Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida and Usman Minjibir

  1. 'Yan Houthi sun gudanar da zanga-zangar adawa da harin Amurka a Sana'a

    A karshen makon da ya gabata ne 'yan Houthi na Yemen suka gudanar da zanga-zanga a wajen Sana'a, babban birnin ƙasar domin nuna adawa da sabbin hare-haren da Amurka ke kai musu, tare da nuna goyon baya ga Falasdinawa.

    'Yan Houthi sun shahara a irin gagarumar zanga-zanga a ƙasar, wadda galibin dubban daruruwan mutane ke fitowa.

    Edmund Fitton-Brown, wanda ya kasance jakadan Birtaniya a Yemen daga shekarar 2015- 2017, ya shaida wa BBC kwanan nan cewa 'yan Houthis na fitar da gungun mutane a kan titi ta hanyar tsoro.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mayaƙan Houthi sun daga tutocin Yemen da Falasdinawa a wani mataki na nuna rashin amincewa da Amurka da Isra'ila
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Sojoji da magoya baya sun yi fareti a gaban jama'a, suna taka tutocin Amurka da Birtaniya
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Tawagar 'yan yara samari dauke da allunan shugaban Houthi
  2. Adadin waɗanda suka mutu a fashewar iskar gas a Kenya ya kai shida

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi sun ce adadin waɗanda suka mutu sakamakon fashewar iskar gas a Nairobi, babban birnin Kenya a ranar Alhamis ya ƙaru zuwa shida.

    Wasu ƙarin mutum biyu sun mutu a ranar Lahadin da ta gabata yayin da suke karɓar magani a babban asibitin ƙasa na Kenyatta.

    Ana kuma jinyar wasu 52 a cibiyoyin lafiya daban-daban.

    Wata babbar mota makare da iskar gas ta fashe da tsakar dare a wani yanki mai yawan jama'a na birnin, lamarin da ya haddasa babbar gobara.

    Hukumomin ƙasar dai sun bayyana kamfanin da ke bayar da iskar gas din a matsayin mai tafiyar da harkokinsa ba bisa doka ba kuma sun ce a baya an rushe wurin har sau biyu.

    'Yan sandan Kenya sun ce suna neman wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu a harin, ciki har da mai kamfanin iskar gas Derrick Kimathi.

    A ranar Asabar din da ta gabata ne shugaban ƙasar William Ruto ya zargi jami’an gwamnati da gazawa da cin hanci da rashawa da kuma barin kamfanin ya yi aiki a wani yanki.

    • Tukunyar gas ta sake fashewa a Kano, ta jikkata kusan mutum 70
    • 'Sinadaran hada bam ne suka haddasa fashewa a Kano'
  3. Yadda Tyla ta lashe kyautar Grammy bayan doke zaratan mawakan Najeriya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Mawakiyar Afirka ta Kudu Tyla ta lashe kyautar Grammy ta wakar da ta fi shahara a duniya da wakarta mai taken 'Water'.

    Tyla ta doke fitattun mawakan Najeriya irin su Burna Boy da Davido da Ayra Starr da Asake.

    Nasarar Tyla ta faranta ran 'yan Afirka ta Kudu duk da dai ta janyo takaddama a tsakanin 'yan Najeriya.

    Bayan sanar da Tyla a matsayin wadda ta lashe wannan kyauta, wasu 'yan Najeriya sun garzaya shafukan sada zumunta domin bayyana mamakinsu kan yadda matashiyar mawakiyar Tyla wadda 'sabon -shiga' ce a fagen rera wakoki ta yi zarra kan zaratan mawakan Najeriya da aka dade ana jin wakokinsu.

    Magoya bayan mawakiya Tyla sun ce ta cancanci nasarar da ta samu inda suka ba da misali da yadda wakar tata ta 'Water' ta samu karbuwa a duniya.

    A bara ne, wakar 'Water' ta karade ko ina a fadin duniya inda ta kafa tarihi a shafukan sauraron wakoki tare da yin fice a jerin wakoki 100 da suka shahara.

    "Wannan abu ne na ba-zato! Ban taba tunanin zan lashe Grammy a shekara 22 ba!" in ji Tyla a lokacin da ta karbi kyautar a Amurka ranar Lahadi da daddare inda take sanye da kayatacciyar doguwar riga ta kamfanin Versace.

    Wasu 'yan Afirka a shafukan sada zumunta sun yaba da gasar ta Grammy a matsayin wani muhimmin lokaci na tarihi ga nahiyar, inda Tyla ta yi nasara sai Burna Boy da ya gwangwaje da wakarsa sai kuma mai wasan barkwancin nan dan Afirka ta Kudu Trevor Noah da ya gabatar da taron wakokin mafi girma karo hudu a jere.

    • Yadda TikTok ya sauya kasuwancin waƙoƙi a ƙasar Hausa
    • Afrochella: Masu zuwa babban casun Ghana sun kaɗu jin cewa an daina shi
  4. Yadda Amurka ta kai hare-hare kan 'yan Houthi a bidiyo

    Rundunar sojin Amurka ta wallafa bidiyo da ke nuna yadda ta kai hari cikin dare wanda ta ce ta kai ne kan mayakan Houthi da ke samun goyon bayan Iran.

    Jiragen uku da aka nuna a bidiyon da ke kasa sun hada da babban jirgin yaki kirar USS Dwight D Eisenhower da kirar USS Gravely da kuma Carney.

    Bayanan bidiyo, Bidiyon yadda Amurka ta kai hare-hare kan mayakan Houthi
  5. An sako dalibai da malaman Ekiti da yan bindiga suka sace

    Yan bindiga a kudu maso yammacin Najeriya sun saki dalibai shida da malamansu uku da suka sace kusan mako daya da ya wuce.

    Hukumomi a jihar Ekiti sun ce yan bindigar sun kashe direban motar da daliban ke ciki a lokacin da masu garkuwar suka far musu.

    Mahukuntan ba su yi bayani kan ko a biya kudin fansa ba kafin sakin daliban.

    Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna daliban a galabaice cikin wani yanayi na kaduwa.

    Ana sa ran za a kai su asibiti domin a duba lafiyarsu.

    Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a arewacin Najeriya sai dai matsalar na kara bazuwa a sassan kasar.

    A makon da ya gabata ne, yan biniga suka harbe wani basaraken gargajiya a jihar Kwara tare da sace mutum biyu har da mai dakin sarkin.

  6. An gyara lantarki bayan lalacewar babban layin wuta a Najeriya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    An dawo da hasken wutar lantaki a akasarin biranen Najeriya da suka fada cikin duhu sakamakon lalacewar babban layin samar da wuta na kasa a ranar Lahadi.

    Lalacewar babban layin ya haifar da rashin hasken wutar lantarki a manyan biranen kasar har da Abuja, babban birnin Najeriya.

    Kamfanonin samar da wutar lantarki a sassan kasar sun aika sakon bai wa abokanan huldarsu hakuri game da rashin wutar.

    Cikin wata sanarwa, kamfanin rarraba lantarki na Najeriya ya sanar da gyaran babban layin wutar lantarkin bayan aikin da aka yi a kai.

    Wannan ne karon farko da babban layin lantarkin ya samu matsala a wannan shekarar. A bara, ya sha fuskantar matsaloli lokuta da dama.

    Najeriya da ke da yawan al'umma na fiye da mutum miliyan 200, har yanzu tana iya samar da wutar lantarki tsakanin megawatts 3500 da 4500.

    Duk da kasancewar ta kasa mai arzikin mai da iskar gas, har yanzu ba a samar da tsayayyiyar wutar lantarki.

  7. Amurka ta kai karin hare-hare kan mayakan Houthi

    ..

    Asalin hoton, Reuter

    Rundunar sojin Amurka ta ce ta kai karin hare-hare ta sama kan makamai masu linzami na mayakan Houthi a kasar Yemen jiya Lahadi - a wani mataki na baya-bayan nan da gwamnatin kasar ta dauka kan kungiyar da ke samun goyon bayan Iran.

    Rundunar ta ce dakarunta sun kai hare hare ta sama kan wasu makamai masu linzami da ake shirin harba wa, jiragen ruwa a tekun Ba har Maliya.

    Tun da farko dai mai ba da shawara kan harkokin tsaro a fadar White House ya ce hare hare ta sama da Amurka ke kai wa mayakan Houthi, ya karya lagwonsu wajan kai wa jiragen ruwan kasashen duniya hari.

    Gaba a yau ne Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken zai isa Gabas ta Tsakiya kuma a yau din ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai tattauna kan hare-haren da aka kai na baya-bayan nan.

  8. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Litinin.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye tare da Nabeela Uba Mukhtar da Aisha Babangida

    Ku biyo mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaɓtanta da sauran sassan duniya.