Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Nabeela Mukhtar Uba and Haruna Kakangi

  1. Rufewa

    To masu bibiyar wannan shafi na BBC Hausa da ke kawo muku labarai da rahotanni da suka shafi Najeriya da makwabtanta da sauran sassan duniya, kai tsaye a nan ne muke muku ban-kwana a yau Laraba.

    A madadin kowa da kowa ni Muhammad Annur Muhammad nake fatan za su sake kasancewa da mu a gobe Alhamis idan Alllah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya

  2. 'Yan sanda sun ceto mutum biyu da aka sace a Abuja

    'Yan sanda sun yi nasarar ceto wasu mutum biyu da masu satar mutane domin karbar kudin fansa suka yi garkuwa da su a cikin daren da ya gabata na Talata 31 ga watan Janairu, 2024 wajen karfe 1:00 na dare, a Abuja.

    Rundunar 'yan sandan birnin na tarayya ta ce, ta shiga farautar barayin ne bayan rahoton da ta samu na satar mutanen biyu, Sarah Hassan da Madam Erima Bobo-John a kauyen Kobi da ke yankin babban birnin tarayyar.

    Rundunar ta ce jami'anta da ke ofishin yanki na Asokoro ne suka shiga farautar barayin inda suka yi nasarar rutsa su a kan hanyar Nyanya zuwa Keffi inda sojoji suka tare barayin a wajen binciken ababen hawa.

    Sanarwar ta ce da ganin'yan sandan ne sai barayin suka bude wuta, inda 'yan sandan suka rinjaye su, ganin haka barayin suka gudu ta dajin da ke kusa da wurin, suka bar mutanen da suka sata.

    Tuni an mika mutanen biyu ga 'yan uwansu ba tare da sun ji wani rauni ba.

  3. Majalisar Wakilai ta umarci hukumar kashe gobara ta mayar da tallafin korona N1.48bn

    Majalisar wakilai ta Najeriya ta umarci hukumar kashe gobara ta tarayya da ta mayar da naira biliyan 1.48, ta tallafin Korona, cikin mako daya ga asusun gwamnatin tarayya.

    Kwamitin binciken kudaden gwamnati na majalisar shi ne ya bayar da umarnin kasancewar hukumar ta kwana-kwana ta ki bayyana a karo na uku a gaban kwamitin da ke bincike, domin bayar da cikakken bayani game da yadda ta sarrafa kudin.

    Mataimakin shugaban kwamitin Jeremiah Umar, shi ne ya gabatar da bukatar bayar da umarnin mayar da kudaden, domin a cewarsa hukumomi da yawa sun bayyana a gaban kwamitin, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike. ''Saboda haka ban ga dalilin da hukumar ta kwana-kwana za ta yi watsi da kwamiti kamar wannan ba.'' In ji shi.

    Wannan na zuwa ne a yayin da kwamitin ya sake mika sabbin takardun gayyata ga wasu ma'aikatu da hukumomi da sassan gwamnatin tarayya a kan su bayyana domin bayar da bahasin da ofishin babban aknatan kasar ya nema su yi kan yadda suka kashe kudaden da aka ba su na tallafin Korona a 2020.

  4. Mun gano wata ƙungiyar addini da ke samar wa 'yan ta'adda kuɗi – EFCC

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC ta ce ta gano hannun wata ƙungiyar addini da ke taimaka wa 'yan ta'adda wajen samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu na tayar da hankalin ƙasar.

    Shugaban hukumar Ola Olukoyede ya yi wannan bayanin yayin wata tattaunawa ta kwana ɗaya da aka shirya a Abuja a yau Laraba.

    Yayin jawabi a taron mai taken: "Matasa da Addini da kuma Yaƙi da cin hanci da rashawa", Olukoyede ya ce an samu wata ƙungiyar addini da laifin kare wasu kuɗaɗe da ake zargi na sata ne bayan da aka samu kuɗaɗen a asusun bankin ƙungiyar.

    "An samu wata ƙungiyar addini a ƙasar nan da ke boye wa ƴan ta'adda kuɗaɗe. Mun yi binciken da ya kai mu ga samun wasu kuɗaɗen sata a hannun wata ƙungiya ta addini."

    "Lokacin da muka tunkari ƙungiyar kan batun yayin aiwatar da bincikenmu, sai aka ba mu umarnin hana ci gaba da aiwatar da binciken namu," a cewar shugaban na EFCC.

  5. Majalisar Wakilan Najeriya ta sanya wa'adin kammala gyaran tsarin mulkin kasar

    Majalisar wakilan Najeriya ta karbi kudurin sake nazari da kuma gyara a kundin tsarin mulkin kasar har guda 40, kamar yadda mataimakin shugaban majalisar Benjamin Kalu, ya bayyana.

    Mista Kalu ya kuma majalisar na duba yuwuwar sanya wa'adin zuwa watan Disamba na 2025 domin kammala gyaran fuskar.

    Kalu, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin gyara kundin tsarin mulkin yana bayani ne ga manema labarai a yayin taron farko na kwamitin a Abuja.

    Dan majalisar ya ce suna dubawa ne su yi nazari domin ganin kwamitin ya kammala aikin a lokacin da ba zai ci karo da harkokin zabe ba, musamman ma watan Disamba na 2025.

    Ya ce tun 2010 majalisun dokokin kasa sun yi nasarar yin muhimman sauye-sauye a kundin tsarin mulkin bayan da gwamnatin mulkin soja ta Janar Abdulsalam Abubakar ta samar da shi.

    Sauye-sauyen da suka hada da na bangaren shari'a da harkokin zabe da rage shekaru da bayar da damar nada matasa a shugabancin hukumar zabe, INEC ko kuma kwamishinoninta na jiha, da kuma bayar da gama ga matasa su yi takarar wasu mukamai.

    Kwamitin mai mutum 37 ya kunshi wakilai daga jihohi 36 da kuma babban birnin tarayyar kasar Abuja.

  6. Yawancin 'yan Najeriya da ke neman mafaka a Belgium daga jihar Edo suke

    Kashi 30 cikin dari na 'yan ci-ranin Najeriya da ke neman mafaka a Belgium daga jihar Edo ta kudu maso kudancin Najeriya suke.

    Darekta Janar na hukumar shige da fice ta Belgium din, Mista Freddy Roosemont ne ya bayyana haka a wajen wani taro da hukumar tare da hadin gwiwar kungiyar Pathfinder Justice Initiative (PJI), ta shirya Benin, babban birnin jihar Edo capital, a yau Laraba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Mista Roosemont ya bayyana batun neman mafaka da 'yan Najeriya ke yi a Belgium da cewa abin damuwa ne.

    Ya ce kashi 30 cikin dari na masu neman mafakar daga jihar Edo suke, sai kashi 20 ciki dari daga jihar lagos yayin da sauran kashi 50 kuma suke daga wasu jihohin kasar.

    Jami'in ya ce yawan 'yan jihar Edo da ke da hannu a safarar mutane idan aka kwatanta da sauran 'yan jihohin Najeriya, shi ya tilasta musu shirya wayar da kan jama'a kan tafiya ci-rani waje ta hanyoyin da suka dace.

    Babban Daraktan ya ce a shekara ta 2022 kusan 'yan Najeriya 370 suka nemi mafakar sannan kuma a shekara ta 2023 kusn 360 ne suka nema.

    Roosemont ya shawarci 'yan Najeriya da su daina bari ana yaudararsu da sunan taimaka musu samun aiki a Belgium, domin guraben ayyukan a can su ma a cike suke.

    Ya ce a halin yanzu akwai 'yan Najeriya kusan 5,000 da ke zaune a ka'ida a Belgium.

    Darektan ya ce wasu daga cikin 'yannajeriyar sun je Belgium din ne ta hanyar ka'ida wasu kuwa sun bi ta haramtacciyar hanyar nan ne mai hadari ta tekun Bahar Rum.

  7. Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci Gwamnan Babban Banki kan karyewar darajar naira

    Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci Gwamnan Babban Bankin kasar da ya bayyana a gabanta domin yin bayani a kan mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki da kuma faduwar darajar naira a kasuwar kudaden waje.

    A yau Laraba ne majalisar ta hannun kwamitinta mai kula da harkokin bankuna da inshora da sauran cibiyoyin kudi ta gayyaci Mista Olayemi Cardoso daya bayyana a gabanta ranar Talata mai zuwa domin bayar da bahasi kan matsalolin da ke neman gurgunta tattalin arzikin kasar.

    Kwamitin karkashin shugabancin Sanata Adetokunbo Abiru ya gana ne bayan da a yau dala daya ta kai naira 1,520 a kasuwar kudaden waje ta bayan fage, inda suka mika gayyatar ga gwamnan na CBN domin ya je ya yi bayani kan mafita.

    Da yake magana da manema labarai bayan taron nasu na sirri, Sanata Abiru ya ce, halin da tattalin arzikin Najeriyar ke ciki musamman hauhawar farashin kayayyaki abu ne da ya damu 'yan majalisar.

  8. 'Yan canji a Abuja za su rufe kasuwar canji har sai abin da hali ya yi

    Kungiyar 'yan kasuwar canji ta Abuja ta ce daga ranar Alhamis za ta rufe kasuwar canji har sai abin da hali ya yi sakamakon tsadar dala da ke ake fama da ita a Najeriya.

    Shugaban kungiyar, Alhaji Abdullahi Dauran shi ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

    Darajar takardar kudin Najeriya - Naira ta yi faduwar da ba ta taba yi ba cikin gomman shekaru na tarihin kasar.

    A kasuwar canji, a ranar Talata, an yi musayar naira kan kowace dala a kan N1,520 yayin da a hukumance ake sayar da dala kan N892 da N910.

    Kungiyar 'yan canji ta alakanta tashin farashin dalar da ayyukan kamfanin da ke hada-hadar kudade ta Intanet irin na Crypto da ake kira Binance

    Hakan ne ya sa kungiyar yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta hana 'yan Najeriya hulda da kamfanin na Binance, idan dai har ana son karyewar farashin dalar.

  9. Ba mu amince da wasu mombobin kwamitin albashi ba - Shugaban NLC

    Shugaban kungiyar Kwadago na Najeriya, Joe Ajaero ya ce wasu gwamnonin da har yanzu ba su fara biyan albashi mafi karanci na naira 30,000 na daga cikin 'yan kwamitin da gwamnatin tarayya ta kaddamar domin sake yi duba kan sabon albashi mafi karanci.

    A ranar Talata ne dai mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya kaddamar da kwamitin mai mutum 37 domin yin duba ga tsarin albashi da kuma fito da sabon tsarin albashi mafi kankanta.

    To sai dai shugaban kungiyar ta Kwadago, Joe Ajaero da yake tattaunawa a gidan talbijin na Channels ya ce "wasu daga cikin 'yan kwamitin musamman ma gwamnoni har yanzu ba su cika alkawarin biyan albashi mafi kankanta ba. Saboda haka ina fatan sun shiga wannan sabon kwamitin da zuciya daya."

  10. 'Yan bindiga sun sake sace wasu 'yan mata 'yan gida daya a Abuja

    Wasu 'yan bindiga su shida sun far wa wani gida a kauyen Guita da ke Chikakore, a yankin Kubwa da ke Abuja inda suka yi awon gaba da 'yan mata guda biyu 'yan uwan juna masu shekaru 16 da 14.

    Bayan kwashe 'yan matan ne kuma 'yan bindigar suka ranta a na kare inda suka shiga daji wanda ya hada kauyen da wasu kauyukan masu makwabtaka.

    Wani shaida ya fada wa jaridar Daily Trust cewa " la ranar Lahadi lokacin da 'yan bindigar suka je sun kutsa gidan ne ba tare da harbi irin na kan-mai-uwa-da-wabi ba kamar yadda suka saba sannan suka kama 'yan matan guda biyu."

    Wannan ne dai karo na biyu a kasa da wata guda da 'yan bindiga ke yin garkuwa da 'yan mata 'yan uwan juna a babban birnin na tarayya.

    Batun tsaro na kara ta'azzara a birnin na Abuja wani abu da ke kara jefa fargaba a zukatan mazauna birnin.

    To sai dai a baya rundunar 'yan sandan birnin ta sha cewa tana iya bakin kokarinta wajen ganin su dakile matsalar.

  11. Shin giwaye sun iya iyo?

    Duk da girman jikinsu, giwaye na daga cikin dabbobi da suka ƙware a ɓangaren iyo. Suna amfani da dogon hancinsu wajen shaƙar iska sannan suna amfani da ƙafafunsu wajen tafiya cikin ruwa.

  12. An ƙaddamar da rundunar tsaron ƴan-sa-kai ta Zamfara

    Gwamnatin jihar Zamfara ta kaddamar da wata rundunar `yan sa-kai don yaki da `yan bindiga da saura miyagun laifuka a jihar, wadda aka yi wa lakabi da `Askarawan Zamfara`.

    Jihar Zamfara dai na cikin jihohin da matsalar `yan bindiga masu satar mutane don karbar kudin fansa ta yi kamari a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.

    Rundunar mai suna Askarawan Zamfara ta kunshi zarata 2,646, wadanda aka harhada daga kananan hukumomin jihar 14, wadanda suka samu horo na musamman daga jami`na tsaro da kwararru daban-daban a fannin tsaro don tunkarar matsalar `yan bindiga masu satar mutane da dabbobi a jihar Zamfara.

    Da yake kaddamar da rundunar yau a Gusau, babban birnin jihar, Gwamna Dauda Lawal ya ce gwamnatin jihar na amfani da hanyoyi da dabaru daban-daban wajen yaki da miyagun laifuka a jihar, ciki har da kafa rundunar Asakarawan da nufin inganta tsaro a jihar Zamfara, wadda ya ce da yaddar Allah kwalliya za ta biya kudin sabulu.

  13. Kotu ta bai wa mabiya addinin Hindu damar yin ibada cikin masallaci a Indiya

    Wata kotu a Indiya ta bai wa mabiya addinin Hindu izinin yin ibada a cikin wani masallaci da ke birnin Varanasi na arewacin ƙasar.

    Masu fafutuka na Hindu, waɗanda firaminista Narendra Modi ke mara wa baya, sun yi imanin cewa masallacin Gyanvapi da aka gina a ƙarni na 17 ya maye gurbin wani gidan ibada na farko ne da aka keɓe wa gunkin Shiva.

    Wannan shine misali na baya-bayan nan na kungiyoyin Hindu da suke neman karɓe wuraren ibada na musulmai da suka ce an gina su a kan tsoffin gidajen ibada.

    A makon da ya gabata, Narendra Modi ya jagoranci bikin kaddamar da wani wurin bautar mabiya addinin Hindu a kusa da Ayodhya inda ƴan Hindu suka rushe wani masallaci ba bisa ka'ida ba a shekarar 1992.

    Modi da jam'iyyarsa ta BJP mai kishin addinin Hindu, sun sha alwashin mayar wa mabiya Hindu irin waɗannan wurare.

  14. Yawan mutanen da yaƙi ya tarwatsa a Sudan ya kai miliyan takwas

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da yaƙin Sudan ya raba da muhallansu ya kai kusan miliyan takwas, wadanda rabinsu yara ne.

    A ziyarar da ya kai ƙasar Habasha makwabciyarta, babban jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Filippo Grandi ya yi kira da a samar da ƙarin tallafi cikin gaggawa.

    Grandi ya ce ya ji labarin yadda mutane suka gudu daga wani mummunan yaƙi kuma suna tsoron komawa gidajensu.

    Kazalika rikicin da ya ɓarke tsakanin sojojin Sudan da ƙungiyar mayaƙa ta RSF ya haifar da rikicin jin ƙai da kuma haddasa kashe-kashen kabilanci a yankin Darfur.

  15. Ana zargi sojojin Mali da na Wagner da laifin kisan mutum 25

    Rahotanni sun ce sojojin kasar Mali da sojojin haya na kungiyar Wagner ta kasar Rasha sun kashe mutum 25, musamman daga kabilar Fulani da ke tsakiyar ƙasashen yankin Sahel.

    Shafin gidan rediyon Faransa na RFI ya bayyana a jiya cewa lamarin ya faru ne a ranar 26 ga watan Janairu a ƙauyen Wellingara da ke kusa da kan iyaka da Mauritaniya, "inda sojojin Mali suke fuskantar hare-haren masu iƙirarin jihadi a makonnin da suka gabata".

    "Sojojin Mali da sojojin hayar Wagner na Rasha sun kai farmakin ne da safe, inda suka kama maza manya da yara sannan suka yi tafiyar tazarar kilomita biyu daga kauyen da su", rahoton ya ƙara da cewa an ƙona mafi yawa daga mutanen da suka kama.

    Majiyoyin cikin gida sun zargi sojojin da nuna kabilanci da kuma daukar fansa maimakon kare al'umma.

    Bayanin ya ƙara da cewa sojojin na fuskantar zargin kashe-kashe makamancin haka a yankin Kidal na arewacin kasar.

    Har yanzu dai rundunar sojin Mali ba ta ce uffan ba a hukumance kan lamarin biyu.

  16. An yanke wa Imran Khan hukuncin ɗauri na biyu cikin kwana biyu

    An yanke wa tsohon firaministan Pakistan, Imran Khan da matarsa ​​Bushra Bibi hukuncin ɗauri na shekara 14, hukunci na biyu da aka yanke wa tsohon Firaministan cikin kwana biyu.

    An samu ma'auratan da laifin cin gajiyar kyautukan gwamnati ba bisa ka'ida ba - mako guda kafin babban zaben da aka hana shi tsayawa takara.

    Khan, wanda abokan hamayyarsa suka hamɓarar da shi a matsayin firaminista a shekarar 2022, ya riga ya yi zaman gidan yari na shekaru uku bayan samun shi da laifin cin hanci da rashawa.

    Ya ce yawancin ƙararrakin da ake yi masa bita da kullin siyasa ne.

    Shari’ar ta ranar Laraba ta shafi tuhume-tuhumen da ake yi masa ne a kan wasu kyaututtukan gwamnati da aka yi masa da matarsa ​​a lokacin da suke kan karagar mulki, yayin da kuma shari’ar ta ranar Talata - wadda aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 10 a kan zargin fallasa wasu bayanan sirri na ƙasar.

    Ana tunanin hukunce-hukuncen biyu za su gudana a lokaci guda, kodayake ba a tabbatar da hakan ba.

    Kotun ta kuma umarci ma'auratan da su biya tarar kuɗi rupe biliyan 1.5, dalar Amurka 5.3m ke nan.

    Lauyoyin Khan sun ce za su daukaka kara zuwa babbar kotun Pakistan kan shari'o'in biyu.

    • Wane ne Imran Khan kuma me ake zargin tsohon firaministan na Pakistan da aikatawa?
    • Imran Khan: Firaminsitan Pakistan na fafutukar tsira da martabar siyasarsa
  17. Shugaban DR Congo ya buƙaci a sanya wa shugabannin Rwanda takunkumi

    Shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Felix Tshisekedi ya yi watsi da duk wata tattaunawa da kungiyar mayaƙa ta M23 da ya sha bayyana ta a matsayin ta ‘yan ta’adda.

    Da yake magana da jami'an diflomasiyyar ƙasashen waje a Kinshasa, Tshisekedi ya buƙaci ƙasashen duniya su kakaba wa Rwanda takunkumi saboda zargin ɗaukar nauyin kungiyar, kamar yadda shafin intanet na Acttualite ya bayyana.

    “Ina kira ga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Afirka da su sanya takunkumin karya tattalin arziki kan shugabannin Rwanda da na kungiyar ‘mayaƙa ta M23 da ke keta hurumin kasarmu."

    "Idan babu irin wannan takunkumin kamar yadda dokokin ƙasashen duniya suka tanada, Rwanda da kawayenta za su ci gaba da gurgunta zaman lafiyar kasa da kasa ba tare da fargabar komai ba."

    Ya ƙara da cewa "babu wata tattaunawa da za a yi da 'mai cin zali' (Rwanda) muddin ta mamaye kowane yanki na yankinmu".

    Ya kuma ce "yayin da yake ci gaba da jajircewa kan shirin zaman lafiya na Luanda da Nairobi, wanda ya tanadi cewa kungiyar M23 ta mika yankinta tare da kwace makamai, "ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an janye sojojin Ruwanda daga yankinmu".

    Tshisekedi ya yi marhabin da aikewa da dakarun yankin kudancin Afirka (SAMIDRC) zuwa lardin Nord Kivu da ke gabashin ƙasar, "wanda ya zo don tallafawa sojojin DR Congo a yaƙin da suke yi da RDF-M23"

    • Su wane ne 'yan tawayen DR Congo na M23, kuma me suke bukata?
    • DR Congo: 'Yadda gahawa ta sauya rayuwata baki ɗaya'
  18. Gobara ta lalata dukiya mai yawa a babbar kasuwar Gusau

    Wata gobara ta lalata shaguna da dama a babbar kasuwar Gusau da ke jihar Zamfara inda kuma ta kashe mutum daya.

    Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe tara, na daren ranar Litinin a bangaren kayan ɗaki na babbar kasuwar.

    Kwamandan hukumar kashe gobara ta Najeriya, Hamza Mohammed, ya sanar da gidan talabijin na Channels cewa wani mai shago wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba ya mutu a lokacin da yake kokarin shiga shagonsa domin kashe gobarar.

    Jami’an kashe gobara daga rundunar ‘yan sandan jihar sun yi ta fama da gobarar tun karfe tara na dare. domin hana yaduwar ta zuwa wasu shaguna.

    • Gobara ta ƙona kimanin shaguna 50 a kasuwar Singa
    • Gobara ta hallaka miji da mata da 'yarsu a Kano
  19. Dubban mutane sun tsere wa yunwa a yankin Tigray

    Sama da ‘yan gudun hijira 7,000 ne daga yankin Tigray da ke fama da yaki a kasar Habasha, suka tsere wa yunwa inda suka nemi mafaka a garin Endabaguna kamar yadda rahotanni suka nuna.

    Rahotannin sun kuma nuna cewa musgunawar da mayaƙan ƙabilar Fano daga yankin Amhara da ke makwabtaka da yankin Tigray ta hanyar koransu shi ma haddasa tserewar tasu.

    Rahoton da Addis Standard mai zaman kansa ya wallafa jiya a shafinsa na intanet ya kuma danganta rarrabuwar kawuna da "sabon zalunci da kuma kara matsin lamba kan 'yan kabilar Tigrai".

    An bayar da rahoton cewa an samu sabbin masu ƙaura da masu shigowa tun ranar 10 ga Disamba 2023.

    Hukumar kare hakkin bil-Adama ta ƙasar Habasha a jiya Talata ta yi kira da a dauki matakin gaggawa kan halin da ‘yan gudun hijira ke ciki tare da bayar da rahoton mutuwar mutane 21 sakamakon yunwa da kuma mata 23 da suka mutu a yankin Amhara da ke arewa maso yammacin kasar.

    ‘Yan gudun hijira sun gudanar da zanga-zangar neman komawa gidajensu sama da shekara guda bayan da aka kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ‘yan tawayen Tigray People’s Liberation Front (TPLF) domin kawo karshen yaƙin basasar da aka kwashe shekaru biyu ana yi a arewacin kasar.

    • Yankin Tigray: An kashe 'ƴan gudun hijira da dama - inji MDD
    • Abin da ya sa ba ma so mu koma gida — ‘Yan gudun hijira
  20. Ba za mu raina Angola ba - Yusuf

    Ɗan wasan Super Eagles na Najeriya, Alhassan Yusuf ya bayyana cewa za su mayar da hankali sosai a karawar da za su yi da Angola duk da kallon da ake yi wa Angola na wadda ba ta shahara ba a harkar ƙwallon ƙafa.

    Yusuf ya faɗi haka ne a tattaunawarsa da BBC yayin da tawagar Najeriyar ke yin atisaye a birnin Abidjan, gabanin karawarta da Angola a zagayen kwata-fainal.

    Najeriya dai ta yi nasara ne a kan Kamaru da ci 2-0 yayin da Angola ta doke Namibiya da ci 3-0 a karawar zagayen ƴan 16.

    A ranar Juma'a 2 ga watan Fabarairu ne Najeriya za ta kara da Angola a wasan na kwata-fainal a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka, 2023 da ke gudana a Ivory Coast.