Kashi 30 cikin dari na 'yan ci-ranin Najeriya da ke neman mafaka a Belgium daga jihar Edo ta kudu maso kudancin Najeriya suke.
Darekta Janar na hukumar shige da fice ta Belgium din, Mista Freddy Roosemont ne ya bayyana haka a wajen wani taro da hukumar tare da hadin gwiwar kungiyar Pathfinder Justice Initiative (PJI), ta shirya Benin, babban birnin jihar Edo capital, a yau Laraba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Mista Roosemont ya bayyana batun neman mafaka da 'yan Najeriya ke yi a Belgium da cewa abin damuwa ne.
Ya ce kashi 30 cikin dari na masu neman mafakar daga jihar Edo suke, sai kashi 20 ciki dari daga jihar lagos yayin da sauran kashi 50 kuma suke daga wasu jihohin kasar.
Jami'in ya ce yawan 'yan jihar Edo da ke da hannu a safarar mutane idan aka kwatanta da sauran 'yan jihohin Najeriya, shi ya tilasta musu shirya wayar da kan jama'a kan tafiya ci-rani waje ta hanyoyin da suka dace.
Babban Daraktan ya ce a shekara ta 2022 kusan 'yan Najeriya 370 suka nemi mafakar sannan kuma a shekara ta 2023 kusn 360 ne suka nema.
Roosemont ya shawarci 'yan Najeriya da su daina bari ana yaudararsu da sunan taimaka musu samun aiki a Belgium, domin guraben ayyukan a can su ma a cike suke.
Ya ce a halin yanzu akwai 'yan Najeriya kusan 5,000 da ke zaune a ka'ida a Belgium.
Darektan ya ce wasu daga cikin 'yannajeriyar sun je Belgium din ne ta hanyar ka'ida wasu kuwa sun bi ta haramtacciyar hanyar nan ne mai hadari ta tekun Bahar Rum.