Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge, Mukhtari Adamu Bawa and Abdullahi Bello Diginza

  1. ISIS ta ɗau alhakin harin da aka kai Kabul

    Ƙungiyar SISI mai ikirarin jihadi ta ɗauki alhakin kai harin da aka kai Kabul a jiya Talata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum uku. Hari na biyu da aka kai birnin a mako guda.

    Ƙungiyar ta sanar da hakan ne ta kafar Telegram, wanda ta ce ta nufi ma'aikatar gidan yarin Pol Charkhi" wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 10.

    Kakakin Taliban a Kabul Khaled Zadran ya sanar da hakan ne a jiya, inda ya ce mutum uku ne suka mutu wasu huɗu na daban suka jikkata, a harin da suka kai dalilin ajiye wani abun fashewa a cikin mota. Ya ce duka mutanen da abun ya rutsa da su "fararen hula ne".

    Kwanaki hudu da uka gabata, mutum biyar sun mutu, 15 kuma suka jikkata a yankin Shi'a da Hazara da ke Kabul wanda shi ma ISIS suka dauki alhaki.

  2. Shekarau ya nemi Abba, Gawuna su amince da duk hukuncin da kotun koli ta sanar

    .

    Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya yi kira da mabiya da shugabannin NNPP da na APC su rungumi hukuncin da kotun kolin ƙasar za ta yanke a matsayin ƙaddara.

    Shekarau ya yi wannan kira ne a wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels a wani shirin siyasa.

    Shekarau ya ce, ya yi imani da cewa babu wani zagi ko cin zarafi ko kuma kalaman ɓatanci da za su sauya hukuncin da ko tu za ta yanke, ko kuma su sa a bai wa wani nasara a yayin hukuncin.

    Tun a watan Maris ɗin 2023 ne ake ta sa-toka-sa-katsi a kotu tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma Nasiru Yusuf Gawuna kan kujerar gwamnan jihar Kano.

    Shekarau ya ce "duk mutumin da ke bin siyasa ta, yasan siyasar zaman lafiya da kwanciyar hankali nake yi. Ina ɗaukar abokan siyasata abokaina ba tare da duba banbancin siyasa ba.

  3. 'Ina fatan harin da aka kai min zai kawo ƙarshen siyasar gaba a Koriya ta Kudu'

    .

    Shugaban babbar jam'iyyar adawa a Koriya ta Kudu, Lee Jae-myung, ya ce ya na fatan harin da aka kai masa ta hanyar daɓa wuka a wuya zai kawo karshen siyasar ƙiyayya a ƙasar.

    Mr Jae-myung, ya bayyana haka ga magoya bayan shi da manema labarai a jawabin, bayan sallamarsa daga asibitin birnin Seoul da safiyar yau.

    Ya ce yana son amfani da wannan dama da fatan za a samu sauyi a siyasar ƙasarsu mai kama da yaki.

    Yana godiya kan yadda mutane suka taimaka masa a lokacin ga shi yanzu kuma rayuwa in yi muku aiki.

    Nan gaba a yau ake sa ran 'yan sanda za su gabatar da sakamakon bincike kan harin da aka kai wa jagoran adawar.

  4. Me ya sa Tiwa Savage ta nemi 'yan sanda su shiga tsakaninta da Davido

    ...

    Asalin hoton, facebook/multiple

    'Yansandan Najeriya sun fara gudanar da bincike kan shahararren mawaƙin nan na ƙasar Davido bayan ƙarar da abokiyar sana'arsa Tiwa Savage ta shigar a kansa, bisa zargin cin zarafinta da kuma yi mata barazana da rayuwarta.

    A watan jiya ne tankiya ta ƙara ƙamari tsakanin mawaƙan biyu, bayan Tiwa ta sanya wani hotonta da na mahaifiyar ɗaya daga cikin 'ya'yan Davido a shafinta na Instagram.

    A ƙorafin da ta shigar a wajen 'yansandan kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka ambato, Tiwa ta ce hoton da ta wallafa ya ɓata wa Davido rai, inda ya yi zargin ta yi hakan ne domin ta fusata shi.

    Ta yi zargin amsar da Davido ya mayar mata kan hoton "ya yi ta ne cikin rashin girmamawa da ɓacin rai".

    Tiwa ta yi zargin Davido ya riƙa aikamata mutane Legas su jamata kunne "ta bi a hankali" wanda ta ce "hakan ya saɓa al'ada" kuma "barazana ce ga 'yancinta na rayuwa, da mutuncinta".

    Har yanzu dai Davido bai ce komai ba kan wannan zargi.

    Duka taurarin biyu dai sun yanke ƙawancen da ke tsakaninsu a Instagram.

  5. An kakkaɓo sama da makamai masu linzami 20 da 'yan tawayen Houthi

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Sojojin Amurka da Burtaniya sun kakkaɓo sama da makamai masu linzami 20 da 'yan tawayen Houthi na Yemen suka harba wa wani jirgin ruwa a tekun maliya a jiya Talata.

    Sanarwar da sojin Amurka suka fitar ta ce babu wanda ya ji rauni ko asarar rai ko lalata wani abu.

    'Yan tawayen Houthi na Yemen da Iran ke marawa baya, sun ce sun zafafa hare-hare kan jiragen dakon kaya a tekun Maliyar a matsayin martani kan yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.

    Ba kuma za su daina ba, har sai sun tabbatar ana kai cikakkun kayan agaji ga Falasdinawa da dakatar da buɗe wuta.

  6. Guguwa da ruwan sama sun faɗawa wasu jihohin Amurka

    Ƙaƙƙarfar guguwa haɗe da ruwan sama sun faɗawa wasu jihohin Amurka, tuni mutane uku suka mutu wasu sama da 600 na zaune babu wutar lantarki.

    An soke tashi da saukar dubban jirage, wasu an ɗage lokacinsu, yayin da tilas aka karkatar da jirgin da mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris na Air Force 1 ke ciki zuwa wata jihar.

    A Alabama, kuma wata tsohuwa mai shekara 80 ta rasu, lokacin da guguwar ta yi awon gaba da gidan tafi-da-gidanka da ta ke ciki.

    Tuni gwamnan Florida Ron DeSantis,ya ayyana dokar ta-ɓaci a jiharsa.

  7. 'Babu sasanci tsakaninmu da 'yan bindiga'

    ,

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban sojin Ecuador ya ce babu wani sasanci tsakaninsu da gungun ɓata garin da suka sanya ƙasar cikin tashin hankali a kwanakin nan.

    Tun da fari shugaba Daniel Noboa ya ce ana fama da rikicin masu ɗauke da makamai na cikin gida.

    Wannan na zuwa ne bayan wasu ƙungiyoyin 'yan daba sun jefa bama-bamai a motoci da gidajen mutane, da ofisoshin gwamnati.

    'Yan dabar sun kuma shiga gidan talabijin ana tsaka da gabatar da shiri kamar yadda wani ma'aikacin ya bayyana.

    Ya ce suna dakin watsarin labarai, sai ya ga abokin aikinsa cikin tashin hankali, ya na cewa ga su anan za su kashe mu, sai ƙarar harbin bindiga.

    Daga baya dai 'yan sanda sun shawo kan lamarin.

  8. Barka da hantsi

    Muhammad Buhari Fagge ke fatan an tashi lafiya, tare da fatan kasancewa da ku a wannan yini na Laraba, domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassa daban-daban na faɗin duniya.

    Abubuwan da ke faruwa a ƙasashen Larabawa da nahiyar Turai da nahiyar Afrika za su kasance cikin wannan shafi namu.

    Ku kasance da mu domin jin mai duniyar ta kwana cikin, da kuma yadda za ta yini a wasu nahiyoyin a wasu kuma yadda za ta kwana.