa"

    "Lamarin dai ya lafa, sojoji sun kara ƙarfafa jami'ansu da ke kewayen yankin."

    Da yake bayyana cewa an tura ƙarin jami’an tsaro yankin domin dakile tabarbarewar doka da oda, kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta dauki nauyin lamarin tare da yin ƙoƙarin shawo kan lamarin.

    • 'Rashin haɗin kan gwamnatoci dama ce ga 'yan bindiga'
    • ‘Yan bindiga sun hana mu girbe amfanin gona‘
  11. Dumamar yanayi a duniya ya zarce digiri 1.5 a 2024 - Masana

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Masana kimiyyar yanayi a Turai sun bayar da wasu kwararan hujjoji da ke tabbatar da cewa har yanzu ba a cimma muhimman manufofin da kasashen duniya suka amince ba na rage dumamar yanayi.

    Masanan na Turai sun ce a karon farko ma’aunin yanayin zafi ya zarta digiri 1.5 cikin shekara daya wanda aka kayyade kasa da shekara 10 da suka gabata a babban taron sauyin yanayi na Paris inda masana suka yi gargadin cewa idan har dumamar yanayi ya zarta wannan ma’aunin to za a iya fuskantar mummunan sakamako a duniya.

    Masanan a hukumar da ke kula da yanayi ta tarayyar Turai sun ce watanni takwas da suka gabata sun kasance mafi zafi da aka taba gani a tarihi, kuma zafin teku ya ci gaba da karuwa.

    Farfesa Liz Bentley ita ce shugabar cibiyar nazarin yanayi ta Royal Meteorological Society.

    "Ta ce ba sabon abu ne karya wadannan tarihin cikin kankanin lokaci, amma kuma zartawa a shekara yana da muhimmanci. Ma’unin da aka amince a yarjejeniyar Paris na dogon zango ne ina tunanin shekara 20." in ji ta.

    Wannan ne dai karon farko da dumamar yanayin ta zarta 1.5 na ma’aunin yarjejeniyar Paris a tsawon shekara, a cewar masanan na tarayyar turai.

    A 2015 ne shugabannin duniya suka amince su rage dumamar yanayin, wanda ake ganin zai taimaka wajen dakile fuskantar balo’i a duniya, kuma masana na ganin daukar matakan gaggawa na rage fditar da gurbatacciyar iskar masana’atu zai taimaka wajen rage dumamar yanayi.

    • Sauyin yanayi: Me ya sa matsalolinsa ke ƙara ta'azzara a duniya?
    • Lokaci yana kure wa al'ummar duniya kan dumamar yanayi
  12. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Alhamis.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu don samun abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida da Nabeela Mukhtar Uba ne ke tare da ku a wannan safiya!