Dakarun RSF sun yi iƙirarin harbo jirgi mara matuki kirar Iran

Asalin hoton, AFP
Dakarun RSF sun ce sun harbo wani jirgi maras matuki kirar Iran da ake zargi na sojin Sudan ne yayin da yaki ke ci gaba da kazanta tsakanun bangarorin biyu a Khartoum, babban birnin kasar da wasu yankuna.
RSF a sakon da ta yi a shafinta na X ta ce "ta yi gagarumar nasara da safiyar nan, ta harbo wani jirgi mara mautki na sojojin Sudan".
"Jirgin da aka bayyana da Mohajer-6 kirar Iran, ya zama jirgi na uku da a baya-bayan nan aka dakile bisa kokarin jajirtattun sojojinmu. Duk da wannan nasara, za mu ci gaba da fuskantar kalubale," kamar yadda kungiyar ta ce.
Rundunar sojin ta Sudan ba ta kai ga cewa komai ba game da al'amarin.
Kafafen yada labarai na kasar sun ba da rahoton samun karuwar hare-hare na jirgi maras matuki da sojoji ke kai wa kan wuraren dakarun RSF a Khartoum da birnin Omdurman da Bahri.
Sojoji sun kara yawan hare-haren da suke kai wa kan RSF a makonnin baya-bayan nan yayin da yakin da ake a kasar ya shiga wata na tara.
- 'An mayar da mata tamkar ganimar yaƙi a Sudan'
- An kashe gwamnan jihar Darfur ta Yamma a Sudan





