Zambiya za ta karɓi kashin farko na rigakafin kwalara da ta ɓarke a ƙasar

Asalin hoton, Zambia Presidency/Facebook
Zambiya na shirin karɓar alluran rigakafin cutar kwalara miliyan 1.6 yayin da ƙasar ke fama da ɓarkewar cutar mafi muni.
Fiye da mutum 350 sun mutu sannan mutum 9,000 suna fama da cutar tun lokacin da ta ɓarke a watan Oktoban bara.
Gwamnatin Zambiya ta samo alluran da haɗin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya da hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, Unicef.
Ma'aikatar lafiyar ƙasar ce za ta karɓi alluran a hukumance bayan an shigar da su ƙasar da yammacin jiya Lahadi.
"Bayan nan kuma ma'aikatar za ta kammala shirye-shirye na soma yi wa al'umma rigakafin a zaɓaɓun cibiyoyi a Lardin Lusaka," in ji ma'aikatar lafiyar inda ta ce Lardin ne aka fi samun masu fama da cutar ta kwalara.
A yanzu cutar ta bazu zuwa Larduna tara cikin 10 na ƙasar ta Zambiya.
Hukumomin ƙasar sun ɗauki matakan kariya daban-daban domin daƙile yaɗuwar cutar ciki har da jinkirta komawar ɗalibai makaranta da taƙaita masu zuwa jana'izar mutanen da cutar ta halaka zuwa mutum biyar.
Filin wasa mafi girma da ke ƙasar a yanzu hukumomi sun mayar da shi wajen kula da masu cutar ta kwalara.
Gwamnati ta kuma yi kira ga al'ummar ƙasar da ke zaune a birni su koma ƙauyuka.






