Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Usman Minjibir and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. 'Yan sandan Brazil sun fara bincike kan yunƙurin juyin mulki a 2022

    Rundunar 'yansandan Brazil ta fara wani gagarumin bincike a kan muƙarraban tsohon shugaban ƙasar, Jair Bolsonaro, kan rawar da ake zargin sun taka a yunkurin juyin mulki a ƙarshen shekara ta 2022.

    'Yansandan sun ce tsohon shugaban ya jagoranci wani yunkuri da bai yi nasara ba, na neman ci gaba da zama a kan mulki, bayan kayen da ya sha a zaɓe a hannun jagoran masu ra'ayin kawo sauyi, Luiz Inacio Lula da Silva.

    Kafofin watsa labarai na Brazil sun ce yunƙurin juyin mulkin da ake zargi bai yi nasara ba ne saboda shugabannin sojoji sun ƙi bayar da goyon baya.

    An kama uku daga cikin tsofaffin jami'an tsohon shugaban ƙasar da kuma shugaban jam'iyyarsa.

    A hira da kafofin yaɗa labarai na Brazil, Mista Bolsonaro ya koka da cewa sama da shekara ɗaya da barinsa mulki, har yanzu hukumomi na yi masa bi-ta-da-kulli.

  3. Za mu ci gaba da tattaunawa da Nijar domin samun maslaha - Ecowas

    Ƙungiyar raya tattalin arzikin Ƙasashen Afirka na Yamma Ecowas ta ce ba za ta gaji ba, za ta ci gaba da amfani da hanyar diflomasiyya wajen ganin ta janyo hankalin ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso na ganin ba su aiwatar fa aniyarsu ba ta ficewa daga cikinta.

    Ecowas ta cimma hakan ne a karshen tattaunawar da ministocin harkokin wajen mambobinta suka gudanar a yau a Abuja, domin shawo kan matsalolin da ake fuskanta a yankin.

    Ecowas ta faɗa cikin ruɗani tun bayan da ƙasashen Nijar da Burkina da Mali suka sanar da aniyarsu ta ficewa daga ƙungiyar.

    Ana tsaka da haka sai ga wani rikici na neman ɓulluwo a Senegal da ke ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar.

    Cikin dokokin Ecowas na fita daga ƙungiyar, sai mambanta ya sanar da ita shekara guda gabanin ficewar, wani abu da ƙasashen suka sa kafa suka yi fatali da shi.

    Sanadiyyar hakan ne ƙungiyar ta ce ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso ba su bi hanyoyin da suka dace na fita daga ƙungiyar ba.

  4. 'Nan ba da jimawa ba farashin kayan abinci zai sauka'

    Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas ya ce majalisar na sane da halin matsalar tsaro da tsadar rayuwa da 'yan ƙasar ke fuskanta.

    Honarabul Tajudeen Abbas ya ce a ɓangarensu na majalisa ba za su zuba wa ɓangaren zartaswa ido ba har sai an samu mafita.

    Kakakin majalisar ya tabbatar wa da BBC cewa za a shawo kan ƙalubalen da ake fuskanta nan ba daɗewa ba.

    ''Majalisa za ta yi duk abin da ya kamata domin ganin an samu sauƙi a matsalar tsaro da tsadar rayuwa da ke fuskanta a ƙasar nan''.

    Kakakin majalisar ya ce majalisa ta za kirawo duka masu ruwa da tsaki a harkar tsaro domin magance matsalar tsaron da ake ciki.

    Honarabul Tajedeen Abbas ya ce 'yan majalisar na sane da irin halin matsin rayuwa da talakawan ƙasar ke ciki, kuma suna duk mai yiwuwa domin magance matsalar.

    Don haka ne ma ya ce 'yan majalisar suka mayar da hankali wajen sayen kayan abinci domin rabar wa talakwan da suka zaɓe su.

    Ya kuma ce gwamnati na yin duk mai yiwuwa don magance matsalar, kuma ya tababtar da cewa nan ba da jimawa ba farashin kayan abincin zai sauka a ƙasar.

  5. Gwamnatin Najeriya na duba yiwuwar shigo da abinci daga waje don magance yunwa

    Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi 'yan kasuwar da ke da ɗabi'ar ɓoye kayan abinci a daidai lokacin da talakawan ƙasar ke cikin matsin rayuwa.

    Ministan yaɗa labaran ƙasar Muhammad Idris ne ya bayyana haka jim-kaɗan bayan taron gaggawa kan halin matsin rayuwa da tsadar abinci da 'yan ƙasar ke ciki.

    Ministan ya ce gwamnati a nata ɓangare za ta fito da metri ton 42,000 na abinci daga rumbunan ma'aikatar harkokin noma.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke cikin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fuskanta a cikin makonnin baya-bayan nan.

    ''Ma'aikatar harkokin noma na da masara da gero da nau'in gari a rumbunan ajiyarta da ke sassan ƙasar daban-daban domin raba wa 'yan ƙasar nan ba da jimawa ba'', in ji ministan.

    Ya ƙara da cewa gwamnati ta ji labarin cewa masu kamfanonin sarrafa shinkafa faɗin ƙasar na da tarin shinkafar da suka taskance, don haka gwamnati ta yi magan da su sun kuma amnce za su fito da metric ton 60,000, don a sayar wa 'yan ƙasar.

    Ministan ya ce idan ta kama ma ƙasar za ta ya shigo da abinci daga ƙasashen wajen do magance matsalar tsadar abincin a faɗin ƙasar.

    ''Nan gaba kaɗan za a yi haka idan ta kama a yi'', in ji Muhammad Idris.

    Ministan ya kuma gargaɗi masu ɓoye kayan abinci da su buɗe shagunansu domin mutane su samu damar saya.

    ''Ba abu ba ne na alkairi ana cikin wannan matsatsi, kai kuma ka je ka ɓoye abinci don wata manufa taka da daban, don haka gwamnati ke kira ga irin waɗanan 'yan kasuwa da su fito da waɗanan kayayyaki domin sauƙaƙa wa 'yan ƙasa'', in ji ministan.

    Yana me cewa duk ɗan kasuwar da ya ki bin wanan umarni to gwamnati ta san su ta kuma san matakin da za ta ɗauka a kansu.

  6. Kotu a Kano ta buƙaci a yi wa Hafsat Chuchu gwajin ƙwaƙwalwa

    Wata babbar kotu da ke zaman ta a birnin Kano ta buƙaci a yi wa Hafsat Surajo (Chuchu) gwajin taɓin hankali a ci gaba da shari’ar da ake yi mata kan zargin kisan wani matashi mai suna Nafi'u Hafiz.

    Kotu ta ɗauki wannan mataki ne bayan da Hafsat ta ƙi cewa uffan a lokacin da aka karanta mata tuhumar da ake yi mata.

    Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Zuwaira Yusuf ta buƙaci a samu likitan ƙwaƙwalwa da zai duba lafiyar Hafsat a inda ake tsare da ita.

    Tun farko an karanta wa Hafsat laifukan da ake tuhumar ta da su, sai dai ba ta ce komai ba a lokacin da kotu ta tambaye ta ko ta fahimci abin da ake nufi ko a’a, balle ma ta amsa ko tana da hannu a cikin abin da ake zargin nata da shi ko a'a.

    Yanzu haka kotun za ta jira sakamakon gwajin da likita zai yi wa Hafsat kafin ci gaba da sauraron shari’ar.

    A cewar kotu, dole ne a tantance lafiyar duk wanda ake tuhuma kafin ci gaba da shari’a, kasancewar "ba a yin shari'a da mai taɓin hankali."

    Wannan ne karo na farko da ake karanto wa Hafsat tuhume-tuhumen da ake yi mata a gaban babbar kotun.

    An gabatar da ita ne a kotun tare da mijinta da kuma wasu mutum biyu da ake zargi da hannu wajen aikata laifin.

    Haka nan a lokacin zaman na yau Alhamis, lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun gabatar wa kotu buƙatar bayar da belin mjin na Hafsat da sauran mutum biyun, sai dai kotun ta ce za ta sanya ranar sauraron buƙatar tasu.

    A watan Disamban shekarar da ta gabata ne rundunar ƴansanda a jihar Kano ta bayyana cewa jami’anta sun kama Hafsat Surajo ƴar shekara 24 da ke Unguwa Uku bisa zargin kashe Nafi'u Hafiz, ɗan shekara 38 a gidanta na aure.

    Haka zalika binciken ƴansandan ya kai ga kama mijin matashiyar, Dayyabu Abdullahi mai shekara 38, sai kuma Mallam Adamu mai shekara 65 da kuma ƙarin wani mutum ɗaya.

    Tun a wancan lokaci ne kotu ta bayar da umarnin ajiye Hafsat a gidan kaso.

    Bayan kammala zaman kotun na yau an mayar da Hafsat da sauran waɗanda ake tuhuma zuwa gidan gyaran hali domin ci gaba da tsare su.

  7. Zelensky ya kori babban kwamandan sojin Ukraine

    Shugaban ƙasar Ukraine Vladimir Zelensky ya kori babban kwamandan sojojin ƙasar, Valerii Zaluzhnyi.

    MIsta Zelensky ya kuma sanar da maye gurbinsa da Kanar - Janar Syrskyi a matsayin sabon shugaban rundunar sojin.

    Hakan na zuwa ne bayan an yaɗa raɗe-raɗin samun saɓani tsakanin shugaba Zelensky sa Janar Zaluzhnyi, wanda ya jagoranci dakarun da ke yaƙi da mamayar Rasha tun farkon fara yaƙin.

    Matakin ya kasance wani babban sauyi a jagorancin rundunar soji Ukraine, tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine cikin watan Fabrairun 2022.

    Mista Zelensky ya ce akwai buƙatar sauya fasalin shugabancin rundunar, sai dai ya ce Janar Zaluzhnyi zai ci gaba da kasancewa cikin rundunar.

    "Daga yanzu, sabon jagorancin rundunar sojin zai fara aiki,'' in ji mista Zelensky.

    Shugaba Zelensky ya ce shi da Janar Zaluzhnyi sun tattauna kan sauye-sauyen da rundunar ke buƙata, sanna ya gode wa Janar Zaluzhnyi kan aikin kare ƙasar da ya yi daga mamayar Rasha.

  8. NNPCL ya musanta shirin ƙara kuɗin man fetur

    Kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya musanta duk wani yunƙuri na ƙarin farashin man fetur a faɗin ƙasar.

    A baya-bayan nan masu ababen hawa na fuskantar dogayen layuka a wasu gidajen mai a wasu yankunan ƙasar, musamman a kudancin ƙasar, sakamakon fargabar da ake yi cewa hukumomi za su ƙara farashin man.

    To sai dai a cikin wata sanarwa da kamfanin mai na ƙasar, NNPCL ya fitar mai ɗauke da sa hanun jami'in hulɗa da jama'a na kamfanin, Olufemi Soneye ya fitar, ya buƙaci 'yan ƙasar su kwantar da hankalinsu.

    ''Ba za a ƙara kuɗin man fetur ba'', kamar yadda sanarwar kamfanin ta tabbatar.

    “NNPC Ltd na buƙatar 'yan Najeriya su yi watsi da duk wata jita-jita da ta dangancin ƙarin kuɗin mai, kuma kamfanin na son tabbatar wa 'yan ƙasa cewa babu wani yunƙuri da hukumomi ke yi game da ƙarin kuɗin man'', in ji sanarwar.

    Tun bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi cikin watan Mayun shekarar da ta gabata, farashin man fetur ya yi tashin gwaron zaɓi, inda ya tsahi daga naira 193 zuwa sama da naira 600.

    Wani abu da mashahanta ke kallon a matsayin babban abin da ya haddasa tashin farashin kayayyaki a ƙasar.

    Lamari da ya jefa tattalin arzikin ƙasar cikin matsi, da tsadar rayuwa.

  9. Majalisar wakilan Najeriya za ta ƙarfafa dokar ɓata-suna

    Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas ya ce majalisar za ta ƙarfafa dokar ɓata-suna da cin cin mutuncin mutane da kuma cin zarafin mutane ta intanet.

    Honarabul Tajedeen ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai kan abubuwan da ke damun ƙasar da aka gudanar a wani ɗakin taro a harabar majalisar.

    Kakakin majalisar ya ce manufar dokar ba zai ci karo da 'yancin faɗar albarkacin baki, amma za ta kare mutane da hukumomi daga cin zarafinsu a intanet.

    Ya ƙara da cewa dole ne 'yan Najeriya su damu bisa yadda ake yawan cin zarafin jami'an gwamnati a shafukan intanet.

    Honarabul Abbas ya bayyana yadda kakakin majalisar da ya gabace shi, Femi Gbajabiamila, ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fuskanci cin zarafi da intanet, da ɓata suna.

  10. 'Nijar da Mali da Burkina Faso ba su cika ƙa'idar fita daga Ecowas ba'

    Ƙungiyar Raya Tattalin Arzkin Ƙasahsne Afirka ta Yamma Ecowas, ta ce dole ne ƙasashe Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar sun cika sharuɗan ƙungiyar kafin ta ba su damar ficewa daga cikinta.

    Ƙungiyar ta ɗauki wanna mataki ne ranar Alhamis lokacin taron kwamitin sasanta wa na ƙungiyar da ka gudanar a Abuja babban birnin Najeriya.

    Ranar 28 ga watan Janairu ne dai ƙasashen uku suka bayyana ficewarsu daga ƙungiyar, sannan suka aike mata da takardar ficewar tasu kwana guda bayan haka.

    Yayin da yke jawabi a wajen taron shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar, OmarAlieu Touray ya ce matakin da ƙasashen uku suka ɗauka na ficewa daga ƙungiyar sun ɗauke sh ne cikin gaggawa don haka ƙungiyar ba za ta amince da shi ba.

    Ƙarƙashin dokar ƙungiyar, duk ƙasar da ke son ficewa daga cikinta dole ne ta bayar da sanarwa shekara guda kafin ranar ficewar. Ya ƙara da cewa ƙasashen uku ba su yi la'akari da irin yadda matakin zai shafi al'ummominsu ba.

    Duka ƙasashen uku dai na ƙarƙashin mulkin soji.

    Haka kuma ana sa ran ƙungiyar za ta ɗauki matki kan halin da siyasar Senegal ke ciki, inda shugaban ƙasar Macky Sall ya ɗage zaɓen shugaban ƙasar da aka yi shirin gudanar da shi cikin wannan wata.

  11. An hana mai ƙalubalantar Putin shiga zaɓen shugaban ƙasar Rasha

    Hukumar zaben Rasha ta hana dan siyasa ɗaya tilo - da ke adawa da yakin Ukraine, wanda ke ƙoƙarin ganin ya kara da Shugaban ƙasar Vladirmir Putin - tsayawa takara a zaben watan gobe da ke tafe.

    Boris Nadezhdin na yawan caccakar shugaba Putin kan mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine.

    Hukumar zaɓen ta zartar da cewa yawan sa-hannun jama'a da Mista Nadezhdin, ya miƙa mata ba su kai yadda ya kamata ya tsaya takara a zaɓen na wata mai zuwa ba.

    Don haka ne hukumar ta ce ta yi fatali da yunkurin nasa.

    To sai dai ɗan siyasar ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa zai ƙalubalanci matakin a kotun kolin ƙasar.

    "Na samu yawan jama'ar da suka sanya hannu kan goyon byan takarata kusan 200,000 a faɗin Rasha, don haka za mu ƙalubalnaci wanan mataki," kamar yadda ya wallafa a shafin naku.

    Hukumar zaɓen ta ce fiye da sanya hannun mutum 9,000 da mista Nadezhdin ya miƙa mata ba su wadatar ba.

    Akwai giɓin aƙalla mutum 95,000, hakan na nufin ya gaza samun mutum 100,000 da yake buƙata kafin hukumar ta yi masa rajista a matsayin ɗan takara, in Andrei Shutov wani jami'i a hukumar zaɓen.

    Za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da ranakun 15 zuwa 17 ga watan Maris, duk da cewa ba za a samu tababa a zaɓen ba, saboda iya 'yan takarar da gwamnatin ƙasar ta amince da su ne za su tsaya.

    A ranar Asabar ne za a fitar da matakn ƙarshe kan wadanda za su tsaya takarar.

    Kusan shekara 25 Mista Putin ke jagorantar Rasha a matsayin Firaminista da kuma Shugaba.

  12. Yadda ƙwallo ke haɗa kan ƴan Najeriya, su manta da damuwarsu

  13. An ceto mutum 20 daga hannun masu garkuwa da mutane a Katsina

    Rundunar sojan kasa ta Najeriya ta ce dakarunta sun ceto wasu mata kusan 20 daga masu garkuwa da mutane a jihar Katsina tare da mika su hannun hukumomin jihar.

    Sojojin sun ce sun samu nasarar kubutar da mutanen ne yayin wasu hare-haren da suka kai kan maboyar ‘yan bindigar a dazukan ‘yan-tumaki da Dan-Ali.

    Hakan dai na zuwa ne bayan sace wasu mata 53 da ke kan hanyarsu ta zuwa kai amarya a yankin karamar hukumar Sabuwa.

    A lokacin da ya yi wa BBC ƙarin bayani, kwamishinan harkokin tsaro na jihar Katsina, Nasir Mu'azu ya ce babu tabbas kan lokacin da aka sace mutanen da aka ceton.

    Sai dai ya bayyana cewa mutanen da aka ceton ƴan asalin ƙaramar hukumar Musawa ne da ke jihar.

    Ko a makon da ya gabata, wasu ƴan bindiga sun sace ƴan rakiyar amarya sama da 50 a ƙaramar hukumar Sabuwa, waɗanda masu garkuwa da mutanen suka yi barazanar sayar da su da kuma sake aurar da amaryar.

    • Bidiyon ƴanbindigar da suka sace amarya farfaganda ce – Gwamnatin Katsina
    • Shin me ya sa Abuja ke fuskantar matsalar tsaro?
  14. An rufe rumfunan zaɓe bayan katse intanet a Pakistan

    An rufe rumfunan zabe a babban zaben Pakistan da ake yi yau Alhamis, zaben da ya gamu da tashin hankali nan da can.

    Jam'iyyun hamayya sun yi Alla-wadarai da hukumomin kasar kan katse hanyoyin sadarwa na wayar salula da intanet.

    Wakiliyar BBC ta ce, jam'iyyun siyasa a nan suna ta nuna bacin ransu da cewa harwayau, wannan wata alama ce ta danniya ga yin zabe cikin walwala da adalci.''

    Jam'iyyar PTI, ta tsohon Firaminista Imran Khan da aka daure, ta kira abin da cewa wata makarkashiya ce kawai ta tauye wa 'yan kasa hakkinsu.

    Su kuwa hukumomin kasar cewa suka yi tabarbarewar halin tsaro ne ya sa suka yi hakan.

    'Yansanda biyar sun mutu a lokacin da wasu 'yan-bindiga suka tayar da bam, sannan suka bude wuta, a lardin Dera Ismail Khan.

    An kuma kashe soja daya a lokacin da aka kai hari kan tawagar sojin a garin Kot Azam.

  15. Jihar Oyo za ta gurfanar da mutum uku kan fashewar abubuwa a Ibadan

    Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a ranar Laraba, ya karbi rahoto a hukumance kan fashewar wani abu da ya faru a unguwar Bodija da ke Ibadan a ranar 16 ga watan Janairu, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata mutane 77 da kuma lalata gidaje 58.

    Mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin tsaro, kuma kwamishinan ‘yan sanda mai ritaya Fatai Owoseni,, ya bayyana wa manema labarai cewa rahoton ya alaƙanta mutane uku da fashewar.

    Ya kuma ce za a gurfanar da mutanen uku a gaban kuliya.

    Rahoton, an gano cewa, ya kunshi binciken da kwamitin kungiyoyin likitoci da jami'an tsaro da kuma injiniyoyi wadanda gwamnati ta kafa suka yi.

    Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan gabatar da rahoton, Owoseni ya ce, “An gano wasu mutane uku da ke da ruwa da tsaki a kan musabbabin faruwar lamarin, kuma za a gurfanar da su gaban kotu bisa binciken da aka gudanar.”

    Ya bayyana cewa wani gidan talabijin da aka rufe a daya daga cikin gidajen da abin ya shafa ya dauki hoton yadda lamarin ya faru, yana mai jaddada cewa gwamnatin jihar za ta gurfanar da waɗanda suka aikata laifin.

  16. Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano za ta fara binciken masu ɓoye kayan abinci

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano ta gargadi ‘yan kasuwar da ake zargi da boye kayan abinci da su daina.

    Hukumar ta ce bayan korafe-korafen da ta karba daga mutane daban-daban ta umarci jami’anta su fara bincike wuraren da ake zargin an makare manyan sito-sito da kayan abinci.

    Shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce sun gano cewar boye kayan na daga cikin abubuwan da suke kara tsadar kayan masarufi a Kano, inda ya ce duk mutumin da suka kama to zai dandana kudarsa.

    Ana dai ta zarge-zarge cewa manyan 'yan kasuwa na boye kayan masarufi har sai ya yi tsada su fito da shi su sayar, wani abu da ake ganin yana taimakawa wajen kara dagula lamarin tsadar kayan na masarufi a Najeriya.

    'Yan kasuwa dai a Kano da ma Najeriya na musanta zarge-zargen da ake yi musu, inda ko a makon da ya gabata sai da gamayyar kungiyar 'yan kasuwa a birnin Kano ta yi barazanar rufe kasuwanci saboda tsadar abubuwa.

    Ko a makon da ya gabata sai da daruruwan al'ummar birnin Minna na jihar Naija suka yi zanga-zangar nuna damuwa kan yanayin tsananin rayuwa da ake ciki.

    Saurari tattaunawar da wakilin BBC Zahradden Lawan yi da shugaban na Hukumar yaƙi da rashawa da sauraron ƙorafe-ƙorafen al'umma na jihar Kano, Mahuyi Magaji a ƙasa.

  17. Matashi mai yi wa kasa hidima ya rasu lokacin wasan Super Eagles da Bafana

    Dan bautar kasar da aka bayyana da Samuel daga jihar Kaduna ya rasun ne kafin bugun karshe na fanaretin da Najeriya ta samu nasara.

    Shugaban ofishin NYSC na jihar Adamawa, Jingi Dennis ya ce an tabbatar da rasuwar dan bautar kasar ne bayan an kai shi babban asibitin garin na Numan.

  18. Mutumin da Amurka ke nema ruwa a jallo ya tsere daga hannun ƴan sandan Kenya

    Wani mutum da ya tsere daga Amurka bayan zargin kashe budurwarsa ya kuma tsere daga hannun ‘yan sanda a Kenya a sirrance.

    An kama Kelvin Kangethe mai shekara 41 a makon da ya gabata a lokacin da yake barin wani kulob a Nairobi babban birnin kasar Kenya, bayan da hukumomin Kenya da Amurka suka kwashe tsawon watanni suna farautarsa.

    Kotu ta amince ‘yan sanda su tsare shi na tsawon kwanaki 30 yayin da yake jira a mika shi.

    Hukumomi sun ce bayan da Kangethe ya kashe budurwarsa a watan Oktoban da ya gabata, ya watsar da gawarta a cikin mota a filin jirgin sama na Boston Logan. Sannan ya hau jirgi zuwa Kenya, kasarsa ta asali.

    Ya dai yi tsokaci kan zargin.

    ‘Yan sandan sun firgita ‘yan kasar Kenya inda suka bayyana cewa Kangethe ya yi nasarar ficewa daga ofishin ‘yan sandan Nairobi inda ake tsare da shi a yammacin Larabar da ta gabata, kuma ya shiga motar jigilar jama’a.

    Kwamandan ‘yan sandan Nairobi Adamson Bungei ya shaida wa kafar yaɗa labaran ƙasar cewa an kama jami’an ‘yan sanda hudu da ke bakin aiki lokacin da Kangethe ya tsere da kuma lauyan da suka gana da shi kafin ya tsere.

    • Yadda maza ke kashe kansu a Kenya
    • Waiwaye: Ɗalibi ya kashe kansa saboda budurwa, wani ya yanke al’aurarsa a Kano
  19. Sauye-sauye uku da zan samar a hukumar fina-finan Najeriya - Ali Nuhu

  20. Tsohon Daraktan NDDC ya rasu yana kallon wasan Najeriya da Afirka ta Kudu

    Tsohon Babban Darakta na Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Cairo Ojougboh, ya rasu a lokacin da yake kallon wasan Najeriya da Afirka ta Kudu a jiya Laraba.

    Rahotanni dai sun bayyana cewa, ya rasu ne a lokacin da aka da aka bai wa Najeriya bugun fenareti a wasan.

    An ce ya yi kururuwa kuma ya fadi sakamakon bugun zuciya lokacin da dan Bafana Bafana ya zubar da ƙwallo.

    Shugaban Bola Tinubu ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan tsohon Babban Daraktan a sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar.

    Sanarwar ta ce Tinubu ya yi addu’ar Allah ya jikan wanda ya rasu.

    Shugaban ya kuma jajanta wa ’yan uwansa sannan ya kuma bukace su da su "kara samun karfi da fata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ke tafiyar da al’amuran mutane".

    Ojougboh ya kasance ɗan majalisar wakilai a shekarar 2003 zuwa 2007 kuma shugaban jam'iyyar APC a jihar Delta.

    Najeriya ta doke Afirka ta Kudu da bugun fanariti a wasan kusa da na karshe a filin wasa na Stade de la Paix da ke Bouake, da yammacin Laraba.

    • Wa zai kai wasan ƙarshe tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu?
    • Yadda za ku iya buga game ɗin BBC Hausa kan Gasar AFCON