Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Mukhtar Adamu Bawa and Usman Minjibir

  1. Amurka za ta kai Koriya ta Arewa ƙara a kan tallafa wa Rasha da makamai

    ...

    Fadar White House ta ce Koriya ta Arewa na ƙara yawan makamai masu linzami da take taimaka wa ƙasar Rasha domin ci gaba da kai wa Ukraine hare-hare.

    Kakakin ma'aikatar tsaron kasar, John Kirby, ya ce dakarun Rasha suna amfani da makaman wajen kai hare-hare cikin Ukraine.

    Ya ce wannan babban abun damuwa ne a taimakon da Korea ta Arewa ke ba wa Rasha, kuma Amurka za ta kai korafinta ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

    Harwayau, Mista Kirby ya kuma yi ikirarin cewa Rashar na neman gudummawar makamai daga Iran.

    Ko a watan Disambar da ya gabata sai da Rashar ta kai wa kasar Ukraine wani hari irinsa mafi muni tun fara yakin, inda aka samu rashe-rashe da jikkata da kuma lalata gine-gine.

  2. Majalisar Wakilan Najeriya na nazari kan ƙudurin kafa ƙarin jami'o'i 47 a ƙasar

    ...

    Akwai yiwuwar yawan jami'o'n gwamnatin tarayya kan iya kai wa 99 a 'yan watanni masu zuwa, sakamakon wani kudiri da aka yi wa karatu na biyu a majalisar wakilan Najeriya.

    Kudirin dai na son kafa ƙarin jami'o'i guda 47 a kasar, ƙari a kan guda 52 da kasar ke da su a yanzu haka.

    Wannan kari ne a kan wasu kudurori guda 56 da majalisar ta yi wa karatun nabiyu domin kafa ƙarin Cibiyoyin kula da lafiya na gwamnatin taryya wato Federal Medical Centres a sassan ƙasar da dama.

    Harwayau, majalisar na duba yiwuwar karin wasu kudurorin domin kafa wasu kwalejojin ilimi 32 da na koyan aikin noma 11 da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha guda biyar.

    Yanzu haka dai akwai manyan cibiyoyin kula da lafiya na gwamnatin tarayya guda 22 da kwalejojin ilimi guda 27 da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha guda 40, a faɗin Najeriya.

    Waɗanda ake son kafawar yanzu sun hada da jami'o'in kimiyya da fasaha da na aikin gona da sufurin jirgin sama da kuma nazarin aikin injiniya da dai sauransu.

  3. An saki Oscar Pistorius bayan yi masa sassauci

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    An saki ɗan wasan tseren nakasassu Oscar Pistorius daga wani gidan yari a Afirka ta Kudu bayan ya yi kusan shekara 11 a ɗaure sakamakon kashe budurwarsa Reeva Steenkamp.

    Hukumomi sun tabbatar Pistorious ya isa gida da safiyar yau Juma'a bayan ya yi rabin zaman ɗaurin da aka yanke masa na sama da shekara 13.

    Mahaifiyar Ms Steenkamp ta ce ta amince da matakin na sakin tsohon ɗan wasan tseren amma ta kara da cewa iyalinta ne ke zaman ɗaurin rai da rai.

    Pistorius da a yanzu shekarunsa 37 ya harbi Ms Steenkamp a 2013 da bindiga inda ɗan wasan tseren ya yi iƙirarin ya yi kuskuren harbinta ne saboda ya yi tunanin ɓarawo ne.

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Reeva Steenkamp

    Daga baya an samu Pistorious da laifin kisa a 2015 bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta sauya matsaya kan hukuncin da aka yi a farko na kisan kai.

    A karƙashin dokar Afirka ta Kudu, masu laifi na iya samun sassauci da zarar sun yi rabin shekarun da aka yanke masa inda a shekarar 2017 aka yanke wa Pistorius hukuncin shekara 13 da wata biyar a gidan yari.

    June Steenkamp cikin wata sanarwa ta ce iyalanta sun san da sanin cewa "yin sassauci ɓangare ne na tsarin shari'ar Afirka ta Kudu" kuma "sun san cewa dole ne a bar doka ta yi aikinta".

  4. Isra'ila ta gabatar da ƙudurori kan makomar Gaza bayan yaƙi

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Wata mata yayin da take kukan mutuwar mijinta a Khan Younis da ke Gaza

    Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya gabatar da shirinsa kan makomar Gaza, bayan kammala yaƙi.

    Amurka ta daɗe tana matsa wa gwamnatin Isra'ila lamba da ta bayyana shirinta a fili.

    Wakilin BBC ya ce a yayin da Isra'ila za ta karɓi ragamar tsaron yankin, alhakin sake gina Gaza zai rataya ne a kan wata rundunar ƙasa da ƙasa da za a samar, sannan Masar za ta iya taka wata muhimmiyar rawa da bai fito ƙarara ya bayyana ba.

    Yoav Galanta ya ce Falasdinawa ne ke rayuwa a Gaza, don haka za su ci gaba da jagorancin yankin, amma bisa sharaɗin cewa babu zaman doya da manja da Isra'ila, kuma babu shirya mata wata kutungwila.

    A cewarsa, yanzu yaƙin da Isra'ila ke yi a zirin zai fi mayar da hankali kan kudancin yankin, kana za su ci gaba da ƙoƙarin ganin sun kashe shugabannin ƙungiyar Hamas, ko a ina suke a doron duniya.

  5. Barka da warhaka!

    Jama'a, assalamu alaikum, barka da wayar gari lafiya a wannan babbar rana ta Juma'a.

    Kamar koda yaushe, za mu wallafa rahotanni da labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

    Da fatan za ku kasance tare da mu. Za kuma ku iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu ƙarin labaran da ma kallon bidiyo.