An bai wa Cabo Verde shaidar rabuwa da zazzabin cizon sauro

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana Cabo Verde a matsayin ƙasar da ta rabu da zazzabin cizon sauro - wani muhimmin ci gaba ga fannin lafiya.
A yanzu ƙasar ta shiga jerin ƙasashe 43 da yanki ɗaya da WHO ta bai wa wannan shaida ta rabuwa da cutar ta maleriya.
Cabo Verde ce ƙasa ta uku a nahiyar Afirka da ta samu wannan shaida daga WHO baya ga Mauritius da aka tabbatar ba ta da cutar a shekarar 1973 sai Algeriya a 2019.
Shugaban hukumar WHO, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yaba wa gwamnatin Cabo Verde saboda jajircewarta wajen kawar da cutar ta zazzaɓin cizon sauro.
"Shaidar da WHO ta bai wa Cabo Verde na rabuwa da maleriya na nuna tasirin tsare-tsaren da suka shafi lafiyar al'umma." in ji Dr Ghebreyesus.
Dr Dorothy Achu, jami'ar WHO a Afirka ta shaida wa BBC cewa an ɗauki matakai sosai kafin samun wannan ci gaba.
Ta ce "muna murna ƙwarai, mun ji daɗi sosai cewa an samu sakamako mai kyau daga ƙoƙarin likitoci da jami'an kula da ƙwayoyin cuta da ƙwararru a yankin wajen ganin an kawar da maleriya daga Afirka. Wannan wani fata ne, wannan ya ƙara mana ƙwarin gwiwa cewar mai yiwuwa ne a cimma haka. Ita ce ƙasa ta farko, Cabo Verde, ƙasa ta farko cikin shekara 50 da ta gabata a yankin kudu da hamadar sahara da ta samu wannan ci gaba."
Cutar zazzabin cizon sauro ta fi ƙamari a nahiyar Afirka da ke da kusan kashi 95 cikin 100 na masu fama da ita sai kashi 96 cikin 100 na mace-macen da ke da nasaba da cutar a 2021.











