Kotu ta soke kasafin kuɗin jihar Ribas na naira biliyan 800

Asalin hoton, RIVERS STATE GOVERNMENT
Babbar kotu a Abuja ta soke kasafin kuɗin jihar Ribas da ya kai naira biliyan 800 wanda majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin ɓangaren Edison Ehie ta amince da shi kuma ya samu sa hannun gwamna Siminalayi Fubara.
Kotun ta tabbatar da ƙarar da majalisar da shugabanta Martin Amaewhule suka shigar don kalubalantar Fubara da suka nemi a dakatar da gwamnan daga yi wa ayyukan majalisar a karkashin jagorancinsa makarkashiya.
Ken Njemanze wanda lauyan Amaewhule ne ya zargi gwamnan da yin katsalandan ga ayyukan yan majalisa saɓanin yadda doka ta bambance ayyukansu.
Wanda ya shigar da karar ya nemi kotu ta hana wanda ake kara daga hana majalisar kudaden da take bukata na tafiyar da ayyukanta har da biyan albashi da alawus-alawus.
Da farko alkali James Omotosho ya ce Ehie ta hannun lauyansa Oluwole Aladedoye ya ce ya yi murabus daga majalisar dokokin Ribas.
Omotosho ya ce Ehie ba shi da ikon shigar da kara saboda ba shi ne shugaban majalisar dokokin Ribas ba sannan kuma ba dan majalisa ba ne.
A ranar 13 ga watan Disamba, lokacin da rikicin siyasa ya yi zafi a jihar mai arzikin man fetur har ta kai ga rushe ginin majalisar, Fubara ya gabatar da kasafin 2024 na N800bn gaban yan majalisa biyar karkashin Edison Ehie.
Ya gabatar da kasafin kudin a fadar gwamnati da ke Fatakwal sakamakon rushe ginin majalisar da gwamnatin jihar ta yi sannan bayan kotu ta hana abokin hamayyar Ehie, Martins Amaewhule daga amfani da harabar majalisar.
Ehie da sauran yan majalisa masu goyon bayan Fubara sun amince da kasafin kudin inda kuma gwamnan ya sanya hannu a kai. Ya ce an yi haka ne domin habaka tattalin arziki da kuma magance matsalolin da suka shafi al'umma.
Daga baya ne kuma Ehie ya ajiye mukaminsa daga majalisar inda aka mayar da Amaewhule a matsayin shugaban majalisar bayan duka bangarorin biyu sun gana da shugaba Bola Tinubu a Abuja.






