Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa and Badariyya Tijjani Kalarawi

  1. Hotunan bikin sabuwar shekara daga faɗin duniya

    Yayin da muka shiga sabuwar shekara, al'ummomi a faɗin duniya na ci gaba da shagulgulan ganin wata sabuwar shekara da a raye.

    Ga wasu hotunan mutane daga sassan duniya da ke bikin baraba da shiga sabuwar shekara.

    Rio de Janeiro

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Tartsatsin wuta ya haske sararin samaniyar birnin Rio de Janeiro a gaban mutum-mutumin Yesu Kiristi da ake kira Christ the Redeemer da ke gaɓar tekun Copacabana a lokacin bukukuwan shiga sabuwar shekara
    southern Spain

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Lorena, mai shekara 29, da Alex Jaunsaras, ɗan shekara 28, sun caɓa ado da tufafin jaruman wasu fina-finai kamar Harry Potter don bikin Sabuwar Shekara a Coin, kusa da birnin Malaga, a kudancin ƙasar Sifaniya
    alms-giving ceremony

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Malaman addinin Buddah yayin bikin bayar da sadaka na safiya a wani ɓangare na shagulgulan sabuwar shekara a wurin ibada na Wat Phra Dhammakaya Temple da ke cikin lardin Pathum Thani, na ƙasar Thailand
  2. Maraba da sabuwar shekara

    Barkanmu da safiya, sannunmu da shiga sabuwar shekara ta 2024.

    Allah ya sa ta kasance alheri a gare mu gaba ɗaya.

    Kamar kullum yau ma za mu kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Mukhtari Adamu Bawa ke yi muku lale maraba.