Ana taron addu'oi a Nijar kan mutuwar malami a hannun ƴan bindiga

Malaman makarantu a Jamhuriyar Nijar na zaman addu’o’i ga malamin da ƴan bindiga suka halaka ranar 10 ga watan Janairu.
Malaman suna gudanar da taron addu'oin a cibiyar ƙungiyar ƙwadago ta malaman makarantu ta SYNACEB.
Taron ya samu halartar ministar ilimin ƙasar, Dr Elizabeth Cherif.
A ranar 27 ga watan Oktoban bara ne ƴan bindiga suka yi awon gaba da wasu malaman makaranta biyu inda ɗaya daga cikinsu ya rasa ransa a hannun su.
A baya-bayan nan ne, malaman ƙarƙashin SYNACEB reshen Makalondi suka gudanar da yajin aiki domin nuna rashin jin daɗinsu game da taɓarɓarewar tsaro a jihar Tillabery.
Ana ci gaba da samun ƙazancewar matsalar tsaro a jihar Tillabery duk da iƙirarin da majalisar mulkin sojin ƙasar ke yi na samun nasara a yakin da take da mahara.
















