Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza

  1. Kotun Kenya ta dakatar da shirin gwamanti na karɓar harajin gidaje

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Wata kotu a Kenya ta dakatar da shirin gwamnatin kasar na karɓar harajin gidaje daga al'umma, har sai an saurari karar da ake yi kan lamarin da kuma yanke hukunci.

    Babbar Kotun ta gano cewa harajin ba bisa ka'ida ba ya shafi 'yan kasar Kenya da ke aiki a fannin ma'aikatun gwamnati.

    Tun a watan Yulin shekarar da ta gabata ne gwamnati ta fara cire kashi 1.5% na yawan albashin ‘yan ƙasar da kuma na ƙasashen waje, domin gina gidaje masu rahusa ga masu karamin karfi.

    Matakin harajin dai ya janyo ce-ce-ku-ce daga ɓangaren 'yan adawa da kuma wani ɓangare na al'umar da dama, wadanda ke ganin rashin dacewar ɓullo da harajin a karkashin Shugaba William Ruto.

    Gwamnati ta yi zargin cewa dakatar da harajin zai jefa dubban ma'aikata a karkashin shirin gina gidaje cikin rashin aikin yi da kuma karya kwangilolin da aka riga aka sanya wa hannu.

    Shari’ar dai na daga cikin kararrakin da suka haifar da rashin jituwa tsakanin bangaren shari’a da zartarwa, inda shugaba Ruto ya zargi alƙalan da cin hanci da rashawa da hada baki da ‘yan adawa wajen yin zagon kasa ga ayyukan ci gaban kasa.

  2. An fara zaman kotu kan kiran Isra'ila ta tsagaita buɗe wuta a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Kotun Majalisar Dinkin Duniya ta fara zamanta kan kiran Isra'ila ta tsagaita buɗe wuta a Gaza

    Kotun za ta yi la'akari da matakan gaggawa guda tara da Afirka ta Kudu ta gabatar, amma ba zargin kisan kiyashi da Isra'ila ta yi ba.

    Daga cikin wadannan matakan har da Isra'ila ta dakatar da ayyukan soji nan take a Gaza.

  3. Hotunan yadda ake shirin fara yanke hukunci a ƙarar da Afrika ta Kudu ta shigar kan Isra'ila

    Ga wasu hotuna guda biyu da aka dauka daga cikin harabar kotun Majalisar Dinkin Duniya da za a yanke hukunci a ƙarar da Afrika ta Kudu ta shigar kan Isra'ila

    ...
    ...
  4. Sarki Charles ya je asibiti kan lalular mafitsara

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    An kwantar da Sarki Charles a asibiti domin jinyar lalurar mafitsara, in ji fadar Buckingham.

    Za a yi masa aiki kan lalurar ne a wani asibitin mai zaman kansa da ke birnin Landan, inda aka yi wa Gimbiya Catherine tiyata a makon da ya gabata.

    An fahimci cewa, Sarkin ya ziyarci Gimbiya Wales da ke jinya a asibitin a safiyar yau, gabanin nasa aikin da za a yi.

    Har yanzu ba a san tsawon lokacin da Sarki Charles zai kwashe a asibitin ba.

    Sarki Charles ya bayyana wa jama'a lalurar da yake fama da ita ne a matsayin wani mataki na ƙarfafa wa maza gwiwa wajen ganin sun je an duba su don kauce wa illar cutar mafitsara.

    Wata sanarwa da fadar Buckingham ta fitar ta ce 'Sarkin ya yi farin ciki da sanin cewa batun cutar tasa na taimakawa wajen wayar da kan jama'a game da lafiyarsu.'

    • Abin da ya sa Sarki Charles ba zai halarci taron COP27 na bana ba
    • Nakan ji kunya idan matata ta wanke shimfiɗar da muka kwanta - Miji mai fitsarin kwance
  5. Rikicin Filato: 'Na ga gawawwaki yashe a kan titi'

  6. An gurfanar da limamin cocin da ya buƙaci a kai wa firaministan Habasha hari

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Masu gabatar da kara a Habasha sun gurfanar da wani fitaccen limamin coci wanda ya yi kira da a kai hari kan firaministan ƙasar Abiy Ahmed.

    Abuna Lukas, babban limamin cocin Christian Orthodox, ya bayyana a kanun labarai a watan da ya gabata lokacin da ya ce baƙaƙen aljanu ke wa Firaministan jagoranci wajen mulkin kasar kuma ya bukaci masu imani da su "harbe shi da dutse a gaɓar goshinsa kamar yadda aka yi wa Dauda a labarin da ya zo cikin littafin baibul.

    A jawabin da ya yi a Amurka, Abuna Lukas ya yi Allah-wadai da hare-haren da gwamnati ta kai da jiragen yaƙi a yayin da sojoji ke fafatawa da kungiyoyi masu dauke da makamai a wurare da dama a fadin kasar.

    Ya kuma shawaraci sojoji da su dauki makami domin yaƙar gwamnatin Abiy.

    A cewar rahotanni daga kafofin yaɗa labarai masu alaka da gwamnati, ma'aikatar Shari'a ta Habasha ta shigar da kara kan laifuka biyu a kan babban limamin cocin saboda tayar da zaune tsaye da kuma kin yin aikin da ya kamata tare da yaɗa farfaganda "wanda aka tsara don inganta muradun abokan gaba."

    Ana zargin babban limamin cocin ne da ƙoƙarin hana matakan gwamnati na tabbatar da doka a kan masu adawa da zaman lafiya.

    • Yakin basasar Habasha: Yadda Fira Minista Abiy ya jagoranci yaki da 'yan tawaye
    • Yankin Tigray: Yaƙin Habasha na dab da ƙarewa in ji firaminista Abiy
  7. Sojojin mulkin Mali sun kawo ƙarshen yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawayen Abzinawa

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin mulkin sojan ƙasar Mali ta sanar da kawo ƙarshen yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma da 'yan tawayen Abzinawa a arewacin ƙasar a shekara ta 2015, matakin da zai ƙara dagula al'amura a yankin Sahel.

    Yarjejeniyar zaman lafiyar dai na da nufin kwantar da tarzoma ne a daidai lokacin da Abzinawa ke ci gaba da tashe tashen hankulla da gwamnatin tsakiya tun a shekara ta 2012.

    Amma an aiwatar da wani bangare ne kawai na yarjejeniyar.

    Hukumomin soji sun fada a yammacin ranar alhamis cewa yarjejeniyar da ake kira Algiers Accord, wacce Majalisar Dinkin Duniya ke ƙullawa, ya kare da nan take.

    A cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na ƙasar, kakakin gwamnatin mulkin soja, Kanar Abdoulaye Maïga, ya ce an kawo karshen yarjejeniyar ne saboda wasu ƙasashen da suka rattaba hannu kan rashin cika alkawuran da suka dauka da kuma nuna adawa da babban mai shiga tsakani na Aljeriya.

    Kawo yanzu dai babu wani martani daga gwamnatin Aljeriya.

    • Rayuwa a biranen Mali da ƴan bindiga suka yi wa ƙawanya
    • Juyin mulki a Mali: Sojojin da suka jagoranci hamɓarar da Keita
  8. Ƴan sandan Najeriya sun kama wasu manyan waɗanda ake zargi a rikicin Filato

    'Yan sanda a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya sun ce an kama manyan waɗanda ake zargi tara a sabbin hare-haren da aka kai a yankin Mangu na Jihar.

    Aƙalla mutane 50 ne aka ruwaito an kashe a cikin kwanaki biyu da aka dauka ana gwabza faɗa tsakanin ƙabilu.

    Wasu mahara ɗauke da makamai dai sun kai hari a ƙauyukan da ke kusa da garin Mangu a ranar Larabar da ta gabata, kwana guda bayan da aka ƙona masallatai da majami'u a arangama tsakanin kabilu biyu da ke gaba da juna.

    Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya Janar Edward Buba, ya ce an tura dakaru na musamman zuwa wuraren da ke fama da tashe-tashen hankula a jihar domin shawo kan lamarin.

    • Yadda sabon rikici a Filato ya janyo saka dokar hana fita a Mangu
    • Abin da ya haddasa zanga-zangar da ta kai ga ƙona fadar hakimi a Filato
  9. 'Yan gudun hijirar Sudan rabin miliyan sun isa Sudan na Kudu - MDD

    ...

    Asalin hoton, IOM South Sudan

    Hukumar jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce Sudan ta Kudu ta karɓi sama da mutane rabin miliyan da ke gudun hijira a makwabciyarta Sudan.

    A cikin rahotonsa na baya-bayan nan game da rikicin Sudan, ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya ce an samu jimillar mutum 516,658 da suka tsallaka kan iyaka zuwa Sudan ta Kudu tun bayan ɓarkewar faɗa a Sudan a ranar 15 ga Afrilun 2023.

    Ya ƙara da cewa, kusan kashi 81 cikin 100 na baƙin 'yan ƙasar Sudan ta Kudu ne, kashi 18 cikin 100 kuma 'yan gudun hijirar Sudan ne.

    Ocha ya kuma ce an samu “ƙaruwa sosai” a yawan ‘yan gudun hijirar Sudan da masu neman mafaka a Sudan ta Kudu a wannan watan.

    Hukumar ta kuma ce karuwar ‘yan gudun hijirar da ke shigowa ta garin Renk na Sudan ta Kudu na fuskantar kalubalen tsaro ga hukumomin yankin da kuma abokan huldar jin kai.

    • 'Mu na cikin mawuyacin hali a Sudan'
    • 'An mayar da mata tamkar ganimar yaƙi a Sudan'
  10. An kama yaran mista Ibu kan zargin satar gudunmawar miliyan 55 na jinyarsa

    ...

    Asalin hoton, Mr Ibu/Instagram

    Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama ɗa da kuma ɗiyar fitaccen jarumin fina-finan barkwancin nan na Najeriya, John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu, bisa zargin satar gudunmawar kuɗin da aka shirya domin jinyar jarumin.

    Ana zargin Onyeabuchi Okafo da Jasmine Okekeagwu da laifin “daukar wayar jarumin tare da yin kutse cikin bayanan bankinsa”, kafin suka sace naira miliyan 55.

    Kuɗaɗen dai na daga cikin gudunmawar kuɗaɗen da masoyan jarumin suka bayar domin jinyarsa, bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya a bara.

    Cutar ta yi sanadin yanke kafar Okafor daya. An kuma yi wa tauraron nollywood din tiyata biyar, in ji iyalansa.

    Hukumomin ƙasar dai sun ƙwato naira miliyan 50, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka ruwaito kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, Mayegun Aminat ya bayyana.

    Ƴaran nasa da ake zargin na shirin tserewa ne zuwa Birtaniya, a cewar Aminat.

    Kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun kuma ruwaito cewa wata kotu a Legas ta saki mutanen biyu kan belin Naira miliyan 15 yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

    Ana sa ran za su gurfana a gaban kotu a watan Maris don ci gaba da sauraren karar.

  11. An aiwatar da hukuncin kisa na farko ta hanyar amfani da sinadarin nitrogen a Amurka

    ...

    Asalin hoton, WHNT/CBS

    Jihar Alabama ta Amurka ta zartar da hukuncin kisa a karo na farko ta hanyar amfani da sinadarin nitrogen kan wani Kenneth Smith da ake rike da shi a gidan yari.

    Kenneth Smith da aka samu da laifin kisa, an yanke masa wannan hukunci ne bayan kotun koli ta yi watsi da karar da aka ɗaukaka a gabanta domin nema masa sasauci.

    Jami'ai dai na cewa salon kashe shi, sassauci ne a gareshi, yayin da masu suka ke cewa an nuna rashin imani.

    An dai biya Smith kuɗi ne ya kashe wata matar wani mai wa'azi, Elizabeth Sennett, inda aka kama shi da laifi kuma aka kama shi tun a cikin shekarar 1989.

    A cewar Cibiyar Bayar da bayani kan Hukuncin kisa, Smith shine mutum na farko da aka kashe ta hanyar amfani da sinadarin iskar nitrogen a duk faɗin duniya.

    A jawabinsa na karshe, Smith ya ce kwata-kwata babu tausayi a zuƙatan wasu.

    Wata sanarwa, da aka fitar ya ce gwamnar Alabama, Kay Ivey, ta ce wannan hukunci shi ne daidai da abin da Smith ya aikata.

    • Jerin mutanen da ke jira a aiwatar musu da hukuncin kisa a Iran
    • Ana tuhumar mutum takwas da laifin tayar da gobarar da ta kashe 'yan ci-rani a Mexico
  12. Kotun Duniya za ta yanke hukunci a karar da Afrika ta Kudu ta shigar kan Isra'ila

    ..

    Asalin hoton, EPA

    A yau Juma'a ake saran kotun Majalisar Dinkin Duniya za ta yanke hukuncin da zai bukaci Isra'ila ta gaggauta kawo karshen ayyukanta na soji a cikin Gaza.

    Shari'ar da ake gudanarwa a kotun hukunta manyan laifuka da ke Hague wani bangare ne na karar da Afirka ta Kudu ta shigar, da ke zargin Isra'ila da aikata kisan kare dangi kan Falasdinawa.

    Isra'ila dai ta fito karara ta musanta wannan zargi kuma da alama za ta yi burus da duk wani hukuncin ko umarni daga wannan kotu.

    Sai dai duk hukuncin da za a yanke kan bukatar tsagaita wuta zai kara matsin kaimi kan kiraye-kirayen da ake yi wa Isra'ila na ganin ta tsagaita wuta.

    Fiye da Falasdinawa 25,000 - akasari mata da yara - aka kashe sannan dubbai sun jikkata, a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas da ke Gaza tun lokacin da Isra'ila ta soma mamayar da ta samo asali daga harin ba-zata da kungiyar ta kai kan Isra'ila.

    Kungiyar Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba ta kashe kimanin mutum 1,300 galibi farar hula. Maharan sun kuma yi garkuwa da mutum 250 a Gaza.

    Afirka ta Kudu wadda ke goyon bayan Falasdinawa ta nemi kotun ta dauki wasu matakai tara ciki har da dakatar da ayyukan soji da Isra'ila take a Gaza. Sai dai ba a tsammanin yanke hukunci a kan wannan na dogon lokaci, watakila shekaru.

    Isra'ila ta fusata da zarge-zargen kisan kiyashi inda ta zargi Afirka ta Kudu da sauya gaskiya. Ta ce tana da ikon kare kanta kuma tana kai hare-hare ne kan mayakan Hamas ba wai farar hula Falasdinawa ba.

    Ta bukaci alkalai ta yi watsi da bukatar Afirka ta Kudu inda ta ce zarge-zargen ba su da tushe bare makama.

    Dole ne alkalai 17 da za su saurari karar su amsa tambayoyi biyu:

    • Na farko, ko Afirka ta Kudu tana da hurumin da zai nuna cewa za a iya hukunta Isra'ila karkashin yarjejeniyar hana kisan kiyashi ta 1948. Yarjejeniyar da Isra'ila da Afirka ta Kudu suka sa wa hannu.
    • Na biyu, ko akwai hadarin illata Falasdinawa a Gaza idan sojojin Isra'ila suka ci gaba da kai hari.
    • Netanyahu ya yi fatali da buƙatar Amurka ta kafa ƙasar Falasɗinawa
    • Za mu iya daidaita alaƙa da Isra'ila amma bisa sharaɗi - Saudiyya
  13. Barka da Juma'a - Babbar Rana

    Jama'a assalamu alaikum, da fatan mun tashi cikin koshin lafiya.

    A yau ma, za mu kawo muku rahotanni da labarai na abubuwan da ke faruwa a duniya musamman Najeriya da sauran kasashe makwabta.

    Sai ku kasance tare da mu. Kuna kuma iya lekawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon bidiyon da ake wallafawa a kai a kai.