Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba a kanmu aka fara sayen motocin alfarma ba — ‘Yan Majalisar Wakilan Najeriya
Majalisar Wakilan Najeriya ta mayar da martani a kan ce-ce-ku-cen da ake yi a ƙasar game da batun saya wa mambobinta su 360 sabbin motocin alfarma.
Majalisar ta ce za a sayi motocin ne don aikin ofis, kuma kuɗin da ake cewa za a sayo motocin bai kai yadda ake zuzutawa ba.
Honorabul Kabiru Alasan Rurum, ɗan majalisar mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano da Bunkure da kuma Kibiya a jihar Kano, ya shaida wa BBC cewa, ba kansu farau ba.
Ya ce,” Tun da mu ne karkatacciyar bishiya mai daɗin hawa kusan duk abubuwan a kanmu yake, ya kamata idan za a yi abu a yi shi gaba ki ɗaya, ma’ana a kasafin kuɗin bana nawa aka ware na saya wa ofishin shugaban ƙasa motoci, da mataimakinsa da kuma ministoci haka a dukkan mataki har a zo kanmu.”
Ɗan Majalisar Wakilan ya ce,” Idan har aka yi la’akari da ba mu kaɗai za a sayawa motocin ba, to shi ne aka yi mana adalci, amma saboda mu ne aka zaɓa shi ne aka yi laifi.”
Honorabul Kabiru, ya ce su kansu sun damu da yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa, kuma kowa a cikinsu na iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya taimaka a wannan gaɓar don a samu sauƙi.
Wannan taƙaddama dai na zuwa ne bayan shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu, ya amince wa majalisar wakilan ƙasar kashe naira biliyan 70 daga cikin ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗin 2022, batun da ya janyo ƙorafe-ƙorafe daga wajen ‘yan ƙasar saboda matsin tattalin arziƙin da ake ciki.
Ƙungiyoyin kare fararen hula a Najeriyar na daga cikin ƙungiyoyin da suka fara ƙorafin inda suka ce matakin majalisar na sayo waɗannan motoci ga ‘yan majalisar ƙasar a daidai lokacin da talakawa ke fama da matsin rayuwa ba komai ba ne illa rashin damuwa da halin da ake ciki.
Ƙungiyoyin sun ce kamata ya yi majalisar dokokin ƙasar ta ba wa ‘yan majalisar kuɗin da aka ce sun kai naira miliyan biyu kan kowacce mota guda su koma mazaɓunsu don taimaka wa waɗanda suka zabe su.
Ƙungiyoyin farar hular sun ce a halin da ake ciki a yanzu mutane na kwana ba tare da sun ci abinci ba, wasu kuma sau ɗaya ko sau biyu suke samu su ci, inda mutane ƙalilan ke samu su ci abinci sau uku a rana, amma a haka ‘yan majalisar za su je su hau motar miliyoyin kuɗi.
Ƙungiyoyin suka ce kamata ya yi ‘yan majalisar su rinƙa ɗibar kuɗi daga aljihunsu suna taimaka wa jama’a ba wai su rinƙa hawa motoci na alfarma, waɗanda kuɗin man da za a sanya a motocin ma da zamansu.