Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, A'isha Babangida and Abdullahi Bello Diginza

  1. Kotu ta yanke wa masu yunƙurin juyin mulki a Ghana hukuncin kisa

    ....

    Asalin hoton, AFP

    Wata babbar kotu a Ghana ta yanke wa wasu ‘yan Ghana 6 da suka haɗa da sojoji uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsu da hannu a wani yunƙurin juyin mulki shekaru uku da suka gabata.

    Wannan dai shi ne karo na farko da aka yi shari'ar cin amanar kasa a Ghana tun shekarar 1966 lokacin da aka hamɓarar da gwamnatin Kwame Nkrumah bayan samun 'yancin kai.

    An kama mutanen 6 ne a shekarar 2021 a lokacin da suke gwajin makamai a babban birnin kasar, Accra, da nufin hamɓarar da gwamnati.

    Waɗanda aka yankewa hukuncin, ciki harda mai ƙera bindiga, sun musanta aikata laifin a yayin shari’ar da ta ɗauki hankulan al’ummar kasar.

    Lauyoyin da ke kare su sun ce za su daukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun ta yanke.

    An saki wasu mutum uku da suka haɗ da babban ɗan sanda daya da wasu sojoji biyu.

    An dai jibge jami'an tsaro da yawa a wajen babbar kotun da ke birnin Accra yayin yanke hukunci a ranar Laraba.

    Kotun ta samu mutanen shida da laifin cin amanar kasa da haɗa baki wajen aikata babban laifi.

    • Wani sojan ruwa ne ya jagoranci yunkurin juyin mulki a Gambia - Gwamnati
    • Jerin mutanen da ke jira a aiwatar musu da hukuncin kisa a Iran
  2. An yanke wa wani mutum hukuncin kisa kan tayar da gobara a Japan

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    An yanke wa wani ɗan kasar Japan hukuncin kisa bisa samunsa da laifin tayar da gobara a wani ɗakin shirya hotuna masu motsi na Kyoto animation a shekarar 2019 wanda ya kashe mutane 36 tare da jikkata wasu da dama.

    Lamarin ya kasance ɗaya daga cikin mafi muni cikin shekaru na baya-bayan nan wanda aka rasa mafi yawan matasa masu fiƙirar zane da kuma girgiza duniyar shirya hotuna masu motsi.

    Shinji Aoba, mai shekaru 45, ya amsa laifin kai harin amma lauyoyinsa sun nemi a yanke masa hukunci mai sauƙi inda suka yi iƙirari cewa yana da matsalar ƙwaƙwalwa.

    Amma alƙalan sun ƙi amincewa da buƙatarsu inda suka ce Aoba ya san abin da yake yi.

    "Na tabbatar da cewa wanda ake tuhuma bai da wata matsalar ƙwaƙwalwa ko rauni a lokacin daya aikata laifin", in ji Babban Alƙali Masuda a ranar Alhamis a wata kotu da ke yankin Kyoto.

    "Mutuwar mutum 36 abu ne mai tsanani da ban takaici. Fargaba da kuma raɗaɗin waɗanda suka rasa ransu a gobarar ba zai kwatantu ba", in ji shi a cewar rahotannin NHK.

    An kashe da yawa daga cikin ma'aikatan dakin shirya hotuna masu motsi bayan sun maƙale a saman bene na ɗakin yayin da gobarar ke yaɗuwa.

    Wannan da ɗaya daga cikin al'amuran da suka fi tayar da hankali a cikin 'yan shekarun nan a Japan, lamarin dai ya haifar da makoki na kasa. Jama'a da kafofin yada labaran ƙasar sun yi ta bibiyar lamarin sosai.

    • Gobara ta ƙona kimanin shaguna 50 a kasuwar Singa
    • Abu bakwai da ke haddasa gobara a lokacin hunturu a Najeriya
  3. Yaran da suka yi ƙiba a lokacin annobar cutar korona na iya fuskantar matsalar lafiya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Masana kimiyya a Biritaniya suna gargaɗin cewa yaran da suka yi ƙiba a lokacin ɓarkewar cutar korona na iya fuskantar ƙalubalen lafiya na tsawon rayuwarsu.

    Rashin zuwa makaranta na tsawon lokaci da rashin motsa jiki da kuma rashin cin abinci mai gina jiki, na cikin dalilan da aka lissafa wanda suka haifar da mummunar kiba a tsakanin yara.

    Masanan Sun ce hakan na iya janyo wa tattalin arziƙin Birtaniyya asarar fiye da dala biliyan goma nan gaba saboda abubuwa da za su jibanci ƙarin kuɗin kiwon lafiya.

    • Akwai alama korona na shirin dawowa
    • Sabon bincike ya fito da sabbin bayanai kan wurin da korona ta samo asali
  4. Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar Aliyu a matsayin Gwamnan Sokoto

    ....

    Asalin hoton, Ahmed Aliyu/X

    Kotun koli ta tabbatar da zaɓen Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar Sokoto.

    Kotun koli a wani mataki na bai ɗaya ta yi watsi da ƙarar da Sa'idu Umar na jam’iyyar PDP ya shigar na ƙalubalantar nasarar Aliyu a zaɓen gwamna da aka gudanar a watan Maris na 2023.

    • Ahmad Aliyu na APC ya lashe zaɓen jihar Sokoto
    • Waɗanne kalubale sabbin gwamnonin Sokoto da Zamfara za su fuskanta?
  5. Agbu Kefas ne halastaccen gwamnan jihar Taraba

    ....

    Asalin hoton, Agbu Kefas/X

    Kotun koli ta tabbatar da zaɓen Agbu Kefas na jam'iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Taraba.

    Kotun kolin a wani mataki na bai daya ta yi watsi da daukaka karar da Farfesa Yahaya Sani na jam’iyyar NNPP ya yi kan rashin cancantar Kefas tsayawa takarar gwamnan jihar.

    • Ni ne dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a Taraba — Sanata Bwacha
    • Halin da ake ciki bayan kashe-kashen ƙabilanci a Taraba
  6. Kotu ta tabbatar da Fubara a matsayin gwamnan Rivers

    ...

    Asalin hoton, RIVERS STATE GOVERNMENT

    Kotun koli ta yi watsi da ɗaukaka karar da Tonye Cole, ɗan jam’iyyar APC ya shigar in da yake ƙalubalantar nasarar Siminalayi Fubara na jam'iyyar PDP a Zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na 2023 a jihar Rivers.

    Kotun ta tabbatar da Fubara a matsayin gwamnan jihar.

    Kotun ta ce Cole bai tabbatar da zarginsa ba na cewa Fubara bai cancanta tsayawa takarar ba saboda bai bai yi murabus daga mukamin babban akanta janar na jihar Rivers ba kafin zaɓen wanda hakan ya saɓawa dokar zaɓe.

    Kotun ta ce karar da aka shigar bai yi nasara ba kuma ta yi watsi da shi.

    • Ƙuri'un da ba za a iya bayaninsu ba a zaɓen Najeriya mai cike da taƙaddama
    • Me zai faru a jihar Ribas bayan soke ‘yan takara ta APC
  7. An zaɓi sabon Baba Addini na jihar Legas

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Mataimakin shugaban babban masallacin Legas, Alhaji Sikiru Alabi-Macfoy, ya zama Baba Adinni na 14 na Legas.

    Zamowar Alhaji Alabi-Macfoy a matsayin baba Addinin ya biyo bayan zaben da aka yi cikin lumana a ranar Laraba a babban masallacin Legas da ke unguwar Idumota.

    Daga cikin mutane uku da suka nuna sha’awar wannan muƙamin, mutum biyu ne suka samu halartar tantancewar da aka yi, wato Alhaji Alabi-Macfoy da kuma Alhaji Jelili Animashaun.

    Daya daga cikin ‘yan majalisar tafiyar da lamurran babban masallacin na Legas, Alhaji Fatai Dawodu, shi ne ya jagoranci kwamitin tantancewa na mutane 30.

    Ƴan takarar biyu sun sha tambayoyi kafin 'yan kwamitin suka fara kada kuri'a.

    Alhaji Alabi-Macfoy ya yi nasara da kuri’u 22 yayin da Alhaji Animashaun ya samu kuri’u takwas.

    Nasararsa a matsayin Baba Adinni, Cif Alabi-Macfroy zai gaji Sheikh AbdulHafeez Abou, wanda ya rasu a ranar 9 ga watan Janairu yana da shekara 101.

    • Mun dawo daga rakiyar gwamnatin Tinubu - Majalisar Shari'ar Musulunci
    • Rashin cunkoso a titunan Legas asara ce ga Najeriya
  8. 'An gargaɗi Israi'ila game da wani matsugunin Falasɗinawa a Gaza kafin ta kai masa hari'

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Wani babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya ce an gargadi Isra'ila game da wani ginin da ke matsugunin Falasdinawa da dama a Gaza kafin ta kai masa hari.

    Philippe Lazzarini ya ce harin da aka kai a jiya Laraba kan wata cibiyar horarwa wanda ya kashe akalla mutane tara ya nuna rashin mutunta ka'idojin yaki.

    Mataimakin kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Vedant Patel, ya yi Allah wadai da harin.

    Ya ce dole ne a mutunta gine-ginen majalisar dinkin duniya kuma dole ne a kare lafiyar ma’aikatan jin-kai domin su iya bayar da agajin da ake bukata.

    • Isra'ila ta ɗau alwashin ci gaba da kai farmakin soji a Gaza har sai ta cimma burinta
    • Yaƙin Gaza : Afirka ta Kudu ta kai ƙarar Isra'ila Kotun Duniya
  9. Ajantina: Dubban mutane sun yi zanga-zangar nuna adawa da sauye-sauyen tattalin arziki

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubunnen mutane ne suka yi zanga-zanga a wajen Majalisar dokoki a Buenos Aires babban birnin Argentina, don nuna adawa da sauye-sauyen tattalin arziki da shugaba Javier Milei ya gabatar.

    Ma’aikata kuma na gudanar da yajin aiki na sa’o’i goma sha biyu, inda Shugaban ƙungiyar ƙwdago ta Argentina, Héctor Daer, ya ce za a gudanar da sabbin zanga-zanga da yajin aiki har sai an janye sauye-sauyen.

    Kakakin shugaba Milie, Manuel Adorni, ya ce yajin aikin ba shi da amfani, ya ce tabbas, sun dauki wannan yajin aikin a matsayin rashin hankali, babu abin da zai haifar sai asarar kuɗi ga daukacin al’ummar Argentina.

    • Zimbabwe: Zanga-zanga kan tabarbarewar tattalin arziki
    • 'Farashin kayan abinci zai ci gaba da tashi a Najeriya'
  10. Volodymyr Zelensky ya ce Rasha ta yi kasada da rayuka a cikin jirgin da ya faɗo

    ...

    Asalin hoton, ...

    Shugaba Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da wasa da rayukan fursunonin yaƙi na Ukraine, bayan da Moscow ta ce 65 daga cikinsu sun mutu a jirgin da sojojin Ukraine suka harbo.

    Jirgin ya faɗo ne a kudu maso yammacin ƙasar Rasha, kusa da kan iyakar ƙasashen biyu.

    Ya ce Wajibi ne a tabbatar da samun cikakkun bayanai bisa la'akari da cewa lamarin ya auku ne a cikin ƙasar Rasha inda ba su da iko.

    Rasha ta ce babu wanda ya tsira a hatsarin jirgin da ke dauke da fursunonin yaƙin Ukraine 65 da ma'aikatan jirgin Rasha 6 da rakiyar 3.

    Moscow ta yi ikirarin cewa ana jigilar 'yan Ukraine din ne don musayar fursunoni.

    Hukumar bayanan sirri na sojin Ukraine (GUR) ta ce ba a sanar da su tabbatar da tsaron sararin samaniya ba, kamar yadda aka saba yi a baya.

    • Mutum 32 sun mutu a hatsarin jirgi a Rasha
    • Me ke faruwa tsakanin Ukraine da Rasha bayan ɓarkewar faɗa a Gaza?
  11. Fursunan Amurka na farko da za a yi wa hukuncin kisa da iskar nitrogen, Daga Muhammad Annur Muhammad

    ..

    Asalin hoton, ALABAMA DEPARTMENT OF CORRECTIONS

    Kotun Kolin Amurka ta yi watsi da bukatar hana aiwatar da hukuncin kisa na farko ta hanyar amfani da iskar Nitrogen a kasar.

    A yau Alhamis ne za a aiwatar da hukuncin kisan a kan Kenneth Eugene Smith,wanda kotu ta same shi da laifin kisan kai a 1989.

    Wannan fursuna da za a fara yi wa wannan sabon tsari na aiwatar da kisan kai, wanda ba a taba gwada shi ba, Kenneth Eugene Smith ya gaza tsallake wannan siradi ne, bayan da ya yi rashin nasara a karar da ya daukaka ko rokon da lauyoyinsa suka gabatar biyu na karshe na neman dakatar da zartar da kisan ta wannan sabuwar hanya ta amfani da iskar gas ta Nitrogen.

    A sanarwar hukuncin da ta fitar mai layi biyu kacal, kotun kolin ta ce ta yi watsi da bukatar Kenneth Smith ta sake duba shari’ar.

    Bayan Kotun Kolin akwai kuma wata karamar kotun da ita ma ta zabi da kada ta sa baki a lamarin a dakatar da hukuncin, wanda ake sa ran aiwatarwa yau Alhamis din nan.

    Yadda za a yi masa wannan hukunci dai shi ne, za a sanya daura masa takunkumi ne a fuska da ba zai iya shakar iska da shi ba, sai dai iskar Nitrogen wadda za ta hana shi samun iskar Nitrogen wadda jiki ke bukata, wato tamkar a yi wa mutum kanshin mutuwa.

    Gwamnan jihar Alabama ya ce an yi nazarin wannn sabon tsari an kuma tabbatr ba shi da wata illa, amma duk da haka kwararru da dama sun yi watsi da ikirarin gwamnan;

    Dr Joel Zivot,malamin jami’a aGeorgia,ya ce ba lalle ba ne mutumin ya mutu da wuri ta wannan hanya;

    "Tsawon wane lokaci zai mutu ba a sani ba, amma duk da haka ina jin jihar na da damar da za ta jira har ya mutu.’’ in ji Dr Zivot.

    Tuni majalisar dinkin duniya ta bukaci a dakatar da aiwatar da kisan, da cewa sabon tsarin kamar azabtarwa ne.

    A shekarar 1989 ne kotu ta samu Smith da laifin kisan matar wani mai wa’azi wanda ya biya shi kudi tare da wani mutumin su biyu, kowanne dala dubu daya su kashe matar.

    Shekara biyu da ta gabata Smith ya yi nasarar hana aiwatar da hukuncin kisan a kansa ta hanyar amfani da allurar guba.

    • Jerin mutanen da ke jira a aiwatar musu da hukuncin kisa a Iran
    • Ana tuhumar mutum takwas da laifin tayar da gobarar da ta kashe 'yan ci-rani a Mexico
  12. Barka da Hantsi!

    Masu bibiyar mu ta wannan shafi na Kai Tsaye, assalamu alaikum. Da fatan mun wayi gari lafiya a wannan rana ta Alhamis.

    A yau ma, muna tafe da rahotanni da labarai na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

    Akwai kuma shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da Instagram da kuma X inda za ku iya karanta karin labarai da kuma kallon bidiyon da aka wallafa.

    Da fatan za ku kasance tare da mu tun daga yanzu har zuwa lokacin da za a rufe shafin na Kai Tsaye.