Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza
Masu garkuwa sun yi barazanar ɗaukan mataki kan daliban Ekiti da suka sace
Asalin hoton, Other
Shugaban makarantar Apostolic Faith Group inda aka sace dalibai biyar da malamai hudu a jihar Ekiti ya ce masu garkuwa sun yi barazanar ɗaukan mataki kan mutanen da suka sace idan aka gaza biyan kudin fansar da suka nema.
Gabriel Adesanya ya shaida wa BBC cewa akwai kimanin dalibai 20 da ke cikin motar lokacin da masu garkuwar suka kai musu hari.
Ya ƙara da cewa, "da yawa daga cikin iyayen yaran ba su da ko kashi daya cikin goma na kudin. Yanayi ne na ban tausayi ga makarantar da kuma al'ummar yankin. Har yanzu ba mu cigaba da karatu ba tun bayan kai harin".
Ɗaya daga cikin daliban da ke cikin motar lokacin da aka kai harin a ranar Litinin ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru bayan an tashi daga makaranta.
Ya ƙara da cewa masu garkuwar sun umarce su da su fito daga motar daga nan suka zaɓi waɗanda za su dauka suka tafi tare dasu.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci a yi gaggawar ceto mutanen inda ya ba da tabbacin hakan ba za ta ƙara faruwa ba.
A halin yanzu an buƙaci shugabannin tsaro da su gurfana a gaban majalisar dattawa ta kasa a mako mai zuwa domin tattaunawa game da karuwar rashin tsaro da ake fuskanta a kasar.
Yin garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa na kara tsananta a Najeriya cikin shekarun baya-bayan nan inda yan bindiga ke kai farmaki ga mutane masu tafiya a mota da ɗalibai har ma da mazauna ƙarkara da wasu wuraren a biranen da ke sassan ƙasar.
An kama shugaban ƴan adawan Indiya kan cin hanci da rashawa
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar yaƙi da laifukan da suka shafi kuɗi ta Indiya ta kama jagoran ƴan hamayyar ƙasar sa'oi bayan ya sauka daga muƙaminsa na babban ministan jihar Jharkhand.
An zargi Hemant Soren ɗan jam'iyyar Jharkhand Mukti Morcha - JMM da laifin rashawa yayin da shi kuma ya musanta zarge-zargen.
Sashen tabbatar da aiki da doka na hukumar ya kama shi a yammacin Laraba bayan shafe sa'a bakwai ana masa tambayoyi.
Jam'iyyarsa ta sanar da ministan sufuri Champai Soren a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
Mr Soren ya ƙalubalanci kama shi da aka yi a gaban babbar kotun ƙoli ta Indiya inda ya ce matakin kulli ne na siyasa. Kotun za ta saurari shari'ar a ranar Juma'a.
Shi ne na baya-baya cikin jerin jagororin ƴan hamayya da ke fuskantar bincike ƙarkashin hukumomin gwamnatin Indiya.
Yadda bashi ya yi wa jarumi Sunny Deol katutu
Indiya ta aika kumbonta na farko zuwa rana
Yadda ‘tarkon soyayya’ ke jefa mutane cikin ƙuncin rayuwa a Indiya
Yadda gobara ta ƙone wani coci ƙurmus a Legas
Wata gobara ta kone wata fitacciyar majami'a da ke Legas da aka fi sani da gidan David a lokacin da ma'aikata ke kokarin shirya wa wani taro.
Gobarar ta faru ne da safiyar jiya Laraba sa'oi kafin cocin ya soma wani taron shekara-shekara da yake samun halartar matasa da manya.
Wasu ma'aikata na aikin shirya dakin taron lokacin da suka gano wuta na tashi daga rufin ginin.
Wani shaida ya fada wa yan jarida cewa gobarar ta soma ne daga rufin ginin inda kuma ta gone wajen kurmus.
Shaidan ya ce a kan idonsu wutar ta kone kayan kide-kide da na'urarorin sanyi saboda ba za su iya yin komai ba saboda wutar da ke tashi gagga-gagga.
Sashen BBC Pidgin ya ruwaito yadda gobarar ta kone ginin baki daya inda yanzu ya zama toka.
Asalin hoton, Instagram/House of David
Dattawan Arewa da na Ibo sun yi alla-wadai da tafiye-tafiyen Tinubu
Asalin hoton, KASHIM SHETTIMA
Kungiyar dattawan arewacin Najeriya da takwararta ta Ohanaeze Ndigbo mai kare muradun al'ummar Igbo da wasu kungiyoyin farar hula sun bayyana rashin jin dadinsu game da tafiya zuwa Paris da shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi daidai lokacin da kasar ke fama da karuwar matsalar tsaro.
A ranar Laraba 24 ga watan Janairu ne shugaba Tinubu ya tafi zuwa Faransa domin wata ziyara ta kashin kai.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar gabanin tafiyar, ta ce Tinubu zai koma Najeriya cikin makon farko na watan Fabarairu.
Sai dai kungiyoyin a hirarsu da jaridar Daily Trust sun koka cewa babu gaskiya cikin sanarwar tafiyar la'akari da yadda aka kira tafiyar ta "kashin kai".
Matakin kungiyoyin na zuwa ne bayan da shi ma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya soki Tinubu inda ya bayyana shakku game da makasudin tafiyar tasa zuwa Faransa yayin da ake fuskantar karuwar matsalar yan bindiga da sauran matsalolin tsaro da ke ci gaba da ta'azzara.
Sai dai Fadar shugaban kasar ta ce duk da cewa Tinubu ba ya kasar, yana aiki tukuru domin kawo saukin matsalolin kuma yana bai wa hukumomin tsaro dukkanin goyon bayan da suke bukata domin samun nasara kan masu aikata miyagun laifuka da nufin fitar da Najeriya daga halin rashin tsaron da take ciki.
Tinubu dai ya sa kafa ya fice daga kasar yayin da ake tsokaci game da jerin hare-haren da aka kai a Filato da sace-sacen jama'a a Abuja, babban birnin kasar da kuma hari na baya-bayan nan na sace dalibai da malaman makaranta a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Kungiyar dattawan arewacin Najeriyar ta ce tafiyar ta Tinubu zuwa Paris a irin wannan yanayi da ake ciki a kasar manuniya ce cewa shugaban ya dukufa ne wajen cimma kudurorinsa na kashin kai a maimakon bai wa yan Najeriya kwarin gwiwa a lokacin da suke bukatar hakan.
Daraktan yada labarai na kungiyar, Abdulazeez Sulaiman ya ce kungiyar tana ganin matakin na shugaban kasar na tabbatar da damuwar da ake nunawa cewa Najeriya ta fada cikin matsalar rashin shugabanci na gari da rashin nuna damuwa da tausayi.
A nata bangaren, kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yi allah-wadai da tafiyar ta shugaba Tinubu zuwa Paris a halin tabarbarewar tsaro da sauran kalubale da ake ciki.
Babban sakataren kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro ya ce bulaguron da Tinubu ya yi na zuwa ne a lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen tattalin arziki.
Isiguzoro ya yi kira ga Tinubu da ya yi wa yan Najeriya bayani dalilin yin irin wadan nan tafiye-tafiye.
Shi ma shugaban kungiyar tabbatar da jagoranci na gari, GGT, Mista Tunde Salman ya ce da alama shugaba Tinubu ya bai wa wasu manyan jami'ai har da mataimakin shugaban kasa damar tafiyar da al'amuran.
Ya ba da misali da wani kwarya-kwaryan taro da aka shirya kan tsaro game da karuwar matsalar a arewacin Najeriya, inda mataimakin shugaban kasa da ministocin tsaro suka zama masu taka rawa sosai a taron.
Har yanzu zafin shan kaye ne ke damun Atiku - Tinubu
Me Tinubu zai yi da bashin kusan dala biliyan takwas da zai karbo?
Batun sayen motocin alfarma na Remi Tinubu na tayar da ƙura a Najeriya
EFCC na bincike kan yarjejeniyar Nigeria Air - Keyamo
Asalin hoton, Nigerian Govt
Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Festur Keyamo ya ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC na gudanar da bincike kan yarjejeniyar kamfanin jiragen sama na ƙasar wato 'Nagerian Air' mai cike da ce-ce-ku-ce da gwamnatin tarayya ta ƙulla ƙarƙashin tsohon ministan kula da sufurin jiragen sama na ƙasar Hadi Sirika
Yayin da yake zantawa da gidan talbijin na Channels ranar Laraba, mista Keyamo ya ce “EFCC na bincike kan yarjejeniyar.
''Ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma muna jiran rahoton binciken''.
Mista Keyamo wanda ya yi aiki tare da Sirika a matsayin ministocin gwamnatin Buhari, ya ce babu wani kamfanin jirage da ke aiki a matsayin kamfanin jirage na ƙasa, amma ya ce za a samar da nagartaccen kamfanin jirage na ƙasa.
A watan Agustan bara ne Mista Keyamo ya ƙaryata yarjejeniyar da Sirika ya ƙulla tare da dakatar da duk wani shiri da ke cikin yarjejeniyar.
Batun yarjejeniyar kamfanin 'Nigerian Air' dai ya ja hankalin 'yan ƙasar ne bayan da jirgin kamfanin ya yi ɓatan-dabo jim kaɗan bayan ƙaddamar da shi, kwanaki kafin ƙarewar wa'adin gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Muhamdu Buhari.
Ce-ce-ku-cen da ke tattare da yarjajeniyar kamfanin Nigerian Air ya tilasta wa shugaban kamfanin Ethiopian Airlines, Girma Wake ajiye muƙaminsa.
Manajan daraktan kamfanin Najerian Air, Capt Dapo Olumide, ya ce jirgin da aka gabatar a lokacin ƙaddamar da kamfanin, na Ethiopian Airlines ne.
Inda ya ƙara da cewa a ranar da wa'adin mulkin shugaba Buhari ya ƙare cikin watan Mayu, aka mayar wa Ethiopian Airlines jirgin bayan ƙaddamarwar.
Tuni dai dama majalisun dokokin ƙasar biyu suka bayyana ƙaddamar da kamfanin 'Nigerian Air' da aka yi a matsayin yaudara.
Houthi ta yi ikirarin kai wa jirgin ruwan Amurka hari a tekun maliya
Asalin hoton, GETTY IMAGES
Mayaƙan Houthi na Yemen sun yi iƙirarin kai hari kan wani jirgin ruwan Amurka a tekun Bahar Maliya, a wani sabon hari da suka kai kan jiragen jigilar kayayyaki.
Mayaƙan sun kira sunan jirgin da suka kai wa hari da KOI, wanda suka ce Amurka ke sarrafa shi.
Jami'an tsaron tekun sun ce wani jirgi da ke aiki a Kudancin tekun ya bayar da rahoton fashewar wani abu a yankin sai dai babu tabbacin ko jirgin da suke magana a kai ne.
A wani labarin, Amurka ta kai sabbin hare-hare kan jirage marasa matuƙa goma a Yammacin Yemen, wadanda ta ce mayaƙan na shirin kaddamar da hare-hare da su.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, KOI wani jirgin dakon kayayyaki ne da kamfanin Birtaniya Oceonix ke tafiyar da shi.
Kakakin mayakan Houthi, Yahya Sarea ya ce jirgin ya nufi tashar jirgin ruwan yankin Falasdinawa da aka mamaye.
Hatsarin mayar da martanin Houthi ga harin Amurka da Burtaniya a Yemen
Ta yaya hare-hare a tekun Maliya za su shafi kasuwancin duniya?
Su wane ne 'yan Houthi kuma me ya sa suke kai hari kan jiragen ruwa?
Barka da Hantsi!
Ma'su bibiyar wannan shafi na Kai Tsaye da BBC Hausa ke kawo muku a kodayaushe, barkan mu da warhaka. Da fatan mun wayi gari lafiya.
A yau Alhamis, shafin zai wallafa muku rahotanni da labarai na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.
Sai ku kasance tare da mu tun daga yanzu har zuwa lokacin da za mu rufe shafin (na Kai Tsaye).
Akwai shafukanmu na sada zumunta da za ku iya karanta karin labarai da kuma kallon bidiyo.