Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo labaran abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya daban-daban.

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa, Nabeela Mukhtar Uba, Badariyya Tijjani Kalarawi and Ahmad Tijjani Bawage

  1. An kama wata matashiya bisa zargin harbe ɗan sanda a jihar Imo

    Rundunar ƴan sanda a jihar Imo ta tabbatar da mutuwar wani jami'inta Cosmos Ugwu sakamakon harbin da da budurwarsa ta yi masa.

    Budurwar ta harbi Ugwu ranar Talatar da ta gabata. Hukumomi sun bayyana sunanta da Amanda Uchechi Ugo, ƴar asalin ƙaramar hukumar Ahiazu Mbaise wadda shekarunta 23.

    Jaridar Punch ta ruwaito daga majiyoyi masu tushe cewa lamarin ya faru a ofishin rundunar da ke Ezinihitte da yammacin ranar rabon kyaututtuka da ake kira Boxing Day a Turancin Ingilishi.

    Jami'an da ke aiki a ranar sun ce sun ji harbin bindiga sau uku daga ɗakin marigayin.

    "Lokacin da ƴan sanda suka garzaya zuwa ɗakin domin ganin abin da ke faruwa, sai suka ga jami'in mai muƙamin kofur kwance cikin jini.

    Wata majiya ta shaida wa jaridar The Punch cewa matashiyar ta harbe shi sau uku a ƙirji da kuma hannunsa na hagu. An garzaya da shi asibitin Evergreen a Ezinihitte, inda likita ya tabbatar ya mutu."

    A yanzu dai matar da ake zargi tana hannun ƴan sanda domin amsa tambayoyi da kuma yiwuwar gurfanarwa a kotu.

    Da aka tuntuɓe shi, kakakin rundunar ƴan sanda ta jihar Imo, Henry Okoye ya tabbatar da faruwar al'amarin inda ya ce ƴan sanda suna duk mai yiwuwa domin duba abin da ya faru.

  2. An ɗage tattaunawar zaman lafiya kan yaƙin Sudan

    Masu shiga tsakani na ƙasashen waje sun shafe makonni suna ƙoƙarin ganin Janar-Janar da ke jagorantar yaƙi a Sudan sun hau teburin tattaunawa da juna.

    Ana fatan zama kan teburin sulhu tsakanin jagoran gwamnatin Sudan Abdel Fatta al-Burhan da na mayaƙan ISF Muhammad Hamdan Dagalo da aka fi sani da Hemeti za ta taimaka wajen dawo da zaman lafiya a ƙasar, sai dai gayyar ta watse tun kafin zaman na yau a ƙasar Djibouti.

    A karon farko tun bayan ɓarkewar yaƙin a watan Afirilun shekarar nan, Janar Mohamed Hamdan Dagalo ya fice daga ƙasar Sudan zuwa Uganda.

    A yanzu dai an sake sanya farkon watan Janairun 2024, domin ganawar tsoffin abokan biyu da mulki ya sanya suka rikiɗe abokan gaba.

    A wani ɓangaren kuma, yaƙin da ɓangarorin da ke marawa al-Burhan da Hemeti ke yi ya sake jefa Sudan cikin mawuyacin hali da kwararar ƴan gudun hijira kuma Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin lamarin na ƙara munana.

  3. Sojojin Isra'ila sun yi barazanar kawar da Hezbolla ta Lebanon

    Wani mamba a majalisar ministocin yaƙin Isra'ila ya yi gargaɗin cewa sojoji za su ɗauki matakin kawar da ƙungiyar Hezbullah daga kan iyakar ƙasar da Lebanon idan har ƙungiyar ba ta daina kai hari cikin Isra'ila ba.

    Benny Gantz ya ce lokacin sasantawa na ƙurewa, kuma dakarun tsaron ƙasar na IDF za su sa ƙafar wando ɗaya da ƙungiyar idan duniya ba ta taka mata birki ba.

    Wakiliyar BBC ta ce musayar wuta tsakanin mayaƙan Hezbollah da dakarun Isra'ila na ƙaruwa, tun ɓarkewar yaƙi tsakaninsu a ranar bakwai ga watan Oktoba.

    Sai dai ta ce babu wanda ke fatan abubuwa su lalace fiye da hakan, ko ma fatan maimaita abin da ya faru a shekarar 2006.

    Ita dai ƙungiyar Hezbollah ta harba ɗaruruwan rokoki cikin Isra'ila tun bayan fara yaƙin, lamarin da ya sa Isra'ilar ta kwashe 'yan ƙasarta da ke zaune a iyakar arewaci saboda fargabar hare-haren.

  4. Amurka ta sake aika wa Ukraine tallafin kayan yaƙi na dala miliyan 250

    Amurka ta aike da ƙarin dala miliyan ɗari biyu da hamsin na makamai da kayan yaƙi ga Ukraine, a matsayin kashi na ƙarshe da yake na tallafin da baya buƙatar amincewar majalisar wakilan ƙasar.

    Shugaba Biden ya buƙaci Majalisa da ta amince da sabon ƙunshin da ke gabanta, da ya kai dala biliyan sittin da ɗaya, amma ‘yan jam'iyyar Republican sun ƙi amincewa da hakan, kan zargin shugaban na neman mayar da Amurka tamkar 'yar sandar duniya.

    Sakataren harkokin wajen ƙasar Antony Blinken ya ce ya zama wajibi majalisar dokokin ƙasar ta ɗauki mataki nan ba da jimawa ba, don ciyar da muradun tsaron kasar ta hanyar taimaka wa Ukraine wajen kare kanta daga mamayar Rasha.

  5. Najeriya ta ci tarar kamfanin taba sigari na British American Tobacco dala miliyan 110

    Gwamnatin Najeriya ta ci tarar kamfanin taba sigari na Birtaniya mai suna British American Tobacco da sauran rassan kamfanin dala miliyan 110.

    Hukumar kare haƙƙin masu sayen kaya ta Najeriya ce ta bayyana cin tarar a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce an ɗauki matakin ne saboda zargin keta dokar hukumar da dokar taƙaita harkokin taba sigari ta ƙasa.

    Hukumar ta ƙara da cewa ya zama dole kamfanin ya mutunta dokoki sannan kuma za a riƙa bibiyar ayyukansa tsawon wata 24, kuma ya bayar da tabbaci a rubuce na kiyaye dokoki da wayar da kai game da kare lafiyar al'umma da kuma rage taba sigari.

    "Domin samun masu kamfanin su cika ƙa'idoji ƙarƙashin dokar izini, hukumar ta janye tuhume-tuhumen da ake yi wa kamfanin da kuma wani ma'aikacinsa dangane da yunƙurin hana gudanar da bincike a kamfanin da kuma rashin ba da haɗin kai domin aiwatar da aikin, kamar yadda hukumar ta ce.

    A cewar hukumar, ta ƙaddamar da bincike tare da ƙwace wasu kayayyaki bayan samun izinin watan babbar kotun tarayya a rassan kamfanin na BAT a ranar 25 ga watan Janairu.

    Hukumar ta bayyana cewa ta tattara ta kuma samu isasshiyar hujja daga binciken ƙwaƙwaf da aka yi na kafofin sadarwa da sauran bayanai da aka tattaro sakamakon binciken da kuma shaidun da aka gano daga sahihan majiyoyi yayi da kuma bayan binciken.

    Hukumar ta ƙara da cewa a shirye take ta inganta da kuma tabbatar da tsaftace kasuwanni domin kare masu sayen kayayyaki.

    • Abin da ya sa dole masu zama da mashaya sigari su damu da lafiyarsu
    • 'Shan taba sigari ya fi ɓarna a ƙasa huɗu'
  6. Barka da hantsi!

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, assalamu alaikum. Barkanmu da wayar gari a wannan rana ta Alhamis.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa tare da mu domin karanta labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashe maƙwabta.

    Kuna iya garzayawa shafukanmu na sada zumunta kamar Fesbuk da X da kuma Instangram inda a nan ma akwai ƙarin wasu labaran har ma da bidiyo da za ku iya kalla.