'Har yanzu ba a bi wa waɗanda jirgin sojin Najeriya ya yi wa ruwan wuta a Nasarawa hakki ba'
Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
A'isha Babangida, Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin mu a wnnan shafi nan muka kawo ƙarshen labari da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah Allah ya kaimu, za mu sake dawowa domin cigaba da kawu muku sabbin labarai.
A madadin sauran Abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya
UAE ta musanta bai wa mayaƙan RSF makamai
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta musanta cewa tana bai wa mayaƙan RSF tallafin makamai a yaƙin da suke da sojojin Sudan.
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da aka fallasa ya ce ana shigar da makamai gabashin Chadi kowanne mako, domin miƙa su ga mayaƙan RSF.
Wannan ne rahoton baya-baya da ya yi iƙirarin cewa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan tana da hannu a rikicin Sudan, amma hukumomi a Abu Dhabi sun musanta hakan.
Sun ce jirgin da ke sauka a gabashin Chadi, jirgi ne na jigilar kayan agaji.
Gwamnan Ondo ya fara sabbin naɗe-naɗe bayan rusa majalisar zartarwar jihar
Asalin hoton, Aiyedatiwa/X
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya amince da naɗin Tayo Oluwatuyi a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar.
Matakin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan ya fitar ranar Laraba da maraice.
Tun da farko gwamnan ya zaɓi Olayide Owolabi Adelami a matsayin mataimakinsa.
Ana sa ran mista Adelami zai bayyana a gaban majalisar dokokin jihar ranar Alhamis domin tantancewa.
A ranar Laraba ne gwamnan ya rusa duka kwamishohin jihar, da masu taimaka wa gwamna na musamman, da masu bai wa gwamnan shawara, waɗanda tsohon gwamnan marigayi Rotimi Akeredolu ya naɗa, tare da umartarsu su miƙa ragamar ma'aikatunsu ga manyan sakatarorin ma'aikatun.
An rantsar da Lucky Aiyedatiwa, mai shekara 59 a matsayin gwamnan jihar ranar 27 ga watan Disambar bara, bayan mutuwar gwamna Rotimi Akeredolu.
NATO ta ƙaddamar da atisayen soji don daƙile samamen Rasha
Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar tsaro ta NATO ta ƙaddamar da atisayin soji mafi girma tun bayan yaƙin cacar-baka, inda ta tura dubban dakaru don daƙile duk wani yunƙurin samame daga Rasha.
Ƙungiyar ta ce hakan zai nuna haɗin kai, da kuma ƙarfin da take da shi.
Wannan na zuwa ne yayin da ake hasashen cewa Donald Trump zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka, kuma a baya ya sha alwashin cewa Amurka ba za ta kai wa Turai ɗauki ba, idan Rasha ta kai mata hari.
An ƙaddamar da atisayin ne a Virginia, inda aka sallami dakarun Amurka da jiragen ruwanta.
Kotun Duniya za ta yanke hukunci kan ƙarar kisan ƙare-dangi da ake yi wa Isra'ila
Asalin hoton, Getty Images
A ranar Juma'a alƙalan Kotun Duniya (ICJ) za su yanke hukunci kan ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar da Isra'ila tana zarginta da aikata kisan ƙare-dangi a Gaza.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce cikin wata sanarwa da kotun ta fitar ranar Laraba, ta ce tawagar alƙalan 17 za su yanke hukunci kan ƙarar ranar Juma'a 26 ga watan Janairu da misalan ƙarfe 12:00 na rana agogon GMT.
A farkon wannan watan ne kotun ta saurari ƙarar cikin kwanaki biyu.
Afirka ta Kudu ta buƙaci kotun ta tilasta wa Isra'ila gaggauta dakatar da Isra'ila daga hare-haren da take yi wa yankunan Falasɗinawa.
Isra'ila ta musanta zargin da cewa an ''jirkita gaskiya'', sannan ta ce tana da damar kare kanta sannan mayaƙan Hamas take kai wa hare-hare ba fararen hula ba.
A hukuncin na ranar Juma'ar, kotun duniyar ba za ta duba ko Isra'ila ta aikata kisan ƙare-dangi ba.
A maimakon haka kotun za ta duba yiwuwar ɗaukar matakan gaggawa, da za su hana rikicin ci gaba da ƙazanta, a yayin da kotun za ta ci gaba da sauraron ƙara har na tsawon shekaru.
Idan kotun ta yanke hukuncin gaggauta dakatar da yaƙin, to ba dole ba ne Isra'ila ta yi biyayya ga hukuncin, wanda shi ne babban burin Afirka ta Kudu.
A ƙa'ida dole ne a yi biyyya ga hukuncin kotun, ba tare da ɗaukaka ƙara ba, to sai dai kotun ba ta da hurumin tilasta biyayya ga hukuncin da ta yi.
An faɗa wa kotu jami'an gwamnatin Isra'ila na goyon bayan a ruguza Gaza
Yaƙin Gaza : Afirka ta Kudu ta kai ƙarar Isra'ila Kotun Duniya
Iraƙi ta gaya wa Amurka ta janye dakarunta daga ƙasar
Gwamnatin Iraƙi ta zargi Amurka da dagula lamurra a ƙasar, bayan wasu dakarun Amurka suka kai hare-hare kan wata ƙungiya a ƙasar da ke samun goyon bayan Iran.
Mai magana da yawun firaministan ƙasar ya bayyana hare-haren yunuri ne na tayar da zaune-tsaye a ƙasar.
Ministan harkokin tsaron ƙasar, Lloyd Austin, ya ce an kai hare-haren ne a wurare uku na ƙasar.
Gwamnatin Iraƙi ta sha kiran Amurka ta janye dakarunta 2,500 daga ƙasar.
Putin ya ce Mahamat Deby ya 'daidaita' Chadi
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ya yaba da shugaban mulkin sojin Chadi, Mahamat Idrs Deby saboda yadda ya ''daidaita ƙasar'' bayan ya karɓi ragamarta shekara uku da suka gabata.
Shugabannin biyu sun gana a birnin Moscow ranar Laraba bayan ziyara da shugaban Chadin ya kai Rasha
Mista Deby ya karɓe ragamar jagorancin ƙasar ne bayan da 'yan tawayen ƙasar suka kashe mahaifinsa a shekara 2021.
Shugaban ya kuma alƙawarta gudanar da zaɓe cikin wata 18 a ƙasar domin mayar da ita kan turbar dimokraɗiyya, to sai dai ya jinkirta hakan zuwa watan Oktoban shekarar da muke ciki.
A watan Disambar bara ne aka gudanar da ƙuri'ar raba gardama domin samar da sabon kundin tsarin mulki, wani mataki da masu suka ke ganin tamkar ƙara da Mista Deby ƙarfin iko ne.
Hukumomin da suka shirya ƙuri'ar sun ce kusan kashi 86 na waɗanda suka kaɗa ƙuri'ar sun goyi bayan sabon kundin tsarin mulkin.
A baya-bayan nan Rasha na ƙoƙarin ƙulla alaƙa da ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar, waɗanda dukkansu yanzu ke ƙarƙashin mulkin soji, kuma suka yanke alaƙa da tsohuwar uwargijiyarsu Faransa.
Uganda na shirin bai wa kamfanin UAE aikin gina matatar man fetur
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Uganda na tattaunawa da wani kamfanin zuba jari wanda ɗan gidan sarautar Dubai ke jagoranta kan gina matatar man fetur mai ƙimar dala biliyan 4.
Ministar cigaban makamashi da ma'adanai Ruth Nankabirwa, ta shaida wa BBC cewa Uganda ta zaɓi kamfanin mai suna Alpha MBM Investment LLC na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa daga jerin kamfanoni biyar da suka nemi kwangilar.
Ana tsammanin ɓangarori biyun su kammala cimma yarjejeniya cikin wata uku.
"Muna fatan ba za su ɓata lokaci wajen neman kuɗi ba saboda sun nuna mana cewa abu ne mai sauƙi samun kuɗi da kayan fasahar da muke buƙata da zai taimaka mana wajen tace ɗanyan man da muke da shi tare da lura da dacewar wurin da za'a kafa matatar " a cewar Ms Nankabirwa.
Ministar ta shaida wa Newsday cewa za a samar da matakan kula da kuma rage illar matatar ga muhalli.
Gwamnatin ta ce matatar man za ta taimakawa Uganda wajen sarrafa ɗanyan man da suke da shi a kasuwance.
Ana sa ran ƙasar ta fara kasuwancin ɗanyen man nata nan da shekarar 2025.
Wata baƙuwar cutar ido ta ɓulla a Kenya
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin lafiya a Kenya na bincike kan barkewar wata kwayar cutar ido a yankin.
Kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa an fi samun rahoton bullar cutar a cikin yankunan Mombasa da Kilifi.
An shawarci mazauna yankunan da su tsaftace kansu ta hanyar wanke hannu da gujewa amfani da kayan mutane da yawa suka yi amfani da su da kuma gujewa taɓa idanunsu.
A makon da ya gabata, hukumomin kiwon lafiya a Tanzania sun ba da sanarwar bayan samun rahoton mutum 869 da suka kamu da cutar a cikin wata guda, akasari a birnin kasuwanci na Dar es Salaam.
Ciwon idon, wanda ake kira da cutar jajayen ido, wani kumburi ne na fatar ido.
Alamunsa sun haɗa da ido ya yi ja, ko ya kumbura ko yari riƙa kaikayi da kuma zubar da hawaye.
Cikin hotunan: Zanga-zanagr 'yan adawa a Tanzania
Babbar jam'iyyar adawa a Tanzania Chadema ta gudanar da zanga-zanga inda take sukar kudurin gwamnatin ƙasar da wata dokar zabe, ga matsalar tsadar rayuwa da kuma jan ƙafa wajen kawo sauye-sauye a tsarin mulkin ƙasar.
'Yan sanda sun bai wa masu zanga-zangar damar gudanar da taronsu a babban birnin kasuwancin ƙasar Dar Salaam, sai dai sun ja kunne kar a tashi hankali ko kuma a zyga mutane su yi barna.
Ga hotunan yadda aka gudanar da zanga-zangar.
Zakuna sun kashe shugabansu bayan sun yi masa tawaye
Ɗan Tanzania da aka kashe a Ukraine wajen yi wa Rasha yaƙi
Ana taron masu ruwa da tsaki kan matsalar tsaro a arewacin Najeriya
Asalin hoton, Ministry of Defence
Gamayyar ƙungiyoyin Arewacin Najeriya sun shirya wani taron masu ruwa da tsaki kan matsalar tsaro da yankin arewacin ƙasar ke fuskanta.
Taron na kwana biyu - wanda aka shirya ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Janar Abdussalami Abubakar mai ritaya - ya samu halartar manyan masu faɗa a ji daga yankin arewacin ƙasar.
Asalin hoton, Ministry of Defence
Daga cikin waɗanda suka halarci taron har da sarkin musulmin Najeriya mai alfarma Dakta Sa'adu Abubakar lll da gwamnonin jihohin Gombe da Kaduna da Zamfara Da Katsina da Bauchi da kuma Nasarawa.
Sauran manyan baƙin sun haɗar ministocin Tsaron ƙasar, Mohammad Badaru Abubakar da Mohammed Belo Matawalle, da babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasar, Janar C.G Musa da tsohon shugaban majalisar dattawan ƙasar Dakta Abubakar Bukola Saraki, da tsohon gwamnan Katsina Aminu Bello Masari, da ministan Ayyukan gona da samar da abinci da shugaban ƙungiyar Kiristoci ta CAN, da tsohon shugaban hukumar zaɓen ƙasar Farfesa Attiru Jega.
An shirya taron ne da nufin lalubo hanyoyin magance matsalolin tsaro da yankin ke fuskanta.
Yankin arewacin Najeriya dai ya daɗe yana fama da matsalolin tsaro kama daga na masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da 'yan fashin daji da 'yan tayar da ƙayar bayan Boko Haram.
Ƙungiyoyin Fararen hula na nuna adawa da ziyarar Ecowas a Nijar
Yan farar hula a jamhuriyar Nijar sun fara zaman dirshan a kan hanyoyin da tawagar Ecowas ko Cedeao za ta wuce don kai ziyara birnin Yamai.
Tawagar ta Ecowas za ta kai ziyara ƙasar a Nijar ɗin ne a ƙoƙarin neman sassanta rikicin siyasa da ƙasar ta tsunduma tun juyin mulkin ranar 26 ga watan yulin 2023.
A baya dai ƙungiyar Ecowas ta sanya wa ƙasar jerin takunkuman karya tattalin arziki don nuna adawarta da juyin mulkin soji da aka yi a ƙasar.
Ecowas dai ta buƙaci sojojin su gaggauta mayar da hamaɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazaoum kan karagar mulki, ko su fuskanci matakin soji daga ƙungiyar.
Ana gudanar da zaman dirshan ɗin ne a wurare daban-daban har guda uku a Yamai, babban birnin ƙasar
An kashe gomman mayaƙan Boko Haram a Nijar - Sojoji
Asalin hoton, BB
Sojojin Mulkin Nijar sun ce gomman mayaƙa masu iƙirarin jihadi ne aka kashe yayin da aka jikkata sojoji masu yawa a lokacin wani gumurzu tsakanin ɓangarorin biyu a yankin Diffa da ke kusa da tafkin Chadi.
Kamfanin dillancin labari na AFP, ya ambato wata sanarwa da gwamnatin sojin ƙasar ta fitar da ke cewa mayaƙan Boko Haram ɗin ne suka kai wa sojojin da ke filin jirgin yanki da ke kusa da kan iyakar ƙasar da Najeriya.
Sanarwar ta ce sojojin saman ƙasar ne suka kai wa mayakan hari a lokacin da suke cikin kwale-kwale a yunƙurinsu na tsallake teku.
Kawo yanzu dai ba a iya tantance haƙiƙanin abin da ya faru ba. Yankin Diffa dai yanki ne da ke ɗauke da dubban 'yan gudun hijirar da Boko Haram ya raba da muhallansu daga Najeriya.
Mai masaukin baƙi a gasar Afcon Ivory Coast ta kori kocinta
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon ƙafa ta Ivory Coast da ke karbar baƙuncin gasar 2023,FIF ta sanar da korar kocin ƙasar lokacin da ake tsaka da gudanar da wasannin gasar Afcon.
"An kawo ƙarshen kwantaragin koci ean-Louis Gasset da mataimakinsa Ghislain Printant saboda ba sa kawo sakamakon mai kyau," in ji sanarwar FIF.
An yi wa tawagar dukan kawo wuƙa inda Equatorial Guinea ta doke ta da ci 4-0 a wasan ƙarshe na rukunin A a ranar Litinin.
Ba shi ne koci na farko da aka kora ba ana tsaka da gasar - Ghana ma ta kori nata kocin a ranar Talata, Tanzaniya ma ta kori Adel Amrouche a matsayin kocinta.
Shi kuwa kocin Gambia Tom Saintfiet ajiye aikinsa ya yi bayan cire ƙasar da aka yi a matakin rukuni.
Batun mayar da birnin tarayya zuwa Legas ba gaskiya ba ne - Fadar shugaban Najeriya
Asalin hoton, fb/Bola Tinubu
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Mai bai wa shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya ce shugaban kasar ba shi da aniyar ɗauke babban birnin tarayyar ƙasar daga Abuja zuwa Legas.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ranar Laraba, Onanuga ya ce masu yada jita-jita ne ke yaɗa maganar domin jan hankalin al'umma gare su.
Wannan na zuwa ne bayan matakin da gwamnatin tarayyar ƙasar ta ɗauka na mayar da wasu ɓangarori na Babban bankin Najeriya da kuma Hukumar kula da filayen jiragen sama na ƙasar zuwa Legas, daga Abuja.
Lamarin da ya janyo ƙorafi da kiraye-kiraye daga wasu ƙungiyoyi na wasu ɓangarorin ƙasar, inda suka yi zargin cewa tamkar wani mataki ne aiwatar da wata 'manufa ta daban.'
Onanuga ya ce matakin mayar da wani sashi na ma'aikatar FAAN bai kamata ya ja hankalin mutane da yawa ba saboda jihar Legas ita ce cibiyar kasuwanci kuma cibiyar sufurin jiragen sama a Najeriya saboda haka ya ce har yanzu FAAN za ta ci gaba da kasancewa a Abuja.
"Akwai ma'aikatu da yawa da ba a Abuja suke ba dangane da aikinsu kamar NIMASA da take Legas. Haka kuma NPA da kuma hukumar kula da sufurin ruwa (NIWA) da ke Lokoja.'
Sanarwar dai ta ƙara da cewa bai kamata a siyasantar da lamurran gwamnati ba.
Tinubu ya tafi Faransa
Asalin hoton, PRESIDENCY
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bar Abuja yau Laraba zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa.
A cikin wata sanarwa da ta fito daga hannun mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale, Tinubu zai yi tafiyar ce ta ƙashin-kansa.
Haka nan sanarwar ta ƙara da cewa ana sa ran shugaban na Najeriya zai koma gida a makon farko na watan Fabarairu.
A makon da ya gabata ne dai wasu rahotonni a Najeriya suka ce shugaba Tinubu ya kashe naira biliyan 3.4 a kan tafiye-tafiyen ciki da wajen ƙasar a cikin watanni shida na farkon mulkinsa.
Hakan na nufin Shugaba Tinubu da jami'an gwamnatinsa sun zarce kasafin kuɗin naira biliyan 2.49 da aka ware wa tafiye-tafiyensu a 2023 da kashi 36, kamar yadda jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito.
Punch ta ce duk da yake shugaban ya gaji kasafin kuɗin ne na rabin ƙarshen shekarar 2023, "ya kashe sama da abin da aka ware a gaba-ɗaya shekarar daga watan Yuni zuwa Disamban 2023".
Rahoton wanda BBC ba ta tabbatar ba, ya zo ne kusan mako ɗaya bayan da Shugaba Tinubu ya zaftare yawan jami'ai da za a bari suna yi masa rakiya yayin tafiye-tafiyensa da kuma na sauran manyan jami'an gwamnatinsa zuwa ƙasashen waje da kuma a cikin gida.
Kafin haka, an soki lamirin shugaban kan makudan kuɗaɗen da yake kashewa wajen tafiye-tafiye waɗanda ƴan Najeriya suke ganin sun yi yawa.
Ɗaya daga cikin tafiye-tafiyen ita ce, wadda gwamnatin Tinubu ta ɗauki nauyin jami'ai sama da 400 domin zuwa taron sauyin yanayi na COP28 da aka a yi Dubai, inda aka yi ta sukarsa.
Jirgin yaƙin Rasha ya yi hatsari a yankin Belgorod
Asalin hoton, RUSSIAN TELEGRAM
Jirgin yaƙin kasar Rasha Ilyushin-76 ya yi hatsari a kudancin yankin Belgorod mai iyaka da kasar Ukraine.
Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce sojojin Ukraine 65 da aka kama suna cikin jirgin da ke kan hanyarsa ta zuwa yankin Belgorod don musayar fursunoni.
Babu wani bayani da ke kewaye da waɗanda ke cikin jirgin da za a iya tabbatarwa
Kamfanin dillancin labarai na Ria Novosti ya ce wasu mutane tara na cikin jirgin da suka hada da ma'aikata shida.
Babban hafsan sojin Ukraine, wanda shafin intanet na Ukrainska Pravda ya ruwaito, ya ce jirgin na jigilar makamai masu linzami na na'urorin tsaron iska na Rasha S-300.Bai ambaci fursunonin yaƙi ba.
Bidiyon da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna wani jirgin sama yana fadowa sai kuma fashewar wani abu da gobara ya biyo baya a kusa da kauyen Yablonovo, mai tazarar kilomita 70 daga arewa maso gabashin birnin Belgorod, da misalin karfe 11:00 na agogon kasar.
Gwamnan yankin Belgorod na ƙasar Rasha Vyacheslav Gladkov ya ce jirgin ya fado ne a wani fili da ke kusa da wani wurin zama kuma duk wanda ke cikin jirgin ya mutu.
Ya kuma ce dukkanin fasinjojin da ke cikin jirgin sojin da ya yi hadari sun mutu, inji gwamnan yankin Vyacheslav Gladkov.
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha dai ta ce Ukraine ce ta kakkabo jirgin saman soji da ya yi hatsarin, inda ta bayyana hakan a matsayin "rashin imani" kamar yadda kamfanin dillancin labarai na TASS ya ruwaito.
Har yanzu BBC ba ta iya tantance waɗanda ke cikin jirgin ba, ko kuma abin da ya yi sanadin hatsarin jirgin.
Amurka ta kai hari kan mayaƙan da ke samun goyon bayan Iran a Iraƙi
Amurka ta ce dakarunta sun kai hare-hare a Iraki kan wasu wurare uku da mayakan da ke samun goyon bayan Iran ke amfani da su.
Sakataran tsaro na Amurka Lloyd Austin yace hare-haren da aka kai a jere an kai su ne a kan "ƙungiyar sa kai ta Kataib Hezbollah da wasu ƙungiyoyi masu alaƙa da Iran".
Ya ce hare-haren da aka kai martani ne kan farmakin da aka kai wa Amurka da ƙawayenta a Iraƙi da Syria.
Sai dai wani babban jami'i a Iraƙi yace hare-haren cin zarafi ne ga Iraƙi a matsayinta na ƙasa mai ƴanci.
Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na Iraki Qassem al-Aaraji ya kara da cewa harin da Amurka ta kai bai taimaka wajen kawo kwanciyar hankali ba
A rubutun da yayi a shafinsa na X wanda aka fi sani da twitter, ya ce " "Ya kamata Amurka ta kara matsa lamba don dakatar da hare-haren da Isra'ila ke yi a Gaza maimakon kai hari da kuma jefa bama-bamai a sansanonin wata kungiyar kasar Iraki".
Yana magana ne game da kawancen tsoffin kungiyoyin tsaro masu samun goyon bayan Iran, Hashed al-Shaabi wanda a halin yanzu aka haɗe su cikin dakarun tsaron ƙasar.
A makon da ya gabata ne wasu sojojin Amurka da dama suka jikkata sakamakon harin makami mai linzami da aka kai a sansanin sojin sama a yammacin Iraki.
Jami'an Amurka sun ce "ana gudanar da bincike kan raunin da suka samu a kwakwalwa".
Kalli bidiyon sabon wurin bautar Hindu da aka gina kan filin masallaci
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Firaministan Indiya, Narendra Modi ya ƙaddamar da wurin bauta na ubangijin mabiya addinin Hindu, Ram a birnin Ayodhya.
Wurin bautar ya maye gurbin wani masallaci da aka gina a ƙarni na 16, wanda mabiya addinin Hindu suka ƙona a 1992.
Yawancin masu adawa da gwamnatin Modi ba su halarci bikin buɗewar ba, suna zargin cewa firaministan na amfani da addini domin cin gajiyar siyasa.
Kalli bidiyon domin samun bayani kan abin da ya sa ake ce-ce-ku-ce kan wurin bautar.
'Har yau ba a bi wa waɗanda jirgin sojin Najeriya ya kashe a Nasarawa haƙƙinsu ba'
Asalin hoton, EPA
Shekara ɗaya bayan wani mummunan harin da jirgin saman sojin Najeriya ya kai a garin Rukubi na jihar Nasarawa da ya yi sanadin mutuwar mutane 40, waɗanda abin ya shafa da iyalansu har yanzu na jiran a yi musu adalci.
Shugaban ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi, ya ce hukumomin ƙasar sun gaza wajen tabbatar da adalci da kuma bin diddigin harin da aka kai.
Sanusi ya soki yadda ake amfani da hare-hare ta sama wajen tabbatar da doka da oda, yana mai cewa hakan ya saɓa wa doka, haramun ne da kuma yin amfani da karfi ne fiye da kima, yana mai jaddada cewa tamkar tsawaita rashin adalci ne ga iyalan waɗanda abin ya shafa.
"Rashin hukunta sojojin da ke da alhakin kai irin wannan harin kan fararen hula na nuna rashin mutunta rayuwar ɗan'adam da kuma ƙara ƙarfafa gwiwar kai irin wannan harin nan gaba tare da kuma ƙara jefa mutanen da ke zaune a yankunan karkara, waɗanda ke fama da tashe-tashen hakula cikin hatsari mai girma." in ji shi.
"Hare-haren jiragen sama tare da yawaitar kashe-kashen mutane ba bisa ƙa'ida ba sun zama daya daga cikin jerin manyan laifukan take haƙƙin bil'adama na baya-baya nan da sojojin Najeriya ke yi."
"Dole ne mahukuntan Najeriya su bai wa sojoji umarni da su rika bai wa rayuwar fararen hula fifiko da muhimanci da kuma mutunta hakkin dan'adam a koda yaushe yayin gudanar da dukkan ayyukan tsaro. Dole ne gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gudanar da bincike mai zaman kansa, ba tare da nuna son kai ba, kuma mai inganci, kan harin da aka kai wa Rukubi ta sama, da ma wasu da dama da suka haddasa kashe-kashe ba bisa ka’ida ba.
"Ya kamata a gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a gaban shari’a ta hanyar shari’a ta gaskiya, ciki har da wadanda ke da alhakin daidaikun mutane da na sojoji da manyan kwamandojin sojoji.”
Hare-haren jiragen yaƙin Najeriya bisa kuskure takwas a kan fararen hula
Amnesty ta caccaki Najeriya kan kasa kawo ƙarshen hare-haren ƴan bindiga