Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Habiba Adamu, Awwal Ahmad Janyau and Ahmad Tijjani Bawage
Gwamnatin Filato ta sa dokar hana fita a karamar hukumar Mangu
Asalin hoton, GOVERNOR PLATEAU STATE/FACEBOOK
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ayyana dokar hana fita - daga safe zuwa dare a karamar hukumar Mangu.
Dokar za ta soma aiki nan take.
Matakin na kunshe cikin sanarwar da daraktan yada labarai da harkokin al'umma na jihar, Gyang Bere ya sanyawa hannu.
Ya ce an dauki matakin ne saboda tabarbarewar harkokin tsaro a yankin.
Sanarwar ta kara da cewa "gwamna Mutfwang ya dauki matakin bayan tuntuba da hukumomin tsaro."
Matsalar tsaro na ci gaba da karuwa a jihar ta Filato. Ko a baya-bayan nan an kai wasu jerin hare-hare da suka yi sanadin mutuwar fiye da mutum 100 da jikkatar wasu da dama. An kuma kona wasu gidaje.
Bidiyon manyan fashewar da aka shafe dare ana ji a babban birnin Yemen
An shafe dare ana jin rugugin manyan fashewa a Sanaa, babban birnin Yemen yayin da Amurka da Birtaniya suka kai hare-hare kan cibiyoyin mayakan Houthi.
An kama yan Najeriya biyu kan zargin hannu a kisan dalibar Kenya
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun kira zanga-zangar gama-gari game da cin zarafin da ake yi wa mata
Yan sandan Kenya sun kama wasu maza biyu yan Najeriya saboda zargin suna da hannu a kisan wata daliba.
Sun bayyana gaban kotu sai dai ba a kai ga tuhumarsu ba.
An gano gawar daliba Rita Wdaeni mai shekara 20 cikin ladejin shara a wani gida da ke Nairobi babban birnin Kenya ranar 14 ga watan Janairu.
Kisan gillar da aka yi wa dalibar dai ya fusata al'ummar Kenya.
Sai dai kokon kanta tare da wayarta da sauran kayayyakinta, sun bata.
Kisan gillar ya sa an yi ta kiraye-kiraye a kara daukan mataki domin magance cin zarafin da ake yi wa mata.
Wasu yan Kenya hudu suma suna tsare game da kisan da kuma wani mutum wanda yake tafiye-tafiye da takardar fasfon Mozambique inda kuma aka damke shi yayin da yake shirin barin kasar.
Yan sanda sun bayyana sunayen mutanen biyu da ake zargi da William Ovie Opia da Johnbull Asbor.
Mr Opia yana da fasfon Najeriya wanda wa'adin amfaninsa ya cika kuma Mr Asbor ya rasa nasa fasfon shekaru biyu da suka gabata, kamar yadda yan sanda suka ce.
Yan sanda sun kwace kayayyaki da dama daga gidan mutanen da ake zargi ciki har da wuka da karamar adda da ake zargin sun yi amfani da su wajen kashe dalibar jami'ar tare da sauya mata kamanni, kamar yadda kafofin yada labaran Kenya suka rawaito yan sanda da cewa.
Mr Opia ya fada wa masu bincike cewa ya sayi addar ta intanet domin kare kansa, in ji jaridar Nation mai zaman kanta.
An kama mutanen biyu a Ndenderu, wani gari kai nisan kilomita 20 daga Nairobi kuma kusa da wata madatsa inda yan sanda suka gano kokon kan da ake zargi na Ms Waeni ne tare da wayoyinta da wasu kayayyakinta da suka bata.
Zuwa yanzu dai iyalin Ms Waeni basu kai ga tantance ko kan nata bane.
Iyalanta, a makon da ya wuce, sun ce wadanda ke da hannu a aika-aikar sun bukaci a biya su 500,000 a kudin Kenya kafin su saki Ms Waeni duk da cewa sun halaka ta.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama da kungiyoyin kare hakkin mata sun shirya zanga-zanga a fadin kasar domin nuna fushinsu kan karuwar kisan mata da cin zarafin da ake masu.
An samu karuwar rahotannin kisan mata tun farkon wannan shekarar. Wani bincike da aka yi a 2022 ya gano cewa akalla kashi 34 cikin 100 na mata sun fuskanci cin zarafi a wasu lokuta na rayuwarsu.
Gwamnatin Taraba ta haramta amfani da babura a Jalingo
Gwamnatin jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya ta haramta amfani da kowane irin babur cikin Jalingo, babban birnin jihar tare da takaita zirga-zirgar babura masu kafa uku daga karfe 6 na safe zuwa 8 na dare.
A cewar gwamnatin jihar an dauki matakin ne saboda karuwar ayyukan masu laifi a birnin na Jalingo.
An kuma dauki matakin ne bayan kafa wani kwamitin kar ta kwana game da haramta amfani da babura da takaita zirga-zirgar babura masu kafa uku.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa sakataren gwamnatin jihar ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
Kwamitin wanda mataimakin gwamnan jihar minu Alkali ya kafa a madadin gwamnan ya kunshi kwamishinan yan sandan jihar ta Taraba, Joseph Eribo a matsayin shugaba.
Rashin tsaro matsala ce da ke addabar jihohi da dama a Najeriya abin da masana ke cewa matakan da gwamnati ke dauka na magance matsalolin ba su yi tasiri ba inda suke kira da a kara kaimi domin kawo karshen matsalolin.
Wasu Jiragen da aka yi amfani da su a kai wa mayakan Houthi harin hadin gwiwa
Ma'aikatar tsaro ta Birtaniya ta saki wasu hotunan jiragen yakin soji da aka yi amfani da su wajen afka wa mayakan Houthi cikin harin da aka shafe dare ana yi.
Jiragen yakin sun tashi daga sansanin sojoji na RAF Akrotiri da ke Cyprus.
Asalin hoton, PA Media
Asalin hoton, PA Media
Asalin hoton, PA Media
Babu tawagar da ta fi Super Eagles ƙarfi a gasar AFCON 2023 - Zaidu
Ɗan wasan Najeriya, Zaidu Sanusi ya ce babu wata tawagar da ta fi Super Eagles ƙarfi a Gasar AFCON, bayan da Najeriya ta samu damar zuwa zagaye na biyu na gasar ta bana.
A jiya ne Najeriya ta doke Guinea-Bissau da ci ɗaya mai ban haushi, a nasarar da ta bai wa tawagar ƴan ƙwallon Najeriya damar tsallakewa zuwa zagaye na gaba.
Sai dai a cikin wasa uku Najeriya ƙwallo uku kacal ta iya zurawa a ragar abokan hamayyarta.
A zagaye na gaba Najeriyar za ta kara ne da duk ƙasar da ta zo ta biyu a Rukunin C, wato rukunin da ya ƙunshi Senegal, Kamaru, Gambia da Guinea.
Shirin rage raɗaɗi ba zai yi maganin talauci ba a Najeriya – Masana
Asalin hoton, ISMAILA UBA MISILLI/FACEBOOK
'Yan Najeriya har yanzu suna fama da matsin rayuwa a lokacin da suke kokarin neman abin rufin asiri, yayin da suke fuskantar tsadar kayan abinci da hauhawar farashi.
Hakan na zuwa ne wata biyar bayan gwamnatin kasar ta fitar da kuɗi har naira biliyan 72 domin shirin rage raɗaɗi, sakamakon matsin rayuwar da aka shiga bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun bara.
Wani kwararre kan al'amuran ci gaban duniya, Dr Hussaini Abdu ya yi wa BBC bayani kan dalilin da ya sa shirin rage radadin bai cimma buri ba.
A cewar sa tallafi ba ya magani kai tsaye musamman kan abin da ya shafi tattalin arziki saboda "ana yi ne domin a cikin takaitaccen lokaci a rage nauyi, kafin ka farfado ka nemi abin yi."
Kwararren ya ce mafi yawan al'umma sun ce an raba kayan tallafi amma ba su gani a kasa ba dalilin da ya sa ya ce ya kamata a ce an dauki lokaci ana aiwatar da tsarin tare da ware adadin da za a rika bai wa mutane.
Dr Abdu ya soki tsarin da aka bi wajen yin rabon kayan tallafin da ya ce irin tsarin ba ya "taɓa maganin talauci a ko ina."
"Abu ne aka yi ba kan tsari ba, saboda haka ba yadda za a yi a ce ya yi maganin irin wannan abun." in ji Dr Abdu.
Ya kara da cewa har yanzu akwai jihohin da ko "ƙwandala" ba su gani ba duk da iƙirarin gwamnati cewa ta fitar da kuɗaɗe ga jihohi domin rage raɗaɗin da al'umominsu ke fuskanta.
Bayanan sautiLatsa alamar sama domin sauraron fahimtar masana kan shirin rage radadin talauci a Najeriya
An kashe sojojin Isra'ila 24 a Gaza lokaci guda
Asalin hoton, AFP
Isra'ila ta ce an kashe sojojinta 24 a Gaza - wannan ce rana mafi muni ga sojojin na Isra'ila tun bayan da ƙasar ta ƙaddamar da gagarumin samame a Gaza.
Babban mai magana da yawun rundunar tsaron Isra'ila (IDF), Daniel Hagari ya ce ana kyautata zaton wata roka ce da aka harba ta faɗa kan wani tanki da ke kusa da wasu gine-gine biyu da sojojin ke ciki.
Rundunar sojin ta Isra'ila ta ce tana yin bincike domin tabbatar da yadda lamarin ya faru.
Mista Hagari ya ce lamarin ya faru ne ranar Litinin da yamma a tsakiyar yankin Gaza, kusa da garin Kissufim ta ɓangaren bakin iyaka.
Ya bayyana cewa lamarin ya rutsa ne da sojojin ko-ta-kwana na Isra'ila waɗanda ke aikin kare mazauna yankin kudancin Isra'ila da ke ƙoƙarin komawa gidajensu, bayan harin da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda ya tursasa wa dubban mutane tserewa daga gidajensu.
Shugaban ƙasar Isra'ila, Isaac Herzog ya rubuta a shafinsa na X, cewa "wannan safiya ce mai muni" bayan sanin yawan sojojin da suka rasa ransu.
Ya ƙara da cewa "Ina jajanta wa iyalan duk waɗanda lamarin ya rutsa da su, a madadin ɗaukacin al'ummar ƙasa."
Isra'ila dai ta ƙaddamar da hari a Gaza ne da nufin kawar da Hamas bayan da mayaƙanta suka kashe mutane 1,300 - mafi yawancinsu fararen hula - sannan suka yi garkuwa da kimanin mutum 240.
Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce aƙalla mutum 25,295 - mafi yawancinsu mata da yara ne aka kashe tun bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da hari a Gaza.
Blinken ya fara rangadin wasu ƙasashen Afrika
Asalin hoton, Reuters
Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya fara rangadin wasu ƙasashe hudu na Afrika, inda ya fara yada zango a Cape Verde.
Blinken ya yabawa tsibirin ƙasar da cewa "fitila ce mai hasken gaske ta ɓangaren zaman lafiya a yankin, a lokacin da muke fuskantar namu ƙalubalen da rashin kwanciyar hankali"
Shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden ya wasa kambun Blinken kan nahiyar Afrika, a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙasashen Afrikan a taron ƙoli na 2022.
Kuma a nan ne shugaban ya ɗauki alkawarin kai ziyara nahiyar a shekarar 2023, sai dai hakan bai yiwu ba.
A watan Maris ɗin shekarar da ta wuce ne Blinken ya kawo ziyara nahiyar, kuma a yanzu yana fama da batun rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.
Amma a yayin da yake magana da mutane a tsibirin Cape Verde, ya ambato shugaba Biden na cewa, "Idan ana maganar Afrika ne to duk ta shafe mu" kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
"Makomarmu na tare, bunƙasarmu na haɗe kuma muryar ƴan Afrika na ƙara saiti wajen jagorantar abubuwan da suka shafi duniya. Inji Bliken.
Australiya ta kakaba manyan takunkumai kan dan Rasha saboda zargin kutse
Asalin hoton, DFAT
Australia ta kakaba wa wani dan kasar Rasha takunkumin da ba a taba ganin irinsa ba bisa zarginsa da hannu a aikata laifin keta bayanan sirri mafi muni a kasar.
Gwamnati ta ce Aleksandr Ermakov ya yi kutse a asusun bayanan mutane kusan miliyan 10 a kamfanin kiwon lafiya ta Medibank, a shekarar 2022.
Yawancin bayanan da aka sace, da suka hada da sunaye, da ranakun haihuwa, da tarihin kiwon lafiya, an sayar da su ne a kasuwar bayan fage na Intanet.
Firaministan Australiya, Anthony Albanese, yana cikin wadanda kutsen ya shafa.
Amurka da Birtaniya sun kai farmakin hadin gwiwa kan mayakan Houthi
Amurka da Birtaniya sun sake kai wasu jerin hare-hare na hadin gwiwa a kan mayakan Houthi a Yemen.
Kasashen biyu sun ce sun kai hare-haren ne a kan wuraren ayyukan soji, a matsayin martani ga hare-haren da 'yan Houthin masu samun goyon bayan Iran ke kai wa a kan jiragen ruwa na kauwanci a tekun Maliya.
Wannan shi ne hari na biyu na hadin gwiwa da Amurka da Birtaniya suka tsara tare da kuma kaiwa a kan wuraren ‘yan Houthi a kasar ta Yemen.
Harin ya kasance mafi girma a kan na farko, da nufin kara kassara karfin ‘yan Houthin na kai hare-hare.
Jiragen sama na yaki da dama ne da suka tashi daga kan wani katafaren jirgin ruwa na dakon jiragen yakin suka kai harin a tsakiyar dare.
Ma’aikatar tsaro ta Amurka Pentagon ta ce an yi nasarar kai harin a wurare takwas na ‘yan Houthi, ciki har da wata ma’ajiyar makamai ta karkashin kasa, da wuraren da ke da alaka da makamai masu linzami da kayayyakin leken asiri ta sama da na kai hari na mayakan.
Rahotanni daga Yemen na cewa an ji manya-manyan fashewa a babban birnin kasar, Sanaa, wanda ke hannun ‘yan Houthin, da ke samun goyon bayan Iran.
Wannan dai shi ne mataki na baya-bayan nan a kan mayakan na Houthi, da ke kai hari a kan jiragen ruwan kasuwanci a tekun Maliya, harin da suke cewa suna kai wa ne a matsayin martanin yakin da Isra’ila ke yi a Gaza da Hamas.
Shugaban Amurka Joe Biden da Firaministan Birtaniya Rishi Sunak sun tattauna kan batun ta waya.
Fadar gwamnatin Amurka, White House, ta ce shugabannin biyu sun jaddada kudurinsu na tabbatar da abin da suka kira ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma kare masu safarar ruwan daga duk wasu hare-hare.
A wata sanarwa ta daban da Ma’aikatar tsaron Birtaniya ta fitar dangane da harin ta ce, jiragen sama na yaki kirar RAF Typhoon guda 4 wadanda suka tashi daga Cyprus sun yi ruwan bama-bamai a sansanonin soji biyu da ke kusa da wani filin jirgin saman soji a Yemen din.
Sakataren tsaro na Birtaniyar GrantShapps ya bayyana harin a matsayin na kare kai daga hare-haren ‘yan Houthi da ba za a lamunta ba a kan jiragen ruwa na kasuwanci.
Kwana goma sha daya da ya gabata Amurka da Birtaniya suka kai hari na farko irin wannan ta sama da ya kai gommai a kan wurare na soji da suka hada da jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami da wuraren na’urorin tsinkayen jiragen sama, wadanda suka ce ‘yan Houthin na amfani da su wajen kai hare-haren a Maliya.
A wancan lokacin an sa ran harin zai sa ‘yan Houthin su daina abin da suke yi, to amma ko alama sai ma suka ci gaba, da kai farmakin kan jiragen ruwa na kasuwanci suka lalata da dama.
A ‘yan makonnin da suka gabata Amurka ita kadai ta rika kai karin hare-hare a kan mayakan na Houthi inda ta ce tana kai wa ne kan makamai masu linzami na mayakan a daidai lokacin da ake shirin harba su.
Su wane ne 'yan Houthi kuma me ya sa suke kai hari kan jiragen ruwa?
Ta yaya hare-hare a tekun Maliya za su shafi kasuwancin duniya?
Hatsarin mayar da martanin Houthi ga harin Amurka da Burtaniya a Yemen
Muna muku maraba!
Masu bibiyar wannan shafi na Kai Tsaye, assalamu alaikum. Barkan mu da wannan lokaci.
Kamar kodayaushe, a yau ma Talata, za mu kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Muna fatan za ku kasance tare da mu. Akwai kuma karin labarai a shafukanmu na sada zumunta inda za ku iya kallon har bidiyo da muke wallafawa.