An katse hanyoyin sadarwa yayin zaɓe a Pakistan
Pakistan ta katse hanyoyin sadarwa da suka hada da kiraye-kirayen waya da na intanet yayin da miliyoyin mutane ke fita rumfunan zaɓe don ka da kuri'a a sabuwar gwamnati.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gida ya ce matakin sun dace, yana mai nuni da abubuwan da suka faru na ta'addanci a kasar.
Zaɓen na zuwa ne kusan shekaru biyu tun bayan da aka hambarar da firaminista Imran Khan dan wasan kurket wanda ya zama dan siyasa a zaben da aka kada.
Yanzu haka dai, Nawaz Sharif, wanda ya yi firaministan ƙasar har sau uku ya sake tsayawa takara.
An daure Khan ne bisa zargin cin hanci da rashawa a bara kuma an hana shi tsayawa takara.
Da yawa daga cikin masu kada kuri'a a birnin Lahore sun shaida wa BBC cewa katsewar intanet na nufin ba za su iya neman tasi ta intanet don zuwa wajen zaɓen ba, yayin da wasu kuma suka ce ba za su iya tattaunawa da sauran 'yan uwa ba domin hada kai a lokacin da za su je rumfunan zaɓe.
- Yadda siyasa ke raba kan iyali a Pakistan gabanin zaɓen firaminista
- Me ya sa Iran ta kai hare-hare kan ƙawayenta?