Rufewa
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mukhtar Adamu Bawa da Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya
Habiba Adamu, Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Mukhtari Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mukhtar Adamu Bawa da Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Ɗan kwallon kafar Argentina da Inter Miami Lionel Messi ya lashe kyautar fitaccen ɗan kwallon kafar Fifa na bana.
Messi ya samu kyautar ne bayan buge abokan karawarsa Erling Haaland da kuma Kylian Mbappe.


Asalin hoton, Defence Headquarters Nigeria

Asalin hoton, Defence Headquarters Nigeria

Asalin hoton, Defence Headquarters Nigeria

Asalin hoton, Defence Headquarters Nigeria

Asalin hoton, Defence Headquarters Nigeria

Asalin hoton, Defence Headquarters Nigeria
Ƴan bindiga sun kai hari wani sansanin sojoji a kauyen Nahuta da ke jihar Katsina, inda suka fatattaki sojoji da cinna wa motocinsu wuta.
Sun kuma kutsa cikin shaguna da gidajen mutane tare da sace kayan abinci da dabbobi da kuɗinsu ya kai miliyoyin naira, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Wani mazaunin kauyen Isa Bello, ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa harin kan sansanin sojin wanda ke ɗauke da sojoji, ƴan sanda da kuma wasu jami'an tsaro a karamar hukumar Batsari na jihar ta Katsina, ya faru ne ranar Lahadi.
Sai dai mai magana da yawun ƴan sandan jihar Abubakar Sadiq bai mayar da martani ba da aka tuntuɓe shi don ji daga ɓangarensu.
Gungun ƴan bindiga rike da makamai suna ta cin karensu ba babbaka a faɗin arewacin Najeriya a cikin shekaru uku da suka gabata, inda suka yi garkuwa da ɗimbin mutane, da kashe ɗaruruwa da kuma saka wa mutane fargabar ƙasa tafiya ta hanya ko zuwa gonaki a wasu yankuna.
Bello ya faɗa wa Reuters cewa ƴan bindigar waɗanda suka zo kan babura da kuma wata babbar mota da misalin karfe 10 na dare, sun ci karfin sojojin inda suka shafe sa'o'i uku suna musayar wuta da juna.
Wani jami'in gwamnatin jihar Katsina ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rayuka ba a kauyen, in ji Reuters.
Harin ya sanya fargaba a cikin mazauna kauyen na Nahuta, inda yawanci daga cikinsu suka tsere zuwa kauyuka da ke kusa domin neman mafaka.

Asalin hoton, Reuters
An kashe wata mata mai shekara 70 tare da jikkata wasu 17 a harin karo da mota a Isra'ila.
A kama Falasɗinawa biyu a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ka lamarin da ya faru a birnin Raanana, kilomitoci 20 da arewacin Tel Aviv.
Waɗanda ake zargin sun shiga cikin motoci uku na sata da yin gudu kan gefen tituna daban-daban.
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da yaƙi tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hamas a Gaza ke shiga kwana 100.
Rahotannin kafafen yaɗa labarai na Isra'ila sun ce ɗaya daga cikin wanda ake zargi ne ya ɗaba wa matar wuka, kafin shi da waɗanda suka aikata laifin suka ɗauki motar ta da rugawa cikin mutane.
Motar ta kubucewa masu laifin ne inda suka sake sace wata mota da ci gaba da tuki cikin mutane, a cewar rahotanni.
Ba a dai san yadda aka tsayar da kuma kama mutanen ba.
Ƴan sanda sun ce dukkan waɗanda ake zargin sun fito ne daga birnin Hebron na gaɓar yamma kuma sun shiga Isra'ila ba bisa ka'ida ba.
Akwai rahotannin kai hare-hare a Isra'ila tun bayan ɓarkewar yaƙi ranar 7 ga watan Oktoba, kuma abin da ya faru ranar Litinin zai ƙara saka wa ƴan Isra'ila fargaba.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC, ta kama tsohon ministan masana'antu, Charles Ugwu, kan zargin almundahanar kuɗi da ya kai naira biliyan 3.6.
An kori Mista Ugwu wanda marigayi shugaban ƙasa Umaru Musa Yar'Adua ya naɗa, bayan sauye-sauye da aka yi a gwamnati da ya shafi ministoci 19.
A cewar wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na EFCC Dele Oyewale ya fitar ranar Litinin, ta ce an kama tsohon ministan tare da wani Geoffrey Ekenma ne a jihar Imo ranar 11 ga watan Janairun 2024.
An bayyana cewa kama mutanen biyu na zuwa ne bayan korafi da wani bankin kasuwanci ya kai wa hukumar yana zargin wani kamfani mai suna Ebony Agro da tafka almundahana, wanda kuma yake alaƙa da tsohon ministan.
Sanarwar ta ce, "Bincike ya gano cewa an zargi Ugwuh da Ekenma da kuma Ebony Agro da karɓar rance daga bankin domin saye da dillancin shinkafar da aka gyara.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta koma atisaye don tinkarar wasanta na gaba a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Ivory Coast ke karɓar bakunci.
Super Eagles ta tashi 1-1 da Equatorial Guinea a wasanta na farko a rukunin A.
A ranar Alhamis, Najeriya za ta buga wasanta na gaba da mai masaukin baki Ivory Coast.



Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga sun sace tsohon shugaban ƴan sandan Burkina Faso.
An ɗauki Lt Col Evrard Somda a gidansa da ke Ouagadougou, babban birnin ƙasar ranar Lahadi, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.
An kori Mista Somda daga aiki a watan Oktoban bara, mako ɗaya bayan da aka tsare wasu jami'an ƴan sanda guda huɗu da zarginsu da yunkurin juyin mulki.
Ana samun batun garkuwa da mutane a baya-bayan nan a ƙasar da ke Yammacin Afrika.
An yi garkuwa da Sansan Anselme Kambou - wani hamshakin attajiri na kusa da Mista Somda -
an influential businessman who was close to Mr Somda - was abducted by intelligence agents in September. In December, former foreign minister Ablasse Ouedraogo was taken by people claiming to be the police.

Asalin hoton, TINUBU/FACEBOOK
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kashe naira biliyan 3.4 a kan tafiye-tafiyen cikin gida da kuma na ƙasashen waje a cikin watanni shida na farkon mulkinsa, a cewar rahotanni.
Hakan na nufin Shugaba Tinubu da jami'an gwamnatinsa sun zarce kasafin kuɗin naira biliyan 2.49 da aka ware wa tafiye-tafiyensu a 2023 da kashi 36, kamar yadda jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito.
Punch ta ce duk da yake shugaban ya gaji kasafin kuɗin ne na rabin karshen shekarar 2023, "ya kashe sama da abin da aka ware a gaba-ɗaya shekarar daga watan Yuni zuwa Disamban 2023".
Rahoton wanda BBC ba ta tabbatar ba, ya zo ne kusan mako ɗaya bayan da Shugaba Tinubu ya zaftare yawan jami'ai da za a bari suna yi masa rakiya yayin tafiye-tafiyensa da kuma na sauran manyan jami'an gwamnatinsa zuwa ƙasashen waje da kuma a cikin gida.
Kafin haka, an soki lamirin shugaban kan makudan kuɗaɗen da yake kashewa wajen tafiye-tafiye waɗanda ƴan Najeriya suke ganin sun yi yawa.
Ɗaya daga cikin tafiye-tafiyen ita ce, wadda gwamnatin Tinubu ta ɗauki nauyin jami'ai sama da 400 domin zuwa taron sauyin yanayi na COP28 da aka a yi Dubai, inda aka yi ta sukarsa.
Jmai'an Amurka sun ce mayaƙan Houthi a Yemen sun harba wani makamai mai linzami kan wani jirgin ruwan Amurka, sai dai ba a samu jin ciwo ko wata gagarumar ɓarna ba.
Wani kamfanin kula da harkokin tsaron teku na Birtaniya ya ce an harbi jirgin ne don mayar da martani ga hare-haren da Amurka da Birtaniya suka kai kan 'yan Houthi da ke Yemen.
Mayaƙan ƙungiyar Houthi sun fara kai hare-hare kan jiragen ruwa masu dakon kaya tun cikin watan Nuwamba. Suna cewa jiragen suna da alaƙa da Isra'ila, ko da kamfanin samar da tsaron teku na Birtaniya ya ce babu wannan alaƙar.
Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya faɗa wa manema labarai cewa ƙasarsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar ƙarin matakai a kan 'yan Houthi don kare kanta a Tekun Maliya.
Da goyon bayan Iran, ƙungiyar Houthi na iko da wani makeken sashe na ƙasar Yemen sannan kuma su manyan ƙawayen Hamaz ne a Gaza. Don haka sun yi alƙawarin ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwan da suka nufi Isra'ila.

Asalin hoton, Hope Uzodinma/X
An rantsar da Hope Uzodinma a matsayin gwamnan jihar Imo karo na biyu.
Gwamnan ya sha rantsuwane filin wasa na Dan Ayiam da ke Owerri, babban birnin ƙasar.
A jawabinsa na rantsuwar kama aiki, Uzodinma ya yi alkawarin ninƙa ayyuka fiye da wanda ya yi a wa'adin mulkinsa na farko.
Ya gode wa al'ummar jihar bisa goyon baya da suka ba shi har ya sake samun nasara.
Ita ma mataimakiyarsa Lady Chinyere Ekomaru, ta sha rantsuwar kama aiki.
Cikin manyan mutane da suka halarci bikin rantsuwar, akwai Shugaba Bola Tinubu, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas, da kuma wasu jiga-jigan jam'iyyar APC.
Haka ma, ɗumbin mutane daga ciki da wajen jihar ne suka halarci bikin rantsuwar na ranar Litinin.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar malaman kananan makarantu ta "(SYNACEB) reshen Makalondi ta jihar Tillabery a Jamhuriyar Nijar ta tsunduma cikin wani yajin aiki.
Malaman sun shiga yajin aikin na kwanaki biyu ne daga ranar Litinin domin janyo hankalin gwamnati ta ɗauki matakai na kare malaman daga matsalar tsaro.
Ƙungiyar ta ce ɗauki matakin ne bayan la'akari da abin da ya faru a ranar 27 ga watan Oktoban bara, inda 'yan bindiga suka yi awon gaba da wasu malaman makarantu biyu da kuma lamarin ranar 10 ga watan Janairu inda aka kashe wani malami bayan shafe tsawon lokaci a hannun ƴan bindigar.
Lamarin tsaro dai na ƙara taɓarɓarewa a jihar Tillabery duk da iƙirarin da shugaban majalisar mulkin sojin ƙasar yayi na cewa suna samun nasara a yaƙin.

Asalin hoton, Reuters/@ndsprod33
Mamakon ruwan sama wanda ya janyo ambaliya na ci gaba da ɗaiɗaita sassan ƙasar Mauritius a cikin sa'o'i kaɗan da suka gabata.
Hukumar lura da yanayi ta ƙasar ta ce wata mahauckaciyar guguwa mai haɗari mai suna Belal na daf da shiga tsibirin da ke gabashin Madagascar.
Ana kuma sa ran cewa guguwar za ta wuce zuwa kudancin tsibirin a safiyar ranar Talata.
A ranar Litinin, wasu hotuna da aka yaɗa a kafofin sada zumunta suka nuna motoci nitse a cikin ruwa a gefen tituna kusa da Port Louis, babban birnin ƙasar.
Mahaukaciyar guguwar ta riga da ta lalata wurare da ke kusa, a cewar hukumomi.
An ruwaito mutuwar mutum ɗaya sannan ta ɗaiɗaita sama da 600.
A safiyar yau ne aka sanar da rufe makarantu a ƙasar sakamakon guguwar da ke tafe.

Asalin hoton, Getty Images
Hauhawar farashi na watan Disamba ya kai tsananin da ba a taɓa gani ba cikin sama da shekara 27a Najeriya.,
An samu hauhawar farashin kayayyakin abinci, abin da ya janyo tsadar rayuwa ga ƴan ƙasar da kuma matsin lamba kan babban bankin ƙasar da ya ƙara kuɗin ruwa.
Farashin kayayyaki ya tashi cikin watanni 12 a jere a watan Disamba zuwa kashi 28.92 bayan da ya kai kashi 28.20 a watan Nuwamba, a cewar Hukumar Kididdiga ta Ƙasar (NBS) ranar Litinin.
Rabon da a samu irin wannan hauhawar farashi a ƙasar da ke sahun gaba a girman tattalin arziki a Afrika tun 1996.
NBS ya ce hauhawar farashi a Najeriya ya tashi zuwa kashi 33.93 a watan Disamba daga kashi 32.84 a watan Nuwamba.
Hukumar ta ce kayayyakin da farashinsu ya yi tashin gwauron zabi sun haɗa da burodi, abinci dangin hatsi, mai, kifi, nama, kayan itace da kuma kwai.
Masana sun ce ƙaruwar kuɗin man fetur da kuma karyewar darajar naira na cikin abubuwan da suka janyo hauhawar farashin.

Asalin hoton, FACEBOOK
Wani mai ɗaukan hoto ɗan ƙasar Ghana, Patrick Amenuvor ya yanke shawarar janye ƙudurinsa na son kafa tarihin tsayuwa mafi tsawo a duniya.
Ya ɗauki matakin janyewar ne ƙasa da sa'a huɗu bayan ya soma tsayuwar da tun farko ya tsara zai shafe kwana bakwai yana yi.
Ya soma tsayuwar a ranar 14 ga watan Janairu sai dai ya dakatar da ƙudurin saboda saɓa wasu ƙa'idoji kamar yadda aka bayyana cikin wata sanarwa, a cewar jaridar Graphic Showbiz.
Patrick Amenuvor ya bayyana ƙudurinsa na tabbatar da adalci a matsayin babban dalilin da ya sa ya dakatar da burin kafa tarihin da yake son yi.
A sanarwar, ya tabbatar da karya wasu dokoki da ke da muhimmanci wajen ƙwace kambun da kuma kafa tarihi.
Ya ce ya zama dole ya sake komawa teburi domin yin nazari kafin ya sake gwada sa'arsa.
Ya kuma bai wa magoya bayansa tabbaci cewa dakatar da ƙudurin ba shi ne ƙarshen burinsa ba sai dai a cewar sa, wata dama ce ta sake shiryawa.

An yanke wa mutum biyu hukuncin ɗaurin rai da rai saboda kisan wata ƴar makaranta a West Dunbartonshire da ke yankin Scotland fiye da shekaru 27 da suka gabata.
A ranar 25 ga watan Agustan 1996 ne aka gano gawar Caroline Glachan mai shekara 14 yashe a gefen kogin Leveb a Renton.
Dole ne Robert O'Brien ya yi zaman yari na aƙalla shekara 22 yayin da Andrew Kelly ya kamata ya yi aƙalla shekara 18 a ɗaure kafin su nemi a yi musu sassauci.
Donna Marie Brand wadda ita ma aka samu da laifin kisa, ba ta samu halartar zaman kotun ba kuma daga baya ne za a yanke mata nata hukuncin.

Asalin hoton, SPINDRIFT
Mutanen uku sun musanta aikata kisan amma an same su da laifi bayan shafe tsawon mako biyu ana shari'a a babbar kotu da ke Glasgow.
Alƙali Lord Braid ya bayyana kisan a matsayin na mugunta.
An faɗa wa masu taimaka wa alƙali cewa Caroline daga Bonhill tana nuna alamar ƙauna ga O'Brien.
A daren da aka yi kisan, ta shirya haɗuwa da shi a wata gada da ke saman kogin Leven.
An kashe ta a wani yanayi da masu gabatar da ƙara suka kira "mummunan hari", an naushe ta sau kusan 10 a ka inda kuma ta samu munanan raunuka a ƙwaƙwalwa.
Masu taimaka wa alkalin sun samu bayanin cewa wata ƙila tana da rai amma ta suma lokacin da ta faɗa ruwa.
Hukumar kare haƙƙin bil adama a Najeriya ta ce ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 752 da ke da nasaba da cin zarafi a jihar Filato tsakanin Janairu zuwa Nuwamban 2023.
Wata jami'a a hukumar, Veronica Abe ce ta bayyana haka ranar Litinin a birnin Jos.
A cewar Abe, ƙorafe-ƙorafen sun shafi na tsare mutane ba bisa ƙa'ida ba da kisan kiyashi da cn zarafi da fyaɗe da auren dole da ƙin ba da gado.
Jaridar Punch ta ruwaito jami'ar na cewa an kammala bincike kan galibin ƙorafe-ƙorafen sai dai akwai waɗanda ake aiki a kansu.
Ta ƙara da cewa lamarin ya shafi mutum 1,053 har da mata 166 da yara 463.
Jami'ar a hukumar ta kare haƙƙin bil adama ta tabbatar da cewa nan ba da daewa ba za su kammala aiki kan ƙorafe-ƙorafen da suke ƙasa.
Ta kuma yi kira ga mazauna jihar ta Filato da su kai rahoton cin zarafi zuwa hukumomin da suka dace domin ɗaukan mataki.