Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Mukhtar Adamu Bawa and Usman Minjibir

  1. 'Binciken Betta Edu zai bankaɗo abubuwa da dama'

    Betta Edu

    Asalin hoton, facebook/Betta Edu

    Masana a Najeriya na ci gaba da tsokaci game da matakin shugaban ƙasar, Bola Tinubu na dakatar da ministar jin ƙai, Betta Edu da ake zargi da badaƙala daban-daban.

    Matakin dakatarwar ya zo ne wata shida kacal da naɗa ta kan muƙamin minista kuma ita ce minista ta farko a karƙashin mulkin Tinubu da ta fuskanci suka kan zargin ta da almundahana.

    Dr Abubakar Kari, wani masanin harkokin siyasa a Najeriya ya shaida wa BBC cewa matakin ya zo kan gaɓa kasancewa ya zo ne a daidai lokacin da al'ummar ƙasar ke kiraye-kiraye na a ɗauki mataki kan ministar da ake yi wa zargin almundahana.

    Sai dai ya yi shakku kan ko gwamnati za ta iya ɗaukan mataki a kan ministar.

    A cewarsa, matakin kuma zai bai wa gwamnatin Tinubu dama ta gudanar da bincike kasancewa gwamnatin na dabaibaye da zarge-zarge da batutuwa da dama.

    Ya kara da cewa hanzarin dakatar da ministar zai aika saƙo ga jami'an gwamnati saboda watakila hakan ya sa su yi tunanin gwamnatin ta sha banban da gwamnatin da ta gada.

    Dr Kari ya ce "duk da gwamnati ta bayar da umarnin a yi bincike a tura ta hukumar EFCC sannan ta kafa kwamiti a karƙashin ministan harkokin tsaro, amma bisa abubuwan da suke faruwa a baya muna da shakku cewa ba kawai suna neman lokaci ba ne maganar ta bi ruwa."

    Ya bayyana cewa matuƙar gwamnati ta yi bincike, to za a gano abubuwa da dama kuma hakan ne zai tabbatar wa ƴan Najeriya ko da gaske ita gwamnatin Tinubu take ko kuma "kawai ta yi ne domin ta sama wa kanta lokaci da kuma sarari."

    Masanin siyasar ya ce zai yi wuya ministar ta koma kan kujerarta ko da kuwa an wanke ta daga zarge-zargen da ake mata, idan kuwa hakan ta faru, toh zai zama na farko a tarihi.

    "Tun da ban taɓa jin akwai inda aka yi waɗannan manya-manyan zarge-zarge a jami'an gwamnati aka cire su kuma aka dawo da su ba." in ji masanin.

    Ya ƙara da cewa abu ne mai wahala a iya wanke ministar daga girman zarge-zargen da ake mata saboda "kusan kowane wayewar gari sai an ɓallo wani abu daga cikin abubuwan da ke faruwa a wannan ma'aikata tata wanda kuma akwai sunanta."

  2. Koriya ta Kudu ta amince da dokar haramta kisa da sayar da naman kare

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Koriya ta Kudu ta amince da wata sabuwar dokar da za ta kawo ƙarshen kisa da saida naman karnuka nan da shekarar 2027.

    Dokar za ta kawo ƙarshen daɗɗiyar al'adar cin naman kare.

    A ƙarƙashin dokar, za a haramta yanka wa da sayar da naman ƙarnuka da rarrabawa.

    A cewar dokar za a hana yanka karnuka don cin namansu. Haka kuma raba naman da sayar da shi. Waɗanda aka samu da laifi, na iya fuskantar zaman gidan yari.

    Masu sana'ar sayar da naman kare na iya fuskantar hukuncin shekara kusan uku a gidan yari yayin da waɗanda ke kiwon karnuka don cin namansu ko sayar da namansu na iya shafe shekara biyu a gidan yari.

    Sai dai cin naman karen a karan kansa ba zai zama laifi ba.

    Sabuwar dokar za ta fara aiki ne nan da shekara uku inda aka bai wa manoma da masu gidajen abincin da ke sana'ar dama ta sake sabuwar sana'a. Za su miƙa ƙudurinsu na sauya sana'a ga mahukunta a ƙananan hukumominsu.

    Gwamnati ta yi alƙawarin tallafa wa masu kiwo da mahauta da kuma masu gidajen abinci da ke sana'ar naman karen da aka tilastawa rufe kasuwancin amma kuma ba a ƙayyade diyyar da za a biya su ba.

    A cewar alƙaluman gwamnati, akwai kusan gidajen abinci 1,600 da ke sayar da naman kare a Koriya ta Kudu da kuma gonakin kiwon kare 1,150 a shekarar 2023.

    Tsofoffi a Koriya ta Kudu sun ɗauki Naman kare a matsayin abinci mai matuƙar muhimmanci amma matasan ƙasar ba su cika damuwa da shi ba.

  3. An kashe gomman Falasɗinawa a arewacin Gaza – Rahotanni

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu - Wafa ya ce Isra'ila ta kai jerin hare-hare a kudanci da tsakiyar Gaza har da kewayen sansanonin Maghazi da Al-Bureij.

    Wafa ya ce an kashe gomman Falasɗinawa a Jabalia da Beit Hanoun waɗanda ke arewacin zirin Gaza.

    Isra'ila ta ce tana kai hare-hare ne kan ƴan ta'adda da cibiyoyinsu kuma tana ƙoƙari don ganin an samu raguwar mace-macen farar hula.

    Tun farko mutum 57 ne suka mutu a asibitin Al-Aqsa da ke tsakiyar Gaza cikin kwana ɗaya.

    • Yadda Zirin Gaza zai kasance bayan kammala yaƙi
    • Dole a bar Falasɗinawa su zauna a Gaza - Blinken
  4. Farashin mai ya ninka sau biyar a Cuba

    Cuba ta sanar da ƙarin farashin man fetur, inda ta ninka farashin har sau biyar, a wani mataki na ƙoƙarin rage tallafin da ake biya da kuma rage kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa.

    Ministan kuɗi da Farashi, Vladimir Regueiro, ya ce matakan sun zama dole don farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

    Gwamnati ta kuma sanar da cewa za ta buɗe gidajen mai guda ashirin da tara waɗanda dalar amurka kaɗai za su riƙa karɓa.

  5. Gwamna Yahaya Bello ya tuɓe rawanin sarakuna uku, ya dakatar da ɗaya

    ..

    Asalin hoton, FACEBOOK/ALHAJI YAHAYA BELLO

    Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya tuɓe rawanin sarakunan gargjiya uku a jihar.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da manema labarai bayan kammala taron majalisar zartaswa na jihar da aka yi a birnin Lokoja, ranar Lahadi.

    A cewar gwamnan, matakin ya zo ne bayan bin duka dokoki da ƙa'idojin da suka shafi masarautun gargajiya kuma hakan na faruwa ne ƙasa da mako uku kafin ya sauka daga kan kujerarsa a matsayin gwamnan jihar.

    Sarakunan gargajiyar da matakin ya shafa sun haɗa da Mai Martaba Alhaji Abdulrazaq Koto, Ohimege-Igu na Koton-Ƙarfe wanda kuma shi ne shugaban majalisar sarakunan gargajiya a ƙaramar hukumar Lokoja/Kogi. A yanzu za a mayar da shi ƙaramar hukumar Rijau ta jihar Neja, da zama.

    Sai Mai Martaba Sam Bola Ojoa, Olu Magongo na Magongo wanda zai a mayar garin Salka a ƙaramar hukumar Magama da ke jihar Neja.

    Mai Martaba Sarki Samuel Ayi Onimisi, Obobanyi na Emani wanda shi kuma za a mayar da shi garin Doko a ƙaramar hukumar Lavun da ke jihar Neja.

    Game da tsige Onimisi, gwamna Bello ya ce muƙamin Obobanyi na Ihima da aka ɗaga darajarsa zuwa ta daya, "an yi haka ne ba tare da duba cewa mukamin Obobanyi na Ihima

    Gwamnan ya kuma ce an dakatar da mai martaba Boniface Musa, Onu-Ife a ƙaramar hukumar Omala har sai yadda hali ya yi.

    An kuma naɗa Ahmed Anaje, wanda shi ne Ohi na Okenwe a matsayin Ohinoyi na Ebiraland.

    "Ibrahim Gambo Kabir kuma an naɗa shi a matsayin Maigari na Lokoja sai Dauda Isah da aka naɗa a matsayin Maiyaƙi na Kupa.

    • Wane ne zaɓaɓɓen gwamnan Kogi Usman-Ododo?
    • Kalli gidan gwamnan mulkin mallaka, bature Lugga a Lokoja
  6. Blinken ya isa Isra'ila a ƙoƙarin hana watsuwar yaƙi a Gabas ta Tsakiya

    ..

    Asalin hoton, US Embassy in Israel

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Isra'ila domin tattaunawa mai wuyar gaske kan yaƙin da ake yi a Gaza.

    Ya ce zai ƙara matsa lamba domin ganin an ƙara tabbatar da kare Falasdinawa farar hula, da kai kayan agaji da kuma barin waɗanda yaƙin ya raba da muhallansu komawa gidajensu.

    Mr Blinken yana ta ganawa da shugabannin Larabawa a ƙoƙarin da yake yi na ganin yaƙin bai watsu ba a yankin na Gabas ta Tsakiya.

    Kafin barin Saudiyya ranar Litinin inda ya gana da Yarima mai jran gado, Mr Blinken ya yi gargaɗi kan ta'azzarar yaƙin.

    Jami'an lafiya na Hamas sun ce fiye da mutum 23,000 aka kashe a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila tun soma yaƙin.

    • Yaƙin Gaza : Afirka ta Kudu ta kai ƙarar Isra'ila Kotun Duniya
    • 'Yaƙin Gaza zai iya ɗaukar ƙarin watanni ana gwabzawa'
  7. Maraba!

    Jama'a assalamu alaikum, barkan mu da safiya. Da fatan muna cikin ƙoshin lafiya.

    Kamar yadda aka saba, a yau ma za mu wallafa muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Muna fatan za ku kasance tare da mu. Ga masu son ƙarin labarai da bidiyo, kuna iya garzayawa shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da X da Instagram.