Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar Fintiri a matsayin gwamnan Adamawa
Kotun ƙoli ta tabbatar da zaɓen gwamna Ahmadu Fintiri a matsayin halastaccen gwamnan jihar Adamawa.
Mai shari’a John Okoro wanda ya karanta hukuncin a ranar Laraba ya yi watsi da ƙarar da ƴar takarar gwamna a jam’iyyar APC, Aisha Dahiru wadda aka fi sani da Binani ta shigar kan rashin cancanta.
A yayin da kotun ta yi watsi da ƙarar, kwamitin alƙalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a John Okoro ta bayyana cewa, abin da Kwamishinan Zabe (REC), Hudu Ari ya aikata, ta hanyar faɗin sakamakon zaɓe kafin kammala ƙirga ƙuri'a - wani abu ne na rashin gaskiya da kuma aikata laifi.
Okoro ya ci gaba da cewa, babban jami’in zaɓe na jihar ne ya kamata ya bayyana sakamakon zabe, domin a kauce wa hargitsi da rudani.
- Gwamna Fintiri ya ce ya ji takaicin abin da jami'in INEC ya yi a Adamawa
- Adamawa: Zaɓen da aka kammala ƙura ba ta kwanta ba