Angola ta musanta alaƙa da jirgin ruwan da mayaƙan Houthi suka kai wa hari

Asalin hoton, Indian Navy
Kamfanin mai na Angola Sonangol ya yi watsi da rahotannin da ke cewa wani jirgin ruwa da mayakan Houthi suka kai wa hari a makon jiya a mashigin tekun Aden na cikin jiragensa.
Jirgin ruwan da ke da alaka da Birtaniya ya shafe sa'o'i da dama yana cin wuta a ranar Juma'ar da ta gabata a mashigin tekun Aden bayan da 'yan Houthi suka harba makami mai linzami.
Ƙungiyar da Iran ke marawa baya, wadda ke da hedkwata a Yemen, ta ce ta kai hari kan Marlin Luanda ne a matsayin martani ga "harin haɗin gwiwar da Amurka da Birtaniya suka kai".
Musantawar ta zo ne a matsayin martani ga rahotannin kafafen yada labarai na Angola da ke alakanta jirgin ruwan Marlin Luanda da Sonangol.
Kamfanin Sonangol ya sanar da jama'a cewa jirgin ruwan Marlin Luanda, wanda makami mai linzami ya harbo kwanan nan a cikin tekun Bahar Maliya, ba ya cikin tashoshin jiragen ruwa mallakar kamfani ko hayarsa," in ji kamfanin a cikin wata sanarwa da kafafen yada labarai na cikin gida suka gani.
Marlin Luanda, wanda ke aiki a madadin Trafigura mai siyar da kayayyaki ta Singapore, yana dauke da tutar tsibirin Marshall.
Trafigura na ɗaya daga cikin manyan masu samar da dizal da dizal na jirgen ruwa zuwa Angola.
Har ila yau, yana da hannun jari a kamfanin makamashi na Puma, wanda ke kula da gidajen mai na Pumangol a Angola.
Sauran masu hannun jari a Puma Energy sun hada da Sonangol.




