Blinken zai ziyarci Gabas ta Tsakiya karo na hudu tun fara yakin Isra'ila

Asalin hoton, Reuters
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken zai kai ziyara Gabas ta Tsakiya karo na huɗu, tun bayan da yaƙi ya ɓarke tsakanin Hamas da Isra'ila cikin watan Oktoba.
Wani jami'in Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP da Reuters cewa ziyarar za ta haɗa da zuwa Isra'ila daidai lokacin da ake bayyana damuwa game da tasirin yaƙin ga yankin.
Jami'in ya ce a daren yau, Alhamis ne Blinken zai yi bulaguron inda zai ziyarci wasu ƙasashen har da Isra'ila.
Sai dai babu ƙarin haske game da yadda jadawalin tafiyar tasa zai kasance.
Lamarin na zuwa ne bayan kashe ɗaya daga cikin jagororin kungiyar Hamas, Saleh al-Arouri, a Beirut, abin da ya sa ƙungiyar Hezbollah ta ce "za ta mayar da martani".
Isra'ila ba ta tabbatar ko musanta hannunta a harin ba, sai dai wani jami'i ya ce hari ne kan shugabancin Hamas.
- Ya kamata a daina ci da gumin 'yan Afirka - Blinken






