Rufewa
To jama'a a nan ne muka kawo karshen rahotannin da muke kawo muku kai tsaye daga wannan shafi na BBC.
Sai gobe Talata idan Allah Ya kai mu. A madadin kowa da kowa ni Muhammad Annur Muhammad nake fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi and A'isha Babangida
To jama'a a nan ne muka kawo karshen rahotannin da muke kawo muku kai tsaye daga wannan shafi na BBC.
Sai gobe Talata idan Allah Ya kai mu. A madadin kowa da kowa ni Muhammad Annur Muhammad nake fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu.

Asalin hoton, Getty Images
Hamshakin attajirin nan shugaban kamfanin samar da kayan kawa a duniya , LVMH, Bernard Arnault ya sake karbe kambin wanda ya fi kudi a duniya daga shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk.
Mujallar Forbes wadda ta bayyana jerin sunayen manyan attajirai na duniya wadda ta bayyana hakan ta kara da cewa kudin da Arnault ya mallaka sun karu zuwa dala biliyan 207.8 wato ya haura na Elon Musk da dala biliyan 3.3.
Mujallar ta bayyana cewa kudin da Arnault da iyalinsa suka mallaka ya kai dala biliyan 207.8 bayan ya karu da dala biliyan 23.6 a ranar Juma'a inda ya wuce na Musk dala biliyan 204.5
Kamfanin attajirin na Faransa, Agache wanda ke da alaka ta gudanarwa da wani kamfanin da ake kira Aglaé wanda Forbes ya ruwaito yana da jari a harkokin da suka hada da Netflix da Bytedance- babban kamfanin da TikTok ke karkashinsa.
Attajirin na daya a duniya mai shekara 74 ya jaddada cewa kamfanin , LVMH na iyalai ne ba shi kadai ba.
A makon da ya gabata ne attajirin ya nada 'ya'yansa biyu a kwamitin gudanarwa na kamfanin

Asalin hoton, State House
Kasar Najeriya ta bayyana rashn jin dadinta dangane da yadda gwamnatin sojin jamhuriyar Nijar ta ayyana ficewarta tare da kasasashen Mali da Burkina Faso daga kungiyar tattalin arzikin Afirka ta ECOWAS ko kuma CEDEAO.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ma'aikatar kasashen wajen Najeriya, Ambassador Francisca Omauli ta fitar, gwamnatin Najeriya ta ce kungiyar ECOWAS ta kwashe shekaru 50 tana iya bakin kokarinta wajen samar da zaman lafiya mai dorewa da mulkin dimokradiyya a yankin Afirka ta yamma.
Sanarwar ta ce "Najeriya na tare da ECOWAS domin samar da tsarin ya dace wajen tabbatar da 'yancin da walwalar 'yan kasashen kungiyar".
Sanarwar ta kara da cewa Najeriya ta yi kokarin kai wa ga dukkan kasashen kungiyar domin warware wannan wahalar da ake fuskanta.
"Yanzu a bayyane take cewa wadanda suke son su fice daga kungiyar ba sa nufin samar da wancan muradin na warware takaddamar da ke tsakani. A maimakon haka, shuagabnnin da ba zababbu ba suna fakewa da jama'a domin dakile musu 'yancin cinsu na zuwa duk inda suke so da kasuwanci da kuma 'yancin zabar shugabannnin da suke so".
Daga karshe sanarwar ta ce kofar najeriya domin tattaunawa a bude take domin warware matsalar da kasashen guda uku wato Nijar da Mali da Burkina Faso domin tabbatar da cewa al'ummar kasashen za su ci gaba da cin moriyar ingantaccen tattalin arziki da mulkin dimokradiyya da kungiyar ECOWAS take dabbakawa.
"Muna kara yin kira ga kasashen duniya da su ci gaba da martaba kungiyar ECOWAS da muradinta na zaman tare da hadin kai".

Asalin hoton, FACEBOOK/BOLA AHMED TINUBU
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa kwamitin mutum 37 da zai yi aikin bayar da shawara kan sabon albashi mafi kankanta a kasar, wanda za a kaddamar a gobe Talata 30 ga watan Janairu a fadar gwamnatin kasar da ke Abuja.
Wata sanarwa da kakakin ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar, Segun Imohiosen ya fitar ta bayyana haka.
Albashi mafi kankanta yanzu a Najeriya shi ne naira dubu talatin, wanda aka amince da shi tun 2019.
Sabon kwamitin ya kunshi wakilai daga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da bangaren 'yankasuwa da kuma 'yan kwadago.
Tsohon shugaban ma'aikatan tarayya Bukar Aji shi ne zai jagoranci kwamitin.
Daga bangaren gwamnatin tarayya akwai karamin ministan kwadago da ayyuka Nkeiruka Onyejeocha da ministan kudi Wale Edun da ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki Atiku Bagudu da shugabar ma'aikatan tarayya Folashade Yemi Esan.
Daga jihohi kuma akwai gwamnan jihar Naija Mohammed Umar Bago da gwamnan Bauchi Bala Mohammed da gwamnan Katsina Umar Dikko Radda da gwamnan Anambra Charles Soludo da gwamnan Osun Ademola Adeleke da gwamnan jihar Cross River Otu Bassey Edet.
Daga bangaren kungiyoyin kwadago akwai shugaban NLC Joe Ajaero da wasu mukarraban kungiyar. Haka shi ma shugaban kungiyar kwadago ta TLCFestus Osifo da sauran mukarrabansa suna ciki.
Kungiyoyin ma'aikata na neman a kara musu mafi kankantar albashin ne daga naira dubu 30, saboda tashin farashin kayayyaki da kuma zubewar darajar naira.

Asalin hoton, ZULUM'S TWITTER
Gwamnnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Farfesa Babagana Zulum ya umarci sababbin shugabannin kananan hukumomin jihar da su tabbatar sun zauna a yankunansu sannan kuma su rika sa hannu a wata rijista sau hudu a kullum domin tabbatar da zamansu a yankunan.
Gwamnan ya bayar da umarnin ne a yau Litinin a Maiduguri, lokacin da yake rantsar da sababbin shugabannin da aka zaba su 27.
Zulum ya kuma umarci ma'aikatar kananan hukumomin jihar da ta samar da na'urorin daukar hoton bayanan mutane a dukkanin kananan hukumomin domin ciyamomin su rika yin rijista sau hudu a kullum domin tabbatar da cewa suna nan a yankunansu.
Shugabannin za su rika yin rijistar ne da karfe 8 na safe da 12 na rana d 2 na rana da kuma karfe 3:30 na yamma.
Ya ce daukar matakin ya zama dole domin maganin ki ko guduwa daga wurin aiki ba tare da wani dalili mai karfi ba, inda ya jaddada cewa barin wajen aiki ba dalili mai kwari laifi ne na tube shugaba.

Asalin hoton, jIGAWA
Gwamnatin jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta kammala dukkanin shirye-shirye na sauya wa daliban jihar 194 da ke karatu a Sudan makarantu zuwa Cyprus da Indiya domin ci gaba da karatunsu na likita.
Da yake gabatar da jawabi ga daliban da iyayensu a gidan gwamnati da ke Dutse, gwamnan jihar Malam Umar Namadi ya ce tun da yaki ya barke a Sudan gwamnatin jihar na bin kadin abubuwan da ke faruwa a kasar.
Gwamnan ya ce tun bayan da aka kammala kwashewa da mayar da dukkanin daliban gida daga Sudan, gwamnatin jihar take ta kokarin sama musu gurbin ci gaba da karatunsu a wata jami'ar da take da kyau sosai domin cimma muradin jihar na samar da isassun ma'aikatan lafiya ga jihar.
Ya ce, ma'aikatar kula da ilimin gaba da sakandire ta jihar ta yi nasarar samun gurbin karatu ga dalibai 184 a Cyprus da kuma 10 a Indiya, kuma an kammala dukkanin shirye-shirye na tashinsu ranar 5 ga watan Fabarairu mai kamawa.
Kwamishinan ma'aikatar ilimin gaba da sakandiren Dr Isa Yusuf Chamo ya ce gwamnatin jihar ta kashe naira biliyan 2.6 a kan guraban karatu da sufuri da rijista da sauran tsarabe-tsarabe a kan daliban 194.

Asalin hoton, Jigawa

Asalin hoton, Jigawa

Asalin hoton, Reuters
Fafaroma Francis ya ce matsayin limaman cocin Katolika na Afirka kan kin yarda da amincewarsa tare da sanya albarka ga auren masu jinsi daya abu ne na musamman.
To amma kuma ya ce yana da kwarin gwiwar cewa sannu a hankali kowa zai samu tabbacin matsayin cocin.
A wata hira da ya yi da wata jarida ta Italiya Fafaaroman ya ce shugabannin coci-cocin Afirka da magoya bayansu suna kallon luwadi daga bangare na al'ada a matsayin wani mummunan abu.
Shugaban Cocin na Katolika ya ce an samar da takardar da aka fitar a watan da ya gabata (Fiducia Supplicans), domin hada kai ba rarraba kai ba
Shugaban ya ce, ba shi da wata damuwa a kan ficewar masu ra'ayin rikau daga Cocin na Katolika saboda sauye-sauyensa yana mai cewa maganar rabuwar kai abu ne da wasu kananan kungiyoyi ke yi.

Asalin hoton, Reuters
An dakatar da tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma daga jam'iyyar ANC, kai tsaye ba tare da bata wani lokaci ba, kamar yadda jam'iyyar ta bayyana a wata sanarwa.
Babban kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta ANC, ya bayyana cewa yanayi ne ya janyo daukar matakin da ya kai ga dakatar da Mista Zuma daga jam'iyyar kai tsaye.
Matakin ya biyo bayan sanarwar da Mista Zuma ya yi ne a watan da ya wuce cewa zai yi wa wata sabuwar jam'iyya yakin neman zabe a babban zaben kasar da za a yi nan gaba a shekarar nan.
ANC ta ce ya zama wajibi ne ta dauki matakin da ta dauka domin kare kimarta da kuma hana ci gaba da bata sunan jam'iyyar.

Asalin hoton, Nichola Mandil/BBC
Hukumomi a jihar Equatoria ta Tsakiya da ke Sudan ta Kudu sun hana sayar da wata mashahuriyar giya bayan da mutane da dama suka mutu sakamakon shan giyar da suka yi a yankin.
Giyar wadda aka fi sani da "Makuei Gin" an ce galibi matasa ba sa iya jurewa sai sun sha.
An ba da rahoton cewa, yawan amfani da giyar ya karu a lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da ba a tantance adadinsu ba.
"Na dakatar da amfani ko shan wannan jar giya mai suna 'Makuei'. Na haramta sayar da ita ko shan ta domin tana kashe matasa da dama, "in ji gwamnan jihar Equatoria ta Tsakiya, Emmanuel Adil Anthony a ranar Lahadi.
Ya kara da cewa, “Matasa da yawa idan suka bugu, sai su rika dukan uwayensu da adduna.
Cocin Anglican da ke babban birnin ƙasar Juba, ta buƙaci gwamnan da ya tabbatar an aiwatar da dokar haramta giyar.
A shekarar da ta gabata ne ministan yaɗa labarai Michael Makuei ya yi kira da a haramta amfani da giyar sannan ya bukaci a rufe masana’antar da ke samar da ita.

Asalin hoton, HANNATU MUSAWA
LinkKungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) bangaren da ke kula da dokar kare maradu da ci gaban al'umma, NBA Spidell na neman babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori ministar Al’adu, Hannatu Musawa daga mukaminta bisa zargin karya dokar bautar kasa ta NYSC.
Kungiyar ta kuma bukaci kotun da ta tilasta wa hukumar NYSC ta soke takardar shaidar da aka bai wa ministar bisa zargin bayar da takardar shaidar da ta saɓawa tanadin dokar NYSC.
Wadanda suka shigar da karar sun hada da Shugaban NBA-SPIDEL, John Aikpokpo-Martins, da Sakatariyar NBA-SPIDEL, Funmi Adeogun.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'ai sun ce an kashe akalla mutum 50 da suka hada da dakarun zaman wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya yayin wani kazamin fada a kan iyakar kasashen Sudan da Sudan ta Kudu.
Wasu mutane dauke da makamai daga jihar Warrap ta Sudan ta Kudu ne dai suka kai wani samame a yankin Abyei mai makwabtaka ranar Asabar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reauters ya rawaito ministan yada labarai na yankin yana fadin hakan.
Har yanzu dai ba a iya gano dalilinsu na kai harin ba. To sai dai kamfanin dillancin labarai na AP ya alakanta ricikin da wanda kabilar Twic Dinka da Ngok Dinka ke yi kan gonaki.
Sudan da Sudan ta Kudu dai kowaccensu na ikrarin mallakar yankin Abyei, inda kuma rikici kan hakan ya ki ci ya ki cinyewa tun 2011 lokacin da Sudan ta Kudun ta samu 'yancin cin gashin kai.

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon Jakadan Burtaniya a Majalisar Dinkin Duniya, Sir Mark Lyall Grant, ya ce "yana da tayar da hankali" kuma shugaban Amurkar, Joe Biden zai so ya mayar da martani.
Ya ce yana hasashen ganin babban martani ga mayakan da ke goyon bayan Iran da ke Syria da Iraq a awa 24 masu zuwa.
To sai dai kuma Mr Grant wanda tsohon maibayar da shawara kan harkokin tsaro ya ce ba ya tunanin Amurka za ta kaddamar da hare-haren "kai tsaye a cikin kasar Iran" kuma ba ya tunanin 'yan Iran din na son ta'azzarar al'amarin.
Ya kara da cewa masu sharhi da dama sun yi zaton al'amura ka kara kazancewa a yankin Larabawa bayan watanni da aka kwashe ana yaki a gaza, sai dai har kawo yanzu rikicin bai bazu ba a yankin.
Mr Grant ya kuma ce shugaban Amurka Joe Biden "ya yi kokari da farko" inda ya dauki matakan dakile kai musu hare-haren da suka hada da aikewa da jiragen yaki zuwa yankin Larabawa da kuma gargadar Iran domin ka da ta janyo rincabewar al'amarin.
Amy da Ano tagwaye ne masu kama da juna sosai, sai dai an sace su daga wurin mahaifiyarsu jim kaɗan bayan haihuwa inda aka raba su da iyalinsu. Bayan tsawon shekaru sai suka gano juna da taimakon TikTok. An gano cewa dubun-dubatar jarirai ne ake sacewa da sayarwa a asibitin kasar Georgia.

Asalin hoton, Google
An gano gawar wata jaririya a bandaki da ke yammacin Yorkshire a ranar Lahadi, kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar.
Nan take aka kira ma'aikatan gaggawa zuwa gurin.
‘Yan sanda sun bayyana lamarin a matsayin wani lamari mai ban tausayi da na rashin imani, sannan ya buƙaci mahaifiyar jaririyar da ta nemi taimakon jinya cikin gaggawa.
Babban sufeton jami'an tsaro a Yammacin Yorkshire, James Entwistle ya ce: "Muna kira ga mahaifiyar jaririyar da ta tuntube mu."
Ya ƙara da cewa mahaifiyar "tana kuma iya bukatar taimakon jinya da kanta".

Asalin hoton, AFP
An dakatar da wani gwanjon kayayyaki kusan 70 na fitaccen ɗan yaƙi da wariyar launin fata na ƙasar Afirka ta Kudu, Nelson Mandela - waɗanda suka haɗa da na'urar taimaka masa wajen sauraron magana, da sandunan tafiyarsa, da gilashin karatunsa da wasu sauran kayansa da dama.
Gidan gwanjon kaya na Guernsey da ke birnin New York a ƙasar Amurka ya sanar da hakan ne a shafinsa na intanet ba tare da bayar da wani dalili ba, amma hakan ya biyo bayan korafe-korafe da aka yi a Afirka ta Kudu kan batun sayar da kayayyakin nasa.
Babbar ‘yar Mandela, Makaziwe Mandela, ta shirya sayar da kayayyakin a wani gwanjo a ranar 22 ga watan Fabrairu, inda ta ce tana son yin amfani da kuɗin ne wajen gina wani wurin tunawa da shi, kusa da inda aka binne shi.
Hukumar kula da al'adun gargajiya ta ƙasar Afirka ta Kudu (Sahra) ta ƙalubalanci aniyar ta Makaziwe Mandela ta sayar da kayan na mahaifinta a gaban kotu, amma ba ta samu nasara ba inda ta kuma ce za ta ɗaukaka ƙara.
Ministan al'adu na Afirka ta Kudu Zizi Kodwa ya ce hana sayar da kayayyakin Mandela ya zama dole saboda "yana da muhimmanci ga al'adun Afirka ta Kudu".
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ambato jikan Mandela, Ndaba yana cewa shi ma yana adawa da gwanjon.
Mandela ya rasu a shekara ta 2013 yana da shekaru 95 a duniya.
Ya shafe kusan shekaru 30 a gidan yari saboda yaƙi da mulkin wariya, kuma shi ne baƙar fata na farko a Afirka ta Kudu da ya zama shugaban ƙasa a shekarar 1994 inda ya sauka daga mulki bayan shekara biyar.

Asalin hoton, ...
Kotun koli za ta sanya ranar yanke hukunci a ƙarar da jam’iyyar APC da ‘yar takarar gwamna, Aisha Dahiru, (Binani), suka shigar suna ƙalubalantar sahihancin zaɓen gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa.
Kotun sauraron ƙorafin zaɓe da kotun ɗaukaka kara sun yi watsi da ƙarar da Binani ta shigar na kalubalantar nasarar Finitiri a zaben gwamna da aka gudanar ranar18 ga watan Maris na 2023.
Alƙalan kotun ƙoli biyar, ƙarƙashin jagorancin John Okoro sun ɗage ci gaba da shari'ar bayan sun saurari bahasi na ɓangarorin da lamarin ya shafa a yau Litinin.
Babban abin da Binani ta ce, ta bakin lauyanta, Akin Olujimi, a zaman da aka yi na yau, shi ne cewa bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnar jihar mai cike da ce-ce-ku-ce da Kwamishinan zabe, Hudu Ari ya yi na kan ƙa'ida ne.
Matakin na ranar Litinin ya zo ne watanni bayan da kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Adamawa tare da yin watsi da ƙarar da Binani ta shigar da cewa bai cancanta ba.

Asalin hoton, ...
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gana domin tattauna takun-saka tsakanin Somaliya da Habasha kan yarjejeniyar da aka kulla ta tashar jiragen ruwa da jamhuriyar Somaliland mai cin gashin kanta.
Gidan talabijin na gwamnatin Somaliya, SNTV, ya ba da rahoton cewa taron na ranar Litinin zai "yi magana game da abubuwan da ke faruwa a ƙasashen biyu".
Rikicin dai ya samo asali ne bayan da Habasha ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Somaliland a farkon wannan watan.
Yarjejeniyar ta bai wa Habasha, wadda ba ta da tudu damar samun tashar jiragen ruwa don ayyukan soji da kasuwanci.
Somaliya wacce ta ɗauki Somaliland a matsayin wani bangare na yankinta, ta yi watsi da yarjejeniyar tare da zargin Habasha da keta 'yancinta.

Asalin hoton, Ecowas
Ministan harkokin wajen Saliyo, Timothy Musa Kabba, ya musanta zargin da kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da ke karkashin jagorancin mulkin soji suka yi na cewa Ƙungiyar kasashen Afirka ta yamma, Ecowas na karkashin ikon kasashen waje.
A ranar Lahadi ne kasashen uku suka sanar da ficewarsu daga ƙungiyar ta Ecowas, suna masu cewa kungiyar tana karkashin ikon kasashen ketare, tana cin amanar ka'idojin kafa ta, kuma ta zama barazana ga kasashe mambobinta da al'ummominsu.
Kabba, wanda yana cikin tawagar da ke shiga tsakani, tsakanin Ecowas da gwamnatocin mulkin sojan kasashen, ya shaida wa shirin gidan rediyon Newsday na BBC cewa wannan zargin ba shi da dadi, domin kuwa Ecowas tana shiga tsakani ne kan juyin mulkin da aka yi a ƙasashen da nufin samar da mafita ga wannan matsala da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a ƙasashen.
Ya kara da cewa "Kuma ba mu a karkashin ikon wata hukuma ta waje don shiga tsakani tsakanin Ecowas da hukumomin Nijar."
Dangantaka tsakanin kungiyar da kasashen uku ta yi tsami ne bayan gaza cimma matsaya kan yadda za a sasanta batun juyin mulki da aka samu a cikin su.
Kungiyar ta kakaba musu takunkumin tattalin arziki, bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar a shekarar 2023, Burkina Faso a 2022 da Mali a shekarar 2020.

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Likitoci ta Najeriya, NMA ta sanar da matakin janye ayyukanta a asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano har sai yanda hali ya yi bayan da wasu da ta kira 'fusatattun mutane dauke da makamai' suka far wa wani likita da ke bakin aiki.
Kungiyar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da sakatarenta ya fitar ranar Lahadi inda ta ce yan'uwan wata mata da ke jinya ne suka tayar da hatsaniya inda suka boye likitan sai dai daga bisani mahaifin likitan, wanda shi ma yake aiki a asibitin ya samu kubutar da ɗansa.
Zuwa yanzu, BBC ba ta kai ga tantance abin da ya sa mutanen suka far wa likitan ba.
Kungiyar ta ce shugabanninta sun je wajen da lamarin ya faru inda suka lura cewa akwai rashin isasshen tsaro a asibitin abin da ta ce babban kalubale ne ga ma'aikatan lafiya da ke aiki a asibitin.
Sakataren kungiyar ta NMA ya ce dalilin haka ne ya zama dole kungiyar ta janye mambobinta daga aiki cikin yanayi na rashin tabbas har sai hukumomin asibitin sun tabbatar masu da tsaro.
A cewar kungiyar, za su ci gaba da bibiyar yanayin tare da shawartar mambobinsu.