Morocco ta ƙwace tan 1.4 na hodar iblis da aka boye cikin ayaba

Asalin hoton, Morocco General Directorate for National Security (DGSN)/X
Ƴan sanda a Morocco sun ƙwace tan 1.488 na hodar iblis a wani samamen haɗin gwiwa da jami'an tsaron Spaniya.
An gano hodar iblis din ne ɓoye cikin kwalayen ayaba da aka maƙara su cikin kwantenar kaya ta jirgin ruwa daya taho daga kudancin Amurka zuwa Turkiyya.
An yi kamen ne a ranar Talata a tashar jirgin ruwa ta Tanger Med a arewacin Morocco.
Mahukuntan Moroccon sun ce suna zargin an shigo da hodar iblis ɗin ne a wani yunƙuri na safarar miyagun kwayoyin zuwa ƙasashen duniya amma har yanzu suna gudanar da bincike.
Lamarin ya faru ne kwana ɗaya bayan mahukunta sun ƙwace hodar iblis mai nauyin kilo 363 daga wata babbar mota da ke ƙoƙarin shiga Morocco ta iyakar ƙasar da Mauritania.
An gano cewa ƙasar da ke arewacin Afrika ita ce babbar hanyar da ake amfani da ita wajen safarar miyagun ƙwayoyi daga kudancin Amurka zuwa Turai.
- 'Kowane dare sai na yi mugayen mafarkai kan girgizar-ƙasa'
- Malamar da girgizar ƙasa ta halaka dukkanin ɗalibanta a Moroko




