Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba, Habiba Adamu and Badariyya Tijjani Kalarawi
Mutum biyar sun yi ɓatan dabo daga jirgin da ke gadin gaɓar teku – rahotanni
Mun ruwaito cewa jami'ai sun yi tunanin jirgin da ya kama da wuta ya yi taho mu gama ne da wani jirgin Japan da ke gadin gaɓar teku.
A yanzu, kafofin yaɗa labaran TBS da NHK sun ce mutum guda da ke cikin jirgin da ke gadin gaɓar teku ya samu tsira yayin da sauran mutum biyar kuma ba a san inda suke ba.
Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani.
Abin da muka sani zuwa yanzu
Kimanin awa ɗaya kenan tun samun hotunan farko daga Filin Jirgin Saman Haneda na Tokyo game da jirgin saman fasinja na kamfanin Japan Airlines da ya kama da wuta.
Nan ga abin da muka sani zuwa yanzu:
Dukkan mutanen da ke cikin jirgin sama su 379 - fasinjoji da ma'aikatansa - an kwashe su cikin aminci, a cewar kamfanin sufurin jirgin sama na Japan Airlines
An yi imani jirgin mai lamba 516 ya yi karo ne da jirgin tsaron gaɓar tekun Japan a lokacin da yake sauka. Rahotannin kafofin yaɗa labarai sun ce mutum ɗaya da ke cikin jirgin jami'an tsaron gaɓar tekun ya kuɓuta, yayin da har yanzu ba a san inda sauran mutum biyar suka shiga ba
Bidiyo da hotunan da aka wallafa a intanet sun nuna cewa jirgin saman kamfanin Japan Airlines ya kama da wuta a kan titin sauka da tashi, yayin da hotuna daga cikin jirgin suke nuna hayaƙi ya turnuƙe fasinjoji
Jirgin saman ya tashi ne daga Sapparo a tsaunin Hokkaido, da ke arewacin Japan, kuma ya kamata a ce ya sauka a filin jirgin saman Haneda kafin ƙarfe 18:00 agogon yankin (09:00 GMT)
An dakatar da dukkan sufurin jiragen sama a Filin Jirgin Sman Haneda
Jirgin tsaron gaɓar teku na hanyar kai agaji ne inda aka yi girgizar ƙasa
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce jirgin da ke gadin gaɓar teku yana kan hanyar zuwa filin jirgin saman Niigata domin kai kayan agaji zuwa yankin Noto Peninsula da girgizar ƙasa ta shafa.
Ga hoton da ke nuna yadda jirgin gaba ɗaya ya kama da wuta
Mun kuma samu wnai hoto, ga shi nan a ƙasa daga wurin gobarar, wanda yake nuna irin ɓarnar da wuta ta yi wa jirgin saman na Japan:
Asalin hoton, Reuters
Yadda fasinjojin jirgin suka kuɓuta
Fasinjojin jirgin kamfanin Japan Airlines da ya kama da wuta sun samu tsira ne ta benen roba da ake hurawa.
Hotuna daga filin jirgin saman Haneda da ke Tokyo sun nuna yadda fasinjojin ke guduwa daga jirgin da ke ci da wuta.
Har yanzu jami'ai suna ƙoƙarin kashe wutar inda bayanai ke cewa wuta ta kusa cinye jirgin gaba ɗayansa.
Labarai da dumi-dumi, An kuɓutar da fasinjoji kusan 400 da ke cikin jirgin – Japan Airlines
Japan Airlines ya ce an kuɓutar da duka fasinjoji 379 da matuƙan jirgin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters da NHK suka ruwaito.
Bidiyo kai tsaye ya nuna jirgin saman ya kama da wuta ganga-ganga
Mun samu hoton bidiyon jirgin saman na kamfanin Japan Airlines kai tsaye da ke nuna gobara ta kama jirgin ganga-ganga a kan titin sauka a birnin Tokyo..
Ma'aikatan kashe gobara suna aiki a kan titin jirgin, kuma mafi yawan gangar jikin jirgin ya kama da wuta, inda ake iya ganin harshen wuta da hayaƙi suna fitowa ta tagogin jirgin.
Kallin bidiyon a nan ƙasa:
Bayanan bidiyo, Kalli bidiyon jirgin saman Japan da ya kama da wuta a kan titinsa da ke Tokyo
Jirgin kamfanin Japan Airlines ya kama da wuta
Asalin hoton, Screen Grab
Bayanai sun nuna cewa wani jirgin kamfanin Japan Airlines ya kama da wuta a lokacin da yake ƙoƙarin sauka a filin jirgin sama na Haneda da ke Tokyo a ranar Talata.
Wani bidiyo daga kafar yaɗa labarai ta NHK ya nuna yadda hayaƙi ke fitowa daga tagogin jirgin saman da kuma ta ƙasansa.
An kuma ga wutar na ci har a kan titin jirgin.
Kafar yaɗa labaran ta NHK ta ruwaito hukumomi na cewa wataƙila jirgin ya yi karo ne da wani jirgin bayan ya sauka a Haneda.
Akwai fasinjoji a cikin jirgin.
Kafar ta kuma ruwaito cewa jirgin ƙirar JAL 516 ya tashi ne daga Hokkaido.
Darussan da Japan ta koya daga girgizar ƙasa
'Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma a jihar Nasarawa
Asalin hoton, Safiyanu Isa-Andaha/Facebook
Wasu 'yan bindiga waɗanda aka yi imani cewa 'yan fashin daji ne sun sace shugaban ƙaramar hukumar Akwanga, Safiyanu Isa-Andaha a jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandar jihar, DSP Ramhan Nansel ya tabbatarwa da BBC cewa suna bincike kan batun sace shugaban ƙaramar hukumar.
Rundunar ta kuma ce ta baza jami'ai domin ceto shugaban ƙaramar hukumar da kuma sauran mutanen da aka sace.
Bayanai sun nuna cewa 'yan fashin sun yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar ne da sauran wasu mutane a ƙauyen Ningo cikin daren Talata.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya kuma ambato Haruna Kassimu, mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu kuma amini ga shugaban ƙaramar hukumar yana tabbatar da rahoton.
Matsalar satar mutane domin karɓar kuɗin fansa, na ci gaba da ƙamari a jihar ta Nasarawa, wadda ta fuskanci irin hakan a kan wasu manyan jami'an gwamnati da daidaikun mutane da kuma ɗaliban jami'a a jihar.
Kasar ta kwashe tsawon shekaru tana fama da matsalar tsaro daga ƙungiyoyin masu dauke da makamai irinsu Boko Haram da ISWAP, yayin da matsalar 'yan fashin daji masu satar mutane domin karɓar kuɗin fansa ke ta'azzara.
Matsalar rashin tsaro ta fara sauƙi a jihar Katsina
Yadda ƴan bindiga ke karban haraji daga 'yan gudun hijira a Neja
Sojojin Isra'ila sun gano ramukan ƙaddamar da harin rokoki
Asalin hoton, IDF
Bayanan hoto, IDF ta nuna hotunan ramukan da ake ƙaddamar da hari da suka ce sun gano yayin samamen da suka kai
Rundunar sojin Isra'ila, IDF, ta yi iƙirarin gano wasu abubuwan fashewa da aka daddasa kusa da gaɓar tekun Gaza.
A wani samamen hadin gwiwa, sojojin Isra'ila na sama da na ƙasa da na ruwa sun kwance abubuwan fashewar kamar yadda sanarwar rundunar sojin ta bayyana.
Sojojin sun kuma kai samame kan wasu gine-gine a Khan Yunis da ke kudanci inda ake zargin Hamas ta ajiye makamanta.
Sun kuma ce sun gano wasu na'urorin haɗa makamai da ramukan ƙaddamar da hari a tsakiyar Gaza, sai dai sun lalata su.
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin na Isra'ila sun kashe "wasu masu riƙe da makamai da aka gano suna tunkarar sojojin a Jabalia da ke arewacin Gaza.
Sun kuma yi iƙirarin gano rokokin da aka saita su kusa da wata makaranta ƙarƙashin kulawar hukumar da ke agaza wa Falasɗinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke sansanin Bureji a tsakiyar yankin.
Yaƙin Gaza : Afirka ta Kudu ta kai ƙarar Isra'ila Kotun Duniya
'Yaƙin Gaza zai iya ɗaukar ƙarin watanni ana gwabzawa'
Yadda aka daɓa wa madugun ƴan adawar Koriya ta Kudu wuƙa a wuya
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Lee Jae-myung
An caka wa madugun ƴan adawar Koriya ta Kudu wuƙa a wuya a wata ziyara da ya kai birnin Busan.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da Lee Jae-myung ke jawabi ga ƴan jarida lokacin da maharin ya far masa.
Mr Lee wanda ya yi rashin nasara da tazarar ƴan ƙuri'u a zaɓen shugaban ƙasa na 2022, ya samu yanka tsayin santimita ɗaya a gefen wuyansa na hagu. Sai dai likitoci sun ce raunin da ya ji ba ya barazana ga rayuwarsa.
Maharin mai shekara 66 ya ce ya yi niyyar kashe Mr Lee ne kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya ruwaito.
Zuwa yanzu ba a iya tantance dalilinsa na kai harin ba.
Harin da aka kai ya girgiza ƙasar abin da ya sa jam'iyyun siyasa da ƴan siyasa suke ta suka har da shugaba mai ci, Yoon Suk Yeol.
Maharin ya tunkari Mr Lee ne yana neman ya sa masa hannu a takarda nan ne kuma ya matsa gaba inda ya daɓa masa wuƙa.
Ƴan sanda sun ce wuƙar ta kai tsawon santimita 18 da maharin ya ce ya siya ne ta intanet.
An dai kama maharin nan take.
Masu gabatar da ƙara za su tuhumi maharin da ƙoƙarin kisan kai, a cewar Yonhap.
Mutumin da ya ɗauki hotunan musgunawar wariyar launin fata a Afirka ta Kudu ya rasu
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Peter Magubane ya riƙa tattara musgunawar da aka yi a zamanin mulkin wariyar launin fata na Afirka ta Kudu
An yaba wa shahararren mai daukar hoto na Afrika ta Kudu kuma dan rajin yaki da nuna wariyar launin fata, Peter Magubane a kan gudunmawar da ya bayar wajen ƙwato 'yancin ƙasar, bayan rasuwarsa a ranar Litinin.
Ya mutu yana da shekara 91 a duniya.
Magubane ya dauki hoton wasu manyan abubuwan da suka faru a lokacin yaƙi da wariyar launin fata, ciki har da juyin-juya-halin Soweto na 1976, lamarin da ya kai ga kisan daruruwan dalibai bakaken fata.
Aikinsa ya janyo masa bakin jiji a wurin hukumomin wariyar launin fata, abin da ya kai ga tsare shi a kebe har tsawon kwana 586 kuma aka haramta masa daukar hoto na tsawon shekara biyar.
Ministan harkokin wasanni da al'adu na kasar, Zizi Kodwa ya yaba wa Makubane da cewa " zakakurin dan jarida ne mai daukar hoto kuma mai fafutukar samun 'yanci, wanda kuma ba tare da tsoro ba ya fito da irin zaluncin da aka yi a lokacin wariyar launin fata."
"Dr Magubane ya yi amfani da abin daukar hotonsa a matsayin wani makami na nuna kin amincewa, kuma bai taba bayar da kai ba ga masu mulkin danniya," Inji Mista Kodwa.
"Za a yi kewar hazakar Magubane da bajintarsa da kuma fitacciyar gudunmawar da ya bayar a aikin jarida," A cewar kungiyar Editoci ta kasar Afrika ta Kudu (Sanef).
Magubane ya taba zama mai daukar hoton gwarzon nan kuma jagorar neman 'yancin kai, Nelson Mandela na shekara hudu, bayan Mandelan ya fito daga gidan kurkuku a shekarar 1990.
Ƙarin hotunan da ke nuna girman ɓarnar girgizar ƙasar Japan
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Yadda gidaje suka ƙone ƙurmus a Wajima bayan da girgizar ƙasar ta janyo tashin gobara cikin dare
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Wani gini ke nan da ya rufta ta gefensa a Wajima da ke Lardin Ishikawa
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Yadda mummunar igiyar ruwa ta tsunami ta lalata gidaje a Suzu da ke Lardin Ishikawa
Yawan mutanen da suka mutu a girgizar ƙasar Japan ya karu zuwa 48
Hukumomi a Japan sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske a Japan ya ƙaru zuwa 48.
A cewar hukumomin girgizar ƙasar ta kai ƙarfin maki 7.6 kuma mutane da dama sun jikkata sakamakon ibtila'in.
Jami'ai sun ce akwai yiwuwar adadin ya ƙaru yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
Masu aikin ceton na ta faɗi tashin zaƙulo masu sauran numfashi daga ɓuraguzon gine-ginen da suka rushe sai dai masu kai ɗaukin na fuskantar cikas sakamakon toshe titunan da suka lalace.
Firaministan Japan, Fumio Kishida ya ce "muna ƙoƙarin lalubo mutanen da girgizar ta shafa kafin lokaci ya ƙure mana."
Ya ƙara da cewa wasu masu aikin agajin na fuskantar ƙalubale wajen kai wa zuwa yankin Noto Peninsula.
Al'ummar yankin sun yi fama da matsanancin sanyi cikin dare saboda rashin wutar lantarki.
Akasarin birane suna cikin matsalar rashin wuta.
Assalamu Alaikum!
Jama'a, assalamu alaikum, barkan mu da hantsi. Da fatan mun wayi gari lafiya a wannan rana ta Talata.
Kamar yadda aka saba, za mu kawo muku labarai da rahotanni game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran ƙasashe maƙwabta.
Da fatan za ku ci gaba da bibiyar mu har zuwa lokacin da za mu rufe shafin na Kai Tsaye.
Akwai wasu ƙarin labarai da ma bidiyo a shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da X da kuma Instangram.