Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida and Usman Minjibir

  1. Jam'iyyun adawa ne ke tunzura jama'a su yi zanga-zanga - APC

    ..

    Asalin hoton, \State house

    Jam'iyya mai mulki a Najeriya ta APC ta zargi jam'iyyun adawar kasar da ingiza matasa su hau kan tituna da sunan zanga-zanga kan abin da ta bayyana da "nuna gwamnatin shugaba Tinubu da wannan ta gaza a tafiyar da mulki a kasar".

    A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam'iyyar ta APC, Felix Morka ya fitar, jam'iyyar ta ce jerin zanga-zangar da aka yi a birnin Kano da Minna duka sun nuna irin zakuwar bangaren adawa na tunzura jama'a su yi wa gwamnati bore.

    "Faruwar zanga-zangar a lokaci guda ba hakan nan ba. Alamu ne da ke nuni da kishirwar tayar da zaune tsaye domin yi wa gwamnati zagon kasa wanda kuma hakan ke barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa.", in ji sanarwar.

    Mr Felix ya kara da cewa a daidai lokacin da gwamnati ta amince 'yan kasa su nuna damuwarsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya to amma su yi hakan ta hanyar da ta dace da kuma doka ta tanada "sannan ka da su mika akalarsu ga 'yan adawa da ke so yin amfani da su domin tayar da tarzoma".

    Daga karshe sanarwar ta bai wa 'yan Najeriya tabbacin cewa gwamnati shugaba Bola Tinubu na sane da halin da 'yan kasa ke ciki kuma tana yin duk abin da za ta yi wajen tabbatar dda ta share musu hawaye.

    • Sa'insar Atiku da Tinubu, rufe kasuwannin canji a Abuja da Kano
    • Dalilanmu na soma zawarcin jagororin kwankwasiyya - Ganduje
    • Idan an ce PDP azaba ce yanzu daɗi ake sha? - Sule Lamido
  2. Likitoci a Kano suna tiyatar sauya kashin kafada a karon farko a Najeriya

    ...

    Likitoci a asibitin kashi na birnin Kano na gudanar da tiyata irinta ta farko ta sauya kashin kafada ga wata mata.

    Hotuna daga asibitin dai sun nuna yadda tawagar likitocin suke gudanar da shirye-shiryen yin wannan aiki.

    Kafin yau din dai ba a taba gudanar da irin wannan aiki ba a Najeriya, inda wasu ke kallon hakan ka iya rage yawan ficewa daga kasar zuwa kasashen waje domin neman lafiya.

    • Likitoci sun yi nasarar dasa wa mutum zuciyar alade
    • Sarkakiya uku da ke tattare da yi wa mutum dashen zuciyar alade
    • An yi dashen azzakari na farko a Amurka
  3. Za a ga yanayin hazo da kura na kwana uku a Najeriya – Nimet

    ..

    Asalin hoton, OTHERS

    Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi hasashen samun hazo da kura daga ranar Talata zuwa Alhamis a sassan kasar.

    A bayanin hasashen da hukumar ta fitar ranar Litinin a Abuja, an yi hasashen samun kura da hazo mai tsanani da ka iya shafar tashi da saukar jiragen sama.

    A cewar Nimet, ana sa ran ganin hazo da kura mai tsananin a jihohin arewa da arewa ta tsakiya.

    Hukumar ta kara da cewa a ranar Alhamis za a fuskanci raguwar yanayin na hazo da kura a jihohin yankunan biyu.

    Nimet ta ce a jihohin kudancin Najeriya kuma, za a ga sauyin yanayi a ranar Alhamis inda da safe za a ga disashewar yanayi daga bisani kuma ya yi sauki.

    Hukumar ta kuma ba da shawara a kula wurin sa wa yara kanana da tsofaffi kayan sanyi.

    Ta kuma ce ya kamata jirage su duba yanayi da hasashen hukumar Nimet domin tsara yadda zirga-zirgarsu za ta kasance a tsukin ranakun.

    • Hazo ya hana jirage tashi a Nigeria
    • Hazo da kankara sun mamaye Burtaniya
    • Burtaniya za ta karfafa fannin hasashen yanayi
  4. 'Ana jan kafar sake gina Turkiyya shekara guda bayan mummunar girgizar kasa'

    Kungiyoyin agaji da ke aiki a Turkiyya sun ce, shekara guda bayan mummunar girgizar kasa ta afkawa kasar wadda ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da dubu hamsin da uku a kudu maso gabashin kasar, har yanzu ba a kammala aikin sake gine- ginen da suka ruguje ba.

    Kungiyar Save the Children ta ce kashi daya bisa uku na wadanda suka rasa muhallansu kawo yanzu ba su da matsuguni.

    Wakiliyar BBC ta ce iyalai da dama suna zaune ne a cikin tantuna da kwantena wanda ya kamata a ce mataki ne na wucin gadi.

    Girgizar kasar ta lalata kashi 85 cikin dari na ababen more rayuwa da suka hada da makaruntu da asibitoci a yankunan da ta yi kamari, kamar lardin Hatay.

  5. 'Yan Najeriya su guji murnar wuce iyaka idan Eagles suka doke Bafana Bafana'

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ofishin jakadancin Najeriya ya shawarci yan kasar da ke zaune a Afirka ta Kudu gabanin wasan da kasashen biyu za su fafata a gasar kwallon Afirka a Ivory Coast.

    Sanarwar da ofishin ya fitar ranar Talata ta gargadi yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudun su guji tsokanar takwarorinsu idan Super Eagles ta yi nasara a wasan.

    Sanarwar ta nemi "yan Najeriya su kula da kalamansu, su kuma yi taka tsan-tsan game da inda za su kalli wasan musamman a wuraren taron jama'a".

    Ta kara da kira ga yan Najeriyar su guji yin murnar wuce gona da iri da ka iya jawo tashin hankali idan har Najeriya ta doke Afirka ta Kudu.

    Ofishin jakadancin ya yi gargadi kan mayar da martani ko ta wace fuska a maimakon haka, ofishin ya bukaci mutanen da abin ya shafa su kai korafi kan duk wani yanayi na tashin hankali ga hukumomin da suka dace.

    A ranar Juma'ar da ta wuce, kwallon da Ademola Lookman ya zura a ragar Angola ce ta bai wa Super Eagles shiga zagayen kusa da na karshe a gasar ta Afcon.

    • AFCON 2023: Najeriya ta tsallaka zuwa wasa na kusa da na karshe
    • Abubuwan ban mamaki da suke faruwa a Afcon a Ivory Coast
    • Victor Osimhen: Daga ɗan talla kan titi a Lagos zuwa 'sabon sarki a Afirka'
  6. Shugabannin duniya na yi wa Sarki Charles fatan samun sauki

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Shugabannin kasashen duniya sun aike da sakonnin nuna goyon baya ga Sarki Charles tare da yi masa fatan samun sauki cikin gaggawa bayan da aka sanar cewa ya kamu da cutar kansa.

    Sai dai ba a bayyana takamaiman nau'in cutar kansar da Sarkin ke fama da ita ba.

    An dai gano cutar kansar ne a lokacin da za a yi wa sarkin tiyata a wani asibiti a makon da ya gabata.

    Fadar Buckingham ta ce Sarkin zai ci gaba da aikinsa amma ba zai halarci tarurruka ba yayin da ake jinyarsa.

    Sai dai Wakiliyar BBC ta ce Sarki ba zai so haka ba saboda zai so a ce ya halarci taron shugabbanin kasashe renon Ingila da za a yi nan gaba.

    A yanzu matarsa Camila da dansa yarima William da sauran yan gidan saurautar Birtaniya ne za su yi haka.

    • Lokutan da sarki Charles III na Birtaniya ya yi jinya
    • Waɗanne irin ƙalubale ne a gaban Sarki Charles III?
    • Ba za a sa hoton Sarki Charles III a jikin dalar Australia ba
  7. Blinken na ci gaba da rangadi a Gabas ta Tsakiya don neman tsagaita wuta a Gaza

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Nan ba da jimawa ba ne Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai isa birnin Alkahira na kasar Masar a wani bangare na yunkurinsa na baya bayan nan na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

    Daga nan zai wuce zuwa Tel Aviv bayan Isra'ila ta sha alwashin ci gaba da kai farmaki ta kasa inda za ta maida hankali a kan garin Rafah da ke kudanci da ke fama da cunkuson 'yan gudun hijira.

    A jiya Litinin ne, Ministan tsaron Isra'ila, Yoav Gallant, ya ce mayakan Hamas da suka boye a can za su gamu da ajalinsu.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan gudun hijira na ci gaba da kwarara zuwa Rafah daga wasu yankuna.

    Ta ce a yanzu haka fiye da rabin al'ummar Gaza na samun mafaka a cikin garin.

    • Birtaniya na duba yiwuwar amincewa da kasar Falasdinawa - Cameron
    • Netanyahu ya yi fatali da buƙatar Amurka ta kafa ƙasar Falasɗinawa
    • An faɗa wa kotu jami'an gwamnatin Isra'ila na goyon bayan a ruguza Gaza
  8. Assalamu Alaikum!

    Jama'a barkan mu da safiya. Da fatan mun wayi gari lafiya a wannan rana ta Talata.

    Nabeela Mukhtar Uba tare da abokan aiki - Usman Minjibir da Aisha Babangida ke muku marhabun a wannan shafi na Kai Tsaye na BBC Hausa.

    Shafin zai kawo muku labarai da rahotanni a kai a kai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran kasashen duniya.

    Sai ku kasance tare da mu tun daga yanzu zuwa lokacin da za a rufe wannan shafi. Akwai shafukanmu na sada zumunta da za ku iya lekawa domin kallon bidiyo da karanta karin labarai.