'Har yanzu ba a bi wa waɗanda jirgin sojin Najeriya ya yi wa ruwan wuta a Nasarawa hakki ba'

Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza

  1. Gwamnan Ondo ya rusa majalisar zartarwar jihar

    ...

    Asalin hoton, LUCKY AIYEDATIWA/TWITTER

    Gwamnan jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa ya rusa majalisar zartarwa ta jihar.

    Gwamnan ya kuma sauke dukkan manyan mataimaka da mataimaka na musamman daga ayyukansu.

    A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran sa, Ebenezer Adeniyan ya fitar a ranar Laraba, gwamnan ya ce wannan matakin zai fara aiki nan take.

    Sanarwar ta ce, “Dukkan mambobin majalisar za su mika ayyukansu ga manyan sakatarorin dindindin ko kuma manyan jami’an gudanarwa a ofisoshinsu.

    “An umurci dukkan jami’an da abin ya shafa da su mika duk kadarorin gwamnati da ke hannunsu.

    “Gwamnan ya godewa jami’an da abin ya shafa bisa ayyukansu da kuma gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar.”

    An dai rantsar Aiyedatiwa, tsohon mataimakin gwamnan Ondo a ranar 27 ga Disamban 2023 a matsayin gwamnan jihar bayan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu.

    Akeredolu, mai shekaru 67, ya rasu ne a lokacin da yake jinyar cutar kansar mafitsara a wani asibitin ƙasar Jamus.

    • Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya rasu
    • Jihohin da ba za a yi zaɓen gwamna ba a ranar Asabar
  2. Ghana ta kori kocinta bayan fitar da ita daga Afcon

  3. Ana gwabza ƙazamin faɗa tsakanin sojojin Somaliya al-Shabab

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Ana gwabza kazamin fada a tsakiyar ƙasar Somaliya bayan da mayaƙan al-Shabab suka kai hari kan sansanonin soji a yankin Mudug.

    Shaidun gani da ido sun shaida wa BBC cewa sun ji ƙarar harbe-harbe da fashewar abubuwa a safiyar ranar Laraba.

    Rahotanni sun ce harin ya fara ne da harin ƙunar baƙin wake, wanda ke harin dakarun gwamnati na musamman.

    Ministan tsaron Galmudug Mohamed Abdi Aden ya shaidawa BBC cewa har yanzu sojoji suna fafatawa da 'yan ta'adda a ƙauyen Aad, inda sansanonin sojoji suke.

    Kamfanin dillancin labaran kasar Somaliya (Sonna) ya bayar da rahoton cewa, sojojin ƙasar tare da taimakon jama'ar yankin sun daƙile harin, tare da yin mummunar ɓarna kan 'yan ta'adda.

    Amma kungiyar al-Shabab ta ce ta ƙwace sansanonin soji biyar tare da kashe sojoji da dama.

    Tun a watan Agustan shekarar 2022 ne dakarun tarayyar Somaliya ke gudanar da wani gagarumin farmaki kan ƙungiyar da ke da alaƙa da al-Qaeda.

  4. Abin da ya sa Hisbah take neman fitattun yan Tiktok shida a Kano

    ..

    Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta tabbatar da sanarwar neman wasu shahararrun masu amfani da shafin Tiktok guda shida saboda furta kalaman batsa cikin wasu bidiyo da suka yi, lamarin da ya ci karo da dokar tabbatar da tarbiyya.

    Shugaban hukumar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya shaida wa BBC cewa cikin masu amfani da shafin da ake nema akwai Abubakar Ibrahim da aka fi sani da Gfresh sai Sadiya Haruna da Ashiru Idris da aka fi sani da Maiwushirya da Ummee Shakira da Murja Ibrahim Kunya da kuma Hassan Makeup.

    A cewar Sheikh Daurawa, suna cigiyar mutanen ne bayan ɓullar wani bidiyo da a ciki suke furta kalaman da ba su dace ba wanda kuma ya ci karo da alkawarin da suka yi lokacin da aka kama su a karon farko domin yi musu wa'azi.

    Ya ce babban burin Hisbah shi ne ta ga an gyara kura-kurai tun da "ba so muke mu ci gaba da gayyato mutanen ba, watakila hakan zai sa su ji cewa ba su kyauta ba tun da an yi yarjejeniya da su, sun yi mana alkawari za su gyara [amma hakan ba ta faru ba]."

    Sheikh Daurawa ya ce kasancewar wannan ne karo na biyu da suke saba dokar ta tarbiyya, ko da sun bayyana a gaban Hisbah, za su sake jan hankalinsu a kan yin irin wadannan dabi'u tare da tabbatar da cewa sun rubuta alkawarin riko da yarjejeniyar da aka yi da su.

    Ya ce sai mutum ya taka doka sau uku sannan ake gurfanar da shi a gaban kotu.

    "Ba kotu za mu kai su ba yanzu, ai yarjejeniya sau uku ake yi, idan suka zo, za mu ce musu ya muka yi yarjejeniya da ku, bayan kun gaya mana ba za ku sake ba kuma kuka sake, sai mu ji uzirinsu." in ji Sheikh Daurawa.

    Shugaban hukumar ta Hisbah ya ce a baya, sun tattauna da jami'ai daga ofishin Tiktok da ke Legas inda kuma suka ce idan aka samu masu amfani da Tiktok da yake saba doka ko jayo tashin hankali ko ɓata addini "idan muka rubuta muka kai musu, suka bayar da rahoto, za a iya toshe [shafinsa]."

    "Wannan ma ya fi yi wa dan Tiktok zafi, ka sa a goge shafinsa domin wani ya tara mabiya da yawa, idan ya ji za a rufe shafinsa saboda gwamnati ta shigo, kuma doka ya karya." in ji Daurawa.

    A shekarar da ta gabata ne hukumar ta Hisbah ta gana da yan Tiktok a Kano domin tattaunawa da su game da yadda za a tabbatar da kyawawan dabi'u tare da kawar da fitsara a shafin.

    • Sadiya Haruna: Tauraruwar ta kammala ɗaurin-talala don 'gyaran tarbiyarta'
    • An tisa ƙeyar Murja Kunya da Ashiru da wasu 'yan TikTok biyu gidan yari
  5. Falasɗinawa sun kai mataki na gaba a gasar cin kofin nahiyar Asiya

    ...

    Asalin hoton, @afcasiancup/X

    Tawagar kwallon kafa ta Falasdinawa ta kai matakin zagaye na gaba a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta nahiyar Asiya a karon farko bayan da ta doke Hong Kong da ci 3-0 a ranar Talata a wasan rukunin C.

    Nasarar, wadda ita ce ta farko da kungiyar ta samu a gasar cin kofin nahiyar Asiya, ta tabbatar da matsayinta a zagayen ƴan 16 a matsayin ɗaya daga cikin ƙungiyoyi huɗu tka rawar gani da suka zo na uku a gasar da ake yi a Qatar.

    Tsohon ɗan wasan gaba Oday Dabbagh shi ne jarumi a filin wasa na Abdullah bin Khalifa da ke Doha lokacin da aka buga karawar, inda ya zura kwallo biyu a raga.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ke yaƙi da Hamas biyo bayan harin da kungiyar ta kai a Gaza a ranar 7 ga Oktoba, wanda ya haifar da ɓarna mai yawa da kuma mummunan halin da al'umma suka faɗa ciki.

  6. Kotun koli za ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Rivers

    ...

    Asalin hoton, TONYE COLE/RIVERS STATE GOVERNMENT

    A yau Laraba ne kotun kolin Najeriya za ta yanke hukunci kan takaddamar da ake yi game da zaben gwamnan jihar Ribas.

    Lamarin dai na tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jam'iyyar PDP da Tonye Cole na jam'iyyar APC.

    A makon da ya gabata ne alƙalai biyar na Kotun Koli karkashin jagorancin Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun suka saurari lauyoyin angarorin biyu.

    Bangarorin sun samu sanarwa daga babbar kotun cewa za a yanke hukuncin a ranar Laraba.

    Cole yana kalubalantar nasarar Gwamna Fubara a zaɓen gwamna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris na 2023 da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar a jihar.

    A sakamakon zaɓen, Fubara ya samu kuri'u 302,614 inda ya doke abokin hamayyarsa, Tonye Cole wanda ya samu kuri'u 95,274.

    Ganin haka ne ɗan takarar jam’iyyar APC ɗin ya ce an tafka maguɗi a zaɓen inda ya kuma ce Fubara bai cancanci tsayawa takarar ba saboda a lokacin yana kan muƙamin Akanta-Janar na jihar Ribas - kuma hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar domin ya kamata ya fara yin murabus kafin tsayawa takara.

    Bayan haka ne Cole ya kai maganar gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna inda ya nemi a tsige Fubara - amma aka yi watsi da ƙarar wanda hakan ya sa ya sake kai karar zuwa kotun ɗaukaka ƙara inda ita ma ta yi watsi da ƙarar tasa.

    Ana sa ran kawo karshen takaddamar a hukuncin da kotun kolin za ta yanke a yau.

    • Ƙuri'un da ba za a iya bayaninsu ba a zaɓen Najeriya mai cike da taƙaddama
    • Me zai faru a jihar Ribas bayan soke ‘yan takara ta APC
  7. Me zai faru idan NNPP da APC suka haɗe a Kano?

  8. Trump ya doke Haley a zaben fitar da gwani na New Hampshire

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Donald Trump ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar Republican a New Hampshire yayin da yake neman tsayawa takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar.

    Sakamakon kusan rabin kuri'un da aka kirga ya ba shi fiye da kashi hamsin da biyar cikin dari, yayin da abokiyar hamayyarsa da ta rage, tsohuwar jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley, ta samu kusan kashi arba'in da uku cikin dari.

    Kuma ta lashi takobin ci gaba da neman takarar.

    Yanzu dai an kirga sama da rabin kur’un zaben fid da gwanin na jihar ta New Hampshire, inda daman kamar yadda aka yi hasashe wanda zai yi nasara, tsohon shugaban Amurkar, Donald Trump yake gaban abokiyar hamayyarsa, guda daya tilo tsohuwar jakadiyar Amurka a majalisar dinkin duniya, Nikki Haley da kusan maki 10.

    Akwai dai wakilai ko delegets, 22 a jihar, inda kafar yada labarai ta CBS, da ke mu’amulla da BBC a Amurkar ta yi hasashen cewa Trump zai samu akalla 12 daga ciki, yayin da Haley za ta samu akalla tara idan ta yi kokari, hakan zai sa Trump ya samu jumulla 32 kenan Haley ta kasance da 17.

    Wanda zai zama gwani a zaben dai dole ne ya kasance ya samu deleget 1,215.

    Zuwa yanzu dai Mista Trump ya kama wannan hanya ba ji ba gani , kuma nasara ce ga tsohon shugaban na Amurka da za ta kara masa karfi na zama dan takarar jam’iyyar Republican a babban zaben kasar a watan Nuwamba.

    Tuni daman ya gabatar da jawabin nasara har sau biyu a cikin kwana 8. Sai dai kalamansa ga taron magoya bayansa a New Hampshire a wannan karon bayan ganin ya kama hanyar nasara sun kasance daban da wadanda ya yi ranar Litinin a Iowa.

    A baya ya nuna muhimmancin hadin kan jam’iyyarsu tare da yaba wa abokan takararsa to amma a wannan karon ya caccaki abokiyar hamayyar tasa ne, Nikki Haley da ta rage, wadda ta yi jawabi ga magoya bayanta jim kadan kafin Trump ya shiga fage ya gabatar da nasa jawabin, inda ya ce tana magana kamar ita ce ta ci zaben.

    Ya ce "dole in gaya muku abin ban sha’awa ne, saboda na ce, kai wannan irin nasara, to amma sai kawai wani ya shigo fagen ya yi kwalliya da kyau, a lokacin ana kan bakwai, to amma yanzu na shigo an ce 14. Amma ita ta shigo a lokacin ana bakwai, to amma dole ne mu yi abin da ya dace ga jam'iyyarmu,

    Ta dage da, tana jawabi, na ce kai, kamar ta yi nasara, ba ta ci ba, ta fadi.

    • Me ya sa Trump ya fi sauran ƴan takarar Republicans farin jini?
    • Trump ya zama shugaban Amurka na farko da aka ɗauki hotonsa a gidan yari
  9. Amurka ta yi alƙawarin haɗa ƙarfi da ƙarfe kan tsaro da Najeriya

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a yammacin Afirka da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da ke ziyarar aiki a ƙasashen Afirka hudu.

    Blinken ya ce Amurka ta kuduri aniyar haɗa ƙarfi da ƙarfe kan tsaro da Najeriya” yayin da ƙasashen biyu ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin.

    Najeriya ta kuma sha fama da tashe-tashen hankula a arewaci da kuma babban birnin tarayya Abuja, inda wasu gungun 'yan bindiga suka addabi al'umma tare da yin garkuwa da jama'a domin neman kuɗin fansa.

    Ƙasashe a yankin Sahel na fuskantar tabarbarewar zaman lafiya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a hudu daga cikin mambobi 15 na ƙungiyar Ecowas.

    Amurka dai na ci gaba da yunƙurin ganin ta ci gaba da yin tasiri a nahiyar Afirka, a daidai lokacin da Rasha da China ke fafatawa.

    • 'Matsalar tsaro ta karu matuka a Najeriya'
    • Antony Blinken ya je China don kyautata alaƙa da Amurka
  10. Assalamu alaikum!

    Jama'a, assalamu alaikum. Barka da safiya. Da fatan muna cikin koshin lafiya.

    Kamar kullum, a yau ma wannan shafi na Kai Tsaye zai kawo rahotanni da labarai na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran kasashe makwabta.

    Sai ku ci gaba da bibiyar mu domin sanin halin da duniya take ciki a yau Laraba.

    Kuna kuma iya lekawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta karin labarai da kallon bidiyo.