Kenya ta kama jami'an ƴan sanda bisa zargin sace wani ɗan ƙasar China

Asalin hoton, Reuters
An kama jami'an ƴan sandan uku a Kenya bisa zargin su da hannu a sace wani dan kasar China domin neman kudin fansa.
Ana zargin su da yi wa ɗan kasar Chinan kwanton-ɓauna yayin da yake kan hanyarsa zuwa aiki a ranar 8 ga watan Janairu, inda suka daure shi tare da dauke shi.
Daga nan ne jami’an ‘yan sandan suka yi masa fashi kafin su sake shi, kamar yadda ‘yan sanda suka ce.
Hukumomin ƙasar na kuma neman wani dan kasar China da ake kyautata zaton shi ne jagoran waɗanda suka sace shi.
"Wanda ya jagoranci garkuwan ya kira dangin wanda aka sace a China yana neman kudin fansa wanda aka aika zuwa wani asusun banki a China," in ji 'yan sandan a kan shafin X.
"Bayan an aika da kudin fansar ne, kuma masu garkuwan suka tabbatar da cewa dangin sun yi biyayya, shi ne aka sako wanda aka yi garkuwa da shi."
‘Yan sanda sun ce lamarin ya “bankado wasu gungun masu aikata laifuka na kasashen duniya waɗanda ke yin bincike kan ƙarfin arzikin wanda suke hari kafin aikata laifin.
Hukumomin kasar Kenya suna aiki tare da hukumar ƴan sandan duniya ta Interpol domin gano wadanda suka aikata laifin a China.
- Shugaban Kenya ya nemi afuwar al'ummar ƙasar kan mace-macen masu azumi
- Yadda azabtar da ɗalibai a makarantu ta zamo annoba a Kenya








