Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Mukhtar Adamu Bawa and Usman Minjibir

  1. Tinubu ya buƙaci hafsoshin tsaron Najeriya su kakkaɓe matsalar rashin tsaro a ƙasar

    .

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bukaci shugabannin tsaron ƙasar da su tabbatar da ɗaura ɗamara domin magance matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta.

    Yayin da yake jawabi ga manyan hafsoshin tsaron a taron majalisar tsaron ƙasar da ya gudana a fadar gwamnatinsa ranar Juma'a da maraice , shugaban Tinubu ya ce yayin da ake samun ci gaba a kakkabe matsalolin tsaro da ƙasar ke fama da su, akwai buƙatar ƙara jajircewa don tabbatar da magance matsalolin tsaron da ke ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya.

    "Nasarar da kuke samu abin a yaba ne. 'Yan Najeriya na gani a ƙasa, amma ya kamata a yi ƙoƙarin kauce wa kura-kurai, irin wanda aka gani a baya-bayan nan a jihar Kaduna, haƙiƙa haɗin kai da ake samu takanin jami'an tsaro na ƙara inganta a watannin baya-bayan nan, amma a yanzu ba lokacin nuna murna ba ne, har sai mun kakkaɓe matsalar baki ɗayanta,'' in ji shugaba Tinubu.

    Shugaban ya kuma ya buƙaci sojojin da su tabbatar da muradin ƙasar na haƙo ganga miliyan biyu na man fetur a kowace rana a cikin rubu'in farko na shekarar 2024.

    .

    Asalin hoton, State House

  2. Blinken ya isa a Turkiyya a rangaɗin yankin Gabas ta Tsakiya

    ..

    Asalin hoton, ....

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa a Turkiyya a zagayen farko na rangaɗin yankin Gabas ta Tsakiya da ya fara wanda zai kai shi har Isra'ila da kuma ƙasashen Larabawa da dama.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce zai nanata buƙatar a kara kai kayan agaji ga fararen hula a Gaza sannan a kuma tabbatar da ba a fitar da su karfi da yaji ba daga yankin.

    Zai kuma so ya hana takon-sakar da ake yi tsakanin Isra'ila da Hizbullah kara yin kamari.

    Amurka dai ta bayar ɗaukin makamai masu yawa ga Isra'ila a yaƙin da take yi da Hamas, amma kuma ta nuna damuwa game da yawan Falasɗinawa fararen hular da aka kashe.

  3. Gwamnatin Yobe ta soke lasisin makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar

    .

    Asalin hoton, MAI MALA BUNI

    Gwamnatin Yobe ta soke lasisin wasu makarantu masu zaman kan su da ke jihar, tare da kiran masu makarantun su bi tsarin doka da odar da gwamnati ta shinfiɗa don neman sabon lasisi.

    Gwamnatin ta kara da cewa daga yanzu duk wasu lamura na makarantar za su dinga tafiya kafaɗa-da-kafaɗa da makarantun gwamnati, ba za a ƙara ba su damar gaban kansu ta fuskar dokoki da sauransu ba.

    Kwamishinan ilimi na jihar Dakta Muhammad Sani Idriss, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, a ganawar da suka yi da masu makarantu masu zaman kansun, a makarantar sakandaren gwamnatin tarayya ta GGC Damaturu.

    Ya ƙara da cewa babu wata makarantun da za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta ba tare da sabon lasisi da bin dokar da gwamnatin jihar Yobe ta gindaya ba.

    Ya ce, “ mun soke lasisin makarantu masu zaman kansu, dan haka za su sake sabo.

    A baya an ba su wannan damar kai tsaye, amma an bukaci su bi wasu dokoki amma hakan bai samu ba, shi ya sa muka ɗauki wannan matakin.''

  4. Yakin Isra'ila da Gaza ya shafi cinikin kamfanin McDonalds

    Soyayyen dankalin da McDonalds ke saidawa

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, McDonalds na daga cikin wuraren saida abinci masu farin jini a kasashen gabas ta tsakiya

    Shahararren kamfanin sayar da abinci nau'in kwalam da maƙulashe na duniya McDonalds, ya ce ya samu koma-bayan ciniki saboda ƙauracewar da a ka yi masa a yankin gabas ta tsakiya sakamakon goyon bayan da ya ke nuna wa Isra'ila.

    Shugaban kamfanin Chris Kempczinski ne ya bayyana hakan a sakon da ya wallafa a dandalin LinkedIn inda ya dora alhakin hakan kan bayanai marasa tushe balle makama.

    Shi ne na biyu cikin shugabannin kamfanin na Amurka da suka yi bayani kan yadda cinikin ke gudana daidai lokacin da yaƙi ke ƙara ƙazancewa tsakanin Isra'ila da Gaza.

    Shi ma kamfanin Starbucks ya bayyana samun koma bayan ciniki, kan alaƙa da tashin hankalin Isra'ila da Hamas.

    "Yawancin kasuwanci a yankin gabas ta tsakiya da wajensa na fuskantar koma bayan ciniki saboda yakin, ana kuma yada labaran da ba su da tushe hakan ya shafi kamfanoni kamar McDonald's," inji Kempczinski a sakon da ya wallafa.

    "Wannan abin takaici ne yadda lamarin ke gudana''.

    "A dukkan ƙasashen da muke gudanar da ayyukanmu, ciki har da na Musulmi, ina alfaharin shaida muku McDonalds na da farin jini kuma muna aiki tare da 'yan ƙasashen ."

    McDonalds dai ya dogara ne ga dubban 'yan kasuwa masu zaman kansu, kuma yawanci su ne kashin bayan rassa sama 40,000 a sassa daban-daban na duniya, kuma kashi 5 cikin 100 su na gaba ta tsakiya.

  5. 'A bai wa kamfanin mai na Shell damar bayar da bahasi bisa zargin malalar mai a Neja Delta'

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun ƙolin Najeriya ta ce ya kamata a bai wa kamfanin mai na shell damar gabatar da bahasi kan zargin da ake yi masa na malalar mai a yankin Naija Delta.

    A baya kotun ɗaukaka ƙara ta hana kamfanin sayar da wata rijiyar man da ya mallaka tare da yanke hukuncin biyan kuɗi kafin a saurari korafinsa.

    A ranar Juma'a Kotun ƙolin ta ce kotun ɗaukaka arar ba ta yi duba na tsanaki ba kan batun, inda ta bai wa kamfanin na Shell damar gabatar da bahasi.

    Ba a dai sani ba hukuncin zai bai wa kamfanin damar sayar da rijijiyar tasa.

    An fara batun ne a gaban wata babbar kotu da awatan Nuwamban 2020 ta bayar da umarni ga kamfanin na Shell ya biya naira biliyan 800 da al'ummomin Egbalor da Ebubu da ke jihar River a matsayin kuɗin diyya.

    Al'ummomin sun zargi kamfanin da da gurɓata musu ruwan shansu da gonakinsu sakamakon malalar mai a yankin, zargin da kamfanin ya musanta.

    Shell ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun ɗaukaka ƙara, to sai dai kotun ta umarci kamfanin ya saka kudin cikin wani asusun banki da kotun ke iko da shi, kafin a ci gaba da sauraro ƙorafin nasu.

    Kamar sauran manyan kamfanonin mai a Najeriya shell na mayar da hankali ne wajen haƙar mai a tsakiyar teku saɓanin gaɓar teku, inda ɓarayin mai da masu fasa bututun mai ke kawo wa cikas.

  6. An mayar da gawar Gwamna Rotimi Akeredolu Najeriya

    Gawar Akeredolu

    Asalin hoton, Richard Olatunde

    Bayanan hoto, Isowar gawar Rotimi Akeredolu Najeriya daga kasar Jamus

    Gawar tsohon gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, SAN, CON, ta isa Najeriya.

    Jirgin da ya ɗauki gawar daga ƙasar Jamus inda marigayin gwamnan ya rasu, ya sauka gida Najeriya da maraicen ranar Juma'a 5 ga watan Janairu 2024.

    Mai ɗakin marigayin Chief Betty Anyanwu-Akeredolu,da 'ya'yansa da ƙaninsa ,Farfesa Wole Akeredolu, da wakilin gwamnan jihar Lagos Mista Babajide Sanwo-Olu,da wakilan gwamnan Ogun, da gwamnan Osun Senator Demola Adeleke da sauran 'yan uwa da abokan arziki da shugaban jam'iyyar APC na jihar sun je tarar gawar tsohon gwamnan.

    Iyalai 'yan uwa da abokan arziki sun ɓarke da kuka a lokacin da aka fara fito da akwatin gawar daga cikin jirgin da ya kawo ta.

    Akeredolu ya rasu a wani aibiti a kasar Jamus bayan fama da jinyar kansar mafitsara a ranar 26 ga watan Disamba 2023.

    A yanzu za a ajiye gawar a mutuware kafin yi masa jana'aiza. Za dai a sanar da lokacin hakan bayan kammala shirye-shirye ga wasu daga cikin hotunan isowar gawar:

    Gawar Akeredolu

    Asalin hoton, Richard Olatunde

    Bayanan hoto, Akwatin gawar Akeredolu nannade da tutar Najeriya
    Gawar Akeredolu

    Asalin hoton, Richard Olatunde

    Bayanan hoto, Gwamnoni da wakilan manyan mutane sun halarci tarar gawar
    Akeredolu

    Asalin hoton, Richard Olatunde

    Bayanan hoto, Matar marigayin da dan uwasan da aminai lokacin da suke jiran isowar jirgin dauke da gawar Akeredolu
  7. Ƴan sandan Birtaniya sun kama mutum biyu kan zargin kisan matashi

    ..

    Asalin hoton, MET POLICE

    Bayanan hoto, Harry Pitman

    Ƴan sanda a Birtaniya sun kama wasu samari biyu kan zargin kisan Harry Pitman wanda ya mutu bayan daɓa masa wuƙa.

    Samarin ƴan shekara 16 da 17 sun miƙa kansu ne bayan da ƴan sanda suka saki hotunan mutanen da take son magana da su.

    Harry, mai shekara 16 ya gamu da ajalinsa ne sakamakon faɗan da ya kaure a Primrose Hill yayin da mutane suka taru domin kallon wasan tartsatsin wuta don maraba da sabuwar shekara.

    Babban jami'in ɗan sanda Geoff Grogan ya ce: "Wannan babban al'amari ne kuma muna tuntuɓar iyalansa."

    Matasan biyu dai na tsare kamar yadda rundunar ta bayyana.

    An kuma ba da belin ƙarin matasa uku ƴan shekara 15 da 16 da kuma 18 da aka tsare kan hannu a kisan inda za a ci gaba da gudanar da bincike.

    Harry ya mutu ne ranar 31 ga watan Disamba bayan faɗan da ya kaure tsakaninsa da wani tsaransa, in ji rundunar ƴan sandan.

    Babbar yayar Harry, Tayla Pitman ta shaida wa Mail Online cewa sun girgiza da kisan ɗan uwan nata.

  8. Yadda zaizayewar ƙasa haɗe da ambaliya suka share gine-gine a Japan

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

    Wannan bidiyon ya nuna yadda zaizayewar kasa ya tafi da gine-gine a Wajima da ke ƙasar Japan.

    Bidiyon ya nuna yadda wasu gungun mutane suka tsira daga mummunar ambaliyar da ta afka wa yankin.

    An ɗauki bidiyon ne a ranar sabuwar shekara bayan mummunar girgizar ƙasa da ta afka wa ƙasar.

    A ranar Juma'a, tawagar masu ceo suka ceto mutum 242 da ba a gani ba sakamakon ambaliyar.

    Akalla mutum 94 ne hukumomi suka tabbatar da mutuwarsu sakamakon girgizar ƙasar.

  9. Rikicin Isra'ila da Hezbolla ya raba fiye da mutum 76,000 da muhallansu a Lebanon

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum 76,000 ne suka rabu da muhallansu a Lebanon sakamakon takun-saƙar da ake yi tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hizbullah.

    Hukumar Kula da Masu Kaura ta Duniya (IOM) ta ce yawancin 'yan Lebanon ɗin da suka ƙaurace wa muhallan nasu na zama a gidaje wasu danginsu.

    Haka ma an kwashe mutanen da ke zaune a ƙauyuka da garuruwan Isra'ila da ke kusa da kan iyakar ƙasashen biyu saboda faɗan.

    Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce dole a samu wani yanayi a yankin iyakar ƙasashen biyu da zai ba da damar Isra'ilawan da aka kwashe daga can su koma.

    Rundunar sojin Isra'ila kuma ta ce ta kai hari kan wasu wurare na ƙungiyar ta Hezbullah a kudancin Lebanon a yau.

  10. Haramcin tantance takardun shaidar karatun Benin da Togo zai shafi ɗalibai 15,000 - NANS

    .

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya ta NANS, reshen ƙasar Benin ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su sassauta dokar soke tantance takardun shaidar karatun digiri daga ƙasashen Benin da Togo,

    Shugaban ƙungiyar NANS reshen ƙasar Benin Ugochukwu Favour ne ya yi wannan kira a lokacin wata tattaunawa da yi da kafar yaɗa labarai ta Channels ranar Alhamis.

    Yana mai cewa matakin zai shafi ɗaliban Najeriya 15,000 da ke karatu yanzu haka a ƙasar ta Benin.

    A farkon makon nan ne wani ɗan jaridar Daily Nigerian ya bayyana yadda ya samu digirin boge cikin mako shida a wata jami'a da ke ƙasar ta Benin har ma ya samu damar shiga sansanin 'yan yi wa ƙasa hidima.

    Bayan ɓullar rahoton ne gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwar dakatar da tantance takardun shaidar digiri daga ƙasashen Benin da Togo.

    To sai dai shugaban ƙungiyar ɗalibana Nejeriya NANS, reshen ƙasar Benin ya ce ya kamata gwamnati ta yi la'akari da ɗaliban da suka samu gurbin karatu kuma suke karatun ta hanyar da ta dace.

    “Abin da zan ce shi ne, ya kamata gwamnatin tarayya ta duba lamarin, babu yadda za a yi don abu ya faru a wata makaranta, sannan a yi hukuncin da zai shafi kowa, saboda matakin ya shafi ɗalibai kusan 15,000 da ke karatu a Benin''.

  11. MDD ta mayar da martani kan sukar da Isra'ila ta yi mata a Gaza

    Hukumomin agaji na MDD sun mayar da martani da sukar da Isra'ila ta yi musu cewa su ne ke hana ruwa gudu wajen kai kayan agaji Gaza.

    Sun ce akwai dalilai masu yawa da ke kawo cikas ga ƙoƙarin da suke yi na kai kayan agajin ciki har da rashin tsaro da lalacewar hanyoyi da kuma tsaikon da ake samu a shingayen bincike.

    Nebal Farsakh, kakakin ƙungiyar ba da agaji ta Red Crescent a Falasdinu, ya ce ƙungiyoyin ba da agajin na yin iyakar ƙoƙarinsu wajen samar da kayan agaji ta mashigar Rafah, kuma daga lokacin da aka fara faɗan zuwa ranar 30 ga Disamba sun samu manyan motoci kusan 5,280 maƙare da kayan abinci da ruwa da kuma magunguna.

    Jami'an lafiya a Gaza sun ce mutum 162 aka kashe cikin sa'a 24 na baya-bayan nan a jerin hare-haren da Isra'ila ta ci gaba da kai wa.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hare-hare ta sama sau 100 a kan cibiyoyin ƙungiyar Hamas a cikin kwana dayan da ya wuce.

    Ana dai sa ran sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da wani babban jami'in diflomasiyya Joseph Borrel za su je yankin a yau Juma'a, domin tattaunawa a kan halin da ake ciki.

  12. Mun bai wa al'ummar Sabon Birni tallafin N20m da kayan abinci - Gwamnan Sokoto

    ..

    Asalin hoton, @Ahmedaliyuskt/X

    Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya yi bai wa al'ummar yankin Sabon Birni da ayyukan ƴan bindiga ya shafa tallafin sama da naira miliyan 20 tare da rarraba magunguna da kayan abinci.

    Ya kuma yi alƙawarin ɗaukar nauyin kuɗin maganin mutanen da suka ji rauni sakamakon hare-haren ƴan bindiga a ƙaramar hukumar da ke jihar.

    Gwamnan ya bayyana haka ne bayan ziyarar da ya kai tare da Sanata Aliyu Wamakko zuwa ƙaramar hukumar domin jajanta wa mutanen da hare-haren ƴan bindiga suka shafa.

    A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Gwamnan ya ce zai ci gaba da tallafa wa al'ummar yankin tare da kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga a jihar.

    ...

    Asalin hoton, @Ahmedaliyuskt/X

    Ya kuma bayyana damuwa kan faruwar hare-haren inda ya ce yana matuƙar kaɗuwa duk lokacin da aka samu afkuwar harin ƴan bindiga a wani yanki na jihar.

    A cewarsa, gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba domin daƙile matsalar rashin tsaro a jihar ta Sokoto.

    Ahmad Aliyu ya kuma ce za su ci gaba da tallafa wa jami'an tsaro inda ya sanar da basu motoci 100 da kuma horas da ƴan vigilante 2,000 domin su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro a jihar.

    Ya ƙara da cewa za a bai wa ƴan vigilanten babura 700 domin sauƙaƙa ayyukansu ƙarƙashin kulawar hukumomin tsaro.

  13. Gobara ta hallaka marasa lafiya a asibitin Jamus

    ..

    Asalin hoton, Alamy

    Mutane hudu ne suka mutu a gobarar da ta tashi a wani asibiti kusa da Hamburg, a arewacin Jamus.

    Da misalin karfe 22:45 na daren Alhamis agogon kasar gobarar ta tashi, a hawa na uku na asibitin Helios Clinic da ke gundumar Uelzen.

    Akalla mutum 20 ne suka jikkata, kuma 'yan sanda sun ce adadin wadanda suka mutu ka iya fin hakan sakamakon munanan raunukan da wasu suka ji.

    Rahotanni sun bayyana cewa 'yan kwana-kwana da ma'aikatan ceto 140 na ciki da wajen gundumar Uelzen ne suka yi taron dangi domin kashe gobarar da kwashe marasa lafiya, wasu ta tsani aka fidda su.

    An yi kiyasin gobarar ta janyo asarar kusan Yuro miliyan daya, kuma tuni hukumomi suka fara gudanar da bincike kan musabbabin tashin gobarar.

    Asibitin Helios dai na karkashin kulawar asibitin koyarwa na Hannover Medical School, kuma shafin intanet na aibitin ya ce su na da akalla ma'aikata 750, yayin da suke kula da lafiyar mutum 42,000 a kowacce shekara.

  14. An kama magidanci bisa zargin sukar matarsa a wuya har ta mutu

    ..

    Asalin hoton, Nig.Police

    Rundunar ƴan sandan Yobe ta kama wani magidanci mai shekara 43 kan zarginsa da hannu a mutuwar matarsa mai shekara 42.

    Kakakin rundunar 'yansandan jihar DSP Dungus Abdulkarim ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin wanda ya ce suna kan gudanar da bincike kan lamarin.

    DSP Dungus ya ce mutumin na tare da matarsa a ɗakinsu a lokacin da aka soke ta a wuya, lamarin da ya sa ta yi ta zubar da jini har rai ya yi halinsa.

    Lamarin ya faru ne a Damaturu bayan da al'ummar rukunin gidajen New Bra Bra suka tashi da labarin mai ratsa zuciya bayan gano gawar matar yashe a gidanta da yanka a wuyanta.

    mai magana da yawun 'yansandan ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike game da mummunan lamarin domin gano mutanen da suke da hannu.

    Ya kara da cewa duka da cewa yankan bai kai ga makogoron matar ba, amma ya shafi jijiyoyin da ke kai jini zuwa kanta, ta yada babu yadda za a yi ta rayu.

    Ya kuma ce kawo yanzu bincikensu bai gano abin da aka yanka ta da shi ba.

    A cewar rundunar, ma'auratan ma'aikata ne a jami'ar jihar Yobe da ke Damaturu.

  15. Fatan madugun adawar Senegal ya gamu da tasgaro bayan hukuncin kotun ƙoli

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Kotun ƙolin Senegal ta yi watsi da ƙarar da madugun ƴan adawar ƙasar ya ɗaukaka kan samunsa da laifin ɓata suna.

    Da wannan hukuncin, Mr Sonko ba zai iya tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen wata mai zuwa.

    Ana kallonsa a matsayin babban abokin karawa a zaɓen domin maye gurbin Shugaba Macky Sall wanda zai sauka daga mulki bayan wa'adi biyu.

    Sonko dai ya sha fuskantar shari'a tun 2021 sai dai ya musanta aikata tuhume-tuhumen.

    A watan da ya gabata ne kuma, kotu ta ba da umarnin a mayar da sunansa cikin jerin sunayen ƴan takara.

    Ana ganin hukuncin ya ba shi damar fafatawa a zaɓen bayan da a baya aka hana shi saboda samunsa da aifi a wata ƙara ta daban.

    A Mayun bara, kotun ɗaukaka ƙara ta yanke wa Sonko hukuncin wata shida a gidan yari saboda ɓata wa ministan harkokin yawon buɗe ido, Mame Mbaye Niang.

    Bayan shafe sa'a 12 ana sauraron ƙarar, Kotun Ƙolin ƙasar ta yi fatali da ƙarar da Sonko ya ɗaukaka domin ƙalubalantar tuhumar da ake masa ta ɓata suna.

    A cewar dokokin zaɓe, hukuncin kotun da ya same shi da laifi ya soke damarsa ta tsayawa takara a zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu.

    Sai dai lauyoyin Sonko sun ce wannan ba shi ne mataki na ƙarshe ba.

    Lauyansa Cire Cledor Ly ya shaida wa ƴan jarida a wajen kotun cewa ba za su gajiya ba.

    Kamen da aka yi masa lokuta da dama cikin shekaru biyu da suka gabata ya janyo mummunan tashin hankali a ƙasar.

    Sai dai rahotanni na cewa ba a ga alamun za a yi wata zanga-zanga ba game da hukuncin kotun.

    A ranar 20 ga watan Janairu ne ake sa ran za a fitar da jadawalin ƙarshe na sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa.

  16. A watan Janairun nan za a kammala gwajin matatar man Fatakwal – NNPCL

    ...

    Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

    Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya ce a cikin watan nan ne za a kammala gwajin matatar mai ta Fatakwal da ke kudancin ƙasar don ci gaba da aikin tace mai bayan shafe shekaru biyar a rufe.

    Kakakin kamfanin Femi Soneye ya ce "nan ba da daɗewa bane za a kammala gwajin matatar don tabbatar da tana aiki yadda ya kamata. Za a kammala a cikin wannan watan."

    Matatar wadda ake inganta ta, za ta soma tace gangar mai 60,000 duk rana kuma kamfanin na NNPCL yana sa ran nan gaba a shekarar, za ta riƙa tace ganga 210,000 ta mai kowace rana.

    Matatar man ta Patakwal ɗaya ce daga matatun mai na gwamnati da suka shafe tsawon shekaru a durƙushe wanda kuma a yanzu gwamnatin ke son farfaɗo da ita da nufin kawo karshen dogaron da ƙasar ke yi kan tataccen man da ake shigowa da shi daga wasu ƙasashe.

    Ana ganin idan matatar man ta soma aiki, za ta taimaka wajen samuwar man fetur a kasar tare da sauƙaƙa wa ƴan ƙasar wahalhalun da suke fuskanta ta dalilin rashin iya tace man a ƙasar.

  17. 'Ana buƙatar sama da naira tiriliyan ɗaya kafin kammala titin Abuja zuwa Kaduna'

    ..

    Asalin hoton, NIGERIA POLICE

    Ministan ayyuka a Najeriya, Sanata David Umahi ya ce kamfanin gine-gine Julius Berger na neman sama da naira triliyan ɗaya domin kammala shimfiɗa babban titin Abuja zuwa Kaduna.

    Da yake magana a wani taro da daraktocin ma'aikatar ayyukan a Abuja, babban birnin Najeriya, ministan ya ce titin da farko an ware naira biliyan 165 wanda aka ƙara kuɗin zuwa naira biliyan 654.

    Ya ce gwamnati ba ta da shirin biyan sabon farashin saboda rashin kuɗi.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an ba da kwangilar aikin a shekarar 2017 amma sai a 2018 aka soma aikin.

    Ya kamata a kammala titin cikin shekarar 2021 wanda ɗaya ne daga cikin ayyukan gwamnatin Buhari.

    Sai dai hakan bai samu ba har gwamnatin ta sauka a 2023 amma dai an kammala fiye da rabin aikin titin.

  18. Har yanzu ba a ga kusan mutum 250 ba bayan girgizar ƙasar Japan

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Masu aikin ceto a Japan na hanzarin lalubo mutum 242 da har yanzu suka yi ɓatan dabo bayan mummunar girgizar ƙasar da aka yi ranar sabuwar shekara.

    A ranar Juma'a, adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 7.6 da ta afku a yankin Noto Peninsula suka ƙaru zuwa 92.

    Rundunar sojin Japan ta ninka yawan sojojin da suke taimakawa wajen kuɓutar da mutanen zuwa 4,600 kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Kyodo ya bayyana.

    Ana tunanin ƙasa ta danne mutane da dama bayan da gidaje suka ruguje - galibi a yankunan Suzu da Wajima.

    Dubban mutane har yanzu ba su da wutar lantarki da ruwa yayin da ɗaruruwa kuma ba sa iya samun taimako saboda zabtarewar ƙasa da toshewar tituna.

    "Ba za mu yanke ƙauna ba," in ji Firaminista Fumio Kashida bayan taron da ya yi da jami'an da ka ba da agaji.

  19. 'Yan sanda sun ce sun kama wadda ake zargi ɓarauniyar waya ce a Borno

    ..

    Asalin hoton, @BornoPoliceNG/X

    Bayanan hoto, Kwamishinan ƴan sandan Borno

    Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Borno ta ce ta kama wata mata da ake zargin ta shahara wajen sace-sacen waya da wasu mutum 84 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.

    Laifukan da ake zargin mutanen sun aikata ƙunshi haɗin baki da fyaɗe da kisan kai da fashi da makami da sata da mallamar muggan makamai da kuma shan tabar wiwi.

    Da ake holen mutanen a Maiduguri ranar Alhamis, Kakakin rundunar ƴan sandan ta Borno, ASP Daso Nahum.

    Ya ce rundunar ta samu rahoton laifuffuka 49 sun kuma samu waɗanda ake zargi 27 da laifi. Ya ƙara da cewa rundunar tana bincike kan wasu laifuffuka 14 sai wasu 31 da aka gurfanar da su a kotu.

    Kakakin ya ce an kama matar ranar 28 ga watan Disamban da ya gabata bayan ayyana ta a matsayin wadda ake neman ruwa a jallo sakamakon sace-sacen wayoyin jama'a.

    "Yayin bincike, ta faɗi wanda suke satar tare, suna zuwa gidajen mutane a matsayin ƴan aiki inda suke kwashe wayoyin mutanen da suke yi wa aiki."

    "An gano waya kirar Techno LC6 yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin kama mutanen da wayar ke hannunsu daga bisani kuma a gurfanar da su a kotu," kamar yadda kakakin ƴan sandan ya bayyana.

  20. Bidiyo: An gano baƙin kumurci laɓe a cikin masan tangaran

    An kirawo mai kama macizai Tennille Banks don ta je ta cire wani baƙin kumurci mai mugun dafi wanda aka hango shi ya kwanta male-male a cikin masan tangaran a ƙauyen Goondiwindi da ke cikin yankin Queensland, na ƙasar Australia.

    Ƴan sanda sun ja da baya lokacin da take kokawar kamo macijin daga cikin masan tangaran, inda ta jawo shi waje da ƙarfen kamun macizai, kuma ya faɗi ƙasa, amma daga bisani ta yi nasarar cusa shi a cikin wani ƙaton buhu.

    Daga baya kuma aka sake shi ya shiga daji.

    Baƙin kumurcin wanda aka sani da suna (blue-bellied black snake) da Ingilishi, yana cikin rukunin macizai masu dafi da ke dazukan ƙasar.

    Bayanan bidiyo, Lamarin ya faru ne a ƙasar Ostireliya