Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo labaran abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya daban-daban.

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa, Nabeela Mukhtar Uba, Badariyya Tijjani Kalarawi and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Masar ta fito da wani tsari mai rassa uku don kawo karshen yaƙin Isra'ila da Hamas

    Masar ta ce ta fito da wani tsari mai rassa uku da ka iya kawo karshen yaƙin Isra'ila da Hamas, kuma tana dakon martanin ɓangarorin biyu.

    Rahotanni na cewa tsarin ya kunshi tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni da sakin waɗanda aka yi garkuwa da su daga kowanne ɓangare.

    Yana kuma kunshe da taswirar yadda za a jagoranci Gaza bayan yakin.

    Masar ta ce za ta saki cikakkun bayanai bayan ta ji amsoshi daga Isra'ila da kuma Hamas.

  2. Gwamnatin Zamfara tayi wa ma’aikata kyautan albashi na wata ɗaya

    Gwamnatin Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara ya yi wa ma'aikatan jihar kyautan albashi na wata ɗaya.

    Wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan jihar kan harkokin yaɗa labarai, Sulaiman Bala Idris ya fitar, gwamna Dauda ya ce bai wa ma'aikatan ƙyautan albashin ne ƙara musu kwarin gwiwar yin aiki tukuru.

    Dauda ya ce gwamnatinsa na da zimmar ci gaba da kula da walwalar ma'aikata a fadin jihar.

    "Gwamna ya bai wa ma'aikata kyautar albashin ne domin su yi hutun karshen shekara cikin jin daɗi," in ji sanarwar.

    Sanarwar ta kuma ce wannan shi ne karon farko da ake yi wa ma'aikata kyautar albashi a jihar ta Zamfara.

  3. Tankokin yaƙin Isra'ila na ƙara kutsawa tsakiyar Zirin Gaza

    Tankokin yaƙin Isra'ila sun ƙara kutsawa cikin garin Bureji da ke tsakiyar Zirin Gaza, a daidai lokacin da dubban fararen hula na Falasdinawa ke ci gaba da guje wa lugudan wuta na kwanaki da aka kwashe ana yi.

    Hukumar kula da 'yan gudun hijra ta MDD ta ce mutum dubu 150 ne da suka haɗa da mata da yara da tsofaffi, aka tilasta musu barin garuruwansu da sansanoninsu da ke tsakiyar Gaza.

    Isra'ila ta ce tana iya ƙoƙarinta wajen ganin ta kare fararen hula, yayin da take ci gaba da kai samamen neman mayakan Hamas.

    Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce an kashe fiye da Falasɗinawa 200 a sa'o'i 24 da suka gabata, wanda hakan ke nuni da cewa an kashe kaso ɗaya na yawan al'ummar Gaza kafin fara yaƙi.

  4. Za mu ci gaba da sayar da sumunti 3,500 - BUA

    Shugaban kamfanin BUA, AbdusSamad Rabi'u, ya ce kamfanin zai cika alkawarinsa na ci gaba da sayar da sumunti kan farashin 3,500 daga watan Janairun 2024.

    Ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da manema labarai bayan ziyara da ya kai wa shugaba Bola Tinubu a gidansa da ke Legas ranar Alhamis.

    Ya ce kamfanin zai kuma tabbatar da cewa sumuntin ya wadata da kuma sauki ga kwastomominsa duk da kalubale da ake ciki.

    "Mun saka farashi sumuntin kan naira 3,500 a kan kowane buhu. Za mu duba kuɗin haraji da kuma nisan yankin da za a kai sumunti.

    "Kamar yadda ka sani, muna da kamfanoni guda biyu; ɗaya a Edo, yayin da ɗaya muke yake jihar Sokoto. Alal misali, idan kana son mu kai maka sumunti daga Sokoto zuwa Legas ko Adamawa ko kuma Maiduguri, idan ka duba yana da nisan gaske," in ji BUA.

    Ya ce duk da cewa idan aka yi la'akari da nisa ko kuma wurin da za a kai sumunti farashin zai iya tashi, amma kamfanin zai cika alkawarinsa inda zai ci gaba da sayarwa a kan 3,500.

    Rabiu ya ƙara da cewa za a kaddamar da kamfanin sumunti da ke Sokoto a watan Janairun 2024, wanda hakan zai sa ya faɗaɗa kasuwancinsa a faɗin ƙasar.

    Ya ce ya kai wa shugaban ƙasar ziyara ne domin yi masa gaisuwar Kirsimeti da kuma na sabon shekara.

  5. Isra'ila ta ce an kashe sojojinta sama da 500 tun fara yaƙi a Gaza

    Isra'ila ta ce sama da sojojinta 500 aka kashe tun soma yaƙi da Hamas ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar rundunar sojojin ƙasar.

    Ta ƙara da cewa sama da dakaru 160 ne kuma aka kashe tun da ta kaddamar da farmaki ta ƙasa cikin Gaza a karshen watan Oktoba.

    An jikkata wasu sojoji 900 tun bayan kaddamar da yaƙi kan Gaza - inda sojoji ke ci gaba da artabu da mayakan Hamas.

    Isra'ila ta ce ba za ta daina kai harin ramuwar gayya ba a Gaza har sai ta kawar da ƙungiyar Hamas.

    Akalla mutum 1,200 aka kashe lokacin da Hamas ta kai kazamin hari cikin Isra'ila ranar 7 ga Oktoba, tare da yin garkuwa da 240.

  6. An kashe Falasɗinawa 50 a luguden wutar da Isra'ila ta kai sassan Gaza

    Ma'aikatar Lafiyar Hamas a Gaza ta ce mutum 50 aka kashe cikin luguden wutar da aka shafe dare ana yi a yankunan Beit da Lahia da Khan Younis da Maghazi.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta daɗe tana kai samame a yankunan birnin Gaza.

    Shugaban hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce yanayin da ake ciki a Gaɓar yamma da kogin Jordan yana ta'azzara inda ya buƙaci Isra'ila ta kawo ƙarshen kashe-kashen da take yi wa al'ummar Falasɗinawa.

    Wani ministan Isra'ila ya ce ƙasar za ta murƙushe ƙungiyar Hezbollah daga kan iyakarta da Lebanon idan ta ci gaba da kai hare-hare kan Isra'ila.

    A farkon makon nan Hezbollah ta zafafa amfani da rokoki da jirage marasa matuƙi maƙare da makamai wajen kai hare-hare sai dai jiragen yaƙin Isra'ila sun yi hanzarin mayar da martani.

    A wani labarin kuma, ƙungiyar agaji ta Palestine Red Crescent Society ta ce an kashe mutum 10 a wani hari da aka kai kusa da asibitin al-Amal da ke Khan Younis, wani birni a kudancin zirin Gaza.

    A wani saƙo a shafin X, ƙungiyar ta ce an kai hare-hare uku a kewayen asibitin cikin ƙasa da sa'a ɗaya.

    An kuma raunata mutane yayin luguden wutar a yankin jiya Laraba.

  7. Hotuna: MDD ta ce kashi 40 na al'ummar Gaza na cikin barazanar faɗawa yunwa

    Hukumar kula da Falasɗinawa ƴan gudun hijira ta MDD ta ce babu isasshen abinci a Zirin Gaza.

    "Kowace rana mutane na ƙoƙarin ganin yadda za su rayu, inda suke neman abinci da ruwa," in ji Thomas White, darektan hukumar ta UNRWA.

    Hukumar ta ƙara da cewa kashi 40 na al'ummar Gaza na cikin barazanar faɗawa yunwa kuma ana buƙatar ƙarin agaji.

  8. Tinubu ya karɓi gwarzuwar kwallon kafa ta mata a Afrika Asisat Oshoala

    Shugaba Bola Tinubu da mai ɗakinsa Remi Tinubu sun karɓi gwarzuwar kwallon kafa ta mata a Afrika Asisat Oshoala.

    Sun karɓi Asisat ne a gidansu da ke birnin Legas.

    Oshoala ta sake lashe kyautar gwarzuwar kwallon kafa ta mata a Afrika na 2023 ne bayan doke waɗanda ta yi takara da su da suka haɗa da Thembi Kgatlana (Afirka ta Kudu, Racing Louisville) da kuma Barbara Banda (Zambia, Shanghai Shengli).

    Wannan shi ne karo na shida da take lashe kyautar.

  9. Bam ya tashi a Maiduguri

    Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani bam ya tashi tare da hallaka mutum ɗaya.

    Wani jami'in Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Bashir Garga ya tabbatarwa da BBC faruwar lamarin.

    Ya ce bam ɗin ya tashi ne da misalin karfe 10 na safiyar yau Alhamis.

    An ɗauki tsawon lokaci ba a samu tashin bam a birnin na Maiduguri ba, wanda ya yi ƙaurin suna wajen fuskantar hare-haren Boko Haram a shekarun baya.

  10. Dubban matasan Isra'ila sun yi maci don buƙatar sakin ƴan ƙasar da ake garkuwa da su

    Dubban matasan Isra'ila na gudanar da maci don buƙatar a saki ƴan ƙasar da ake garkuwa da su a Gaza.

    Waɗanda suka shiga macin za su bi ta Birnin Kudus kuma za su kai har zuwa majalisar dokokin ƙasar.

    Sun fara macin ne daga wani dandali da ke birnin Tel Aviv a ranar Lahadi.

    Matasan na yin kira da a cimma sabuwar yarjejeniya domin ba da damar sakin sauran ƴan ƙasar da ake ci gaba da rike da su a Gaza.

    Isra'ila ta ce ba ta san halin da mutum 129 da aka yi garkuwa da su ke ciki ba, waɗanda aka ɗauka zuwa Gaza lokacin harin Hamas ranar 7 ga watan Oktoba.

  11. Batutuwa mafi jan hankali a shafukan sada zumunta a 2023

  12. Kulob ko ƙasa? Tsaka mai wuya kan Gasar cin Kofin Afirka

  13. Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar da rahoton keta haƙƙin ɗan'adam a Gabar Yamma

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci Isra'ila ta kawo ƙarshen abin da ta kira “haramtattun kashe-kashen” da take yi wa Falasɗinawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan.

    Babban jami'in kare 'yancin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya, Volker Turk, ya ce ya shiga tsananin damuwa saboda salon dabarun yaƙi da sojojin ƙasar suke amfani da su, da amfani da fin ƙarfi da kuma taƙaita zirga-zirga.

    Rahoton wanda aka fitar yau, ya kuma zargi Isra'ila da aikata:

    • Kamen kan mai uwa da wabi da tsare mutane da rahotannin azabtarwa da sauran cin zarafi daga dakarin Isra'ila da ƙara nuna damuwa game da hukunci kan kowa da kowa
    • Ƙaruwar hare-hare ninkin-ba-ninki daga 'yan kama-wuri-zauna masu makamai wanda kan haddasa korar ɗumbin Falasɗinawa daga garuruwansu
    • Nuna bambanci wajen taƙaita zirga-zirga, wanda ke shafar rayuwar yau da kullum da kassara tattalin arziƙin jama'ar yanki.

    Da yake jawabi game da rahoton da aka fitar, Volker Turk ya ce abubuwan da suka gano suna da "tayar da hankali matuƙa", kuma duk da yake keta 'yancin ɗan'adam a lokacin yaƙi ba sabon abu ba ne, "tsananin tashin hankali da matakan murƙushewar, wani abu ne da ba a taɓa gani ba a 'yan shekarun nan." Isra'ila ba ta yi martani game da rahoton ba nan take.

    Isra'ila ta ce ayyukan da take gudanarwa a Gabar Yamma da Kogin Jordan na da nufin yin riga-kafi da kuma shawo kan barazanar tsaro.

  14. An ji jiniyar harin rokoki a garuruwan kudancin Isra'ila

    An ji jiniyar harin rokoki a garuruwan kudancin Isra'ila kusa da iyaka da Gaza a ranar Alhamis.

    Hamas da ƙungiyar Islamic Jihad da kuma wasu ƙungiyoyi sun sha kai harin rokoki akai akai zuwa cikin Isra'ila.

    Na'urar kariya na makami masu linzami na Isra'ila Iron Dome, ya kakkaɓe da yawa daga cikin rokoki da aka harba zuwa ƙasar, duk da haka an samu waɗanda suka jikkata da kuma wuraren da suka lalace.

    A wani lamari tun da farko, an ji jiniyar a yankin Krayot da ke arewacin Isra'ila.

    Ma'aikatar tsaron Isra'ila ta ce martani ne kan wani jirgi maras matuki da ya kawo hari daga Lebanon zuwa yankin Isra'ila, amma an samu damar kakkaɓe shi.

  15. Ƴan sanda na neman waɗanda suka yi wa wani yaro mummunan kisan gilla a Zariya

    Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da gano gawar wani yaro ɗan shekara takwas, wandaaka ba da rahotonsa ɓatansa a baya-bayan nan lokacin da suka je ziyara unguwar Kwanar Ɗangoma a cikin birnin Zaria.

    Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kaduna, ASP Mansur Hassan ya ce an kira jami'ansu ne bayan ganin gawar yaron a yashe kuma sun ga jini a kafofin jikinsa kamar idanu da dubura da sauran sassa.

    A ranar Laraba ne, aka fara ganin cigiyar Ibrahim Muntaqa Mohammed, wanda wasu ke cewa yana da lalura irin ta ƙwaƙwalwa da ake kira autistic. Kuma an ce an yi masa ganin ƙarshe lokacin da ya bar gida da misalin ƙarfe 4 na yamma a Zariya.

    Ya dai musanta raɗe-raɗin cewa an ƙwaƙwale idanuwan yaron, amma dai ya shakka akwai jini a kafar idanuwan.

    ASP Mansur Hassan ya ce daga bayanan da suka samu yaron sun je Zariya ne ziyara daga Kano kafin wannan ƙaddara ta faru da shi.

    A cewarsa, sun baza koma domin samun bayanan da za su taimaka musu ga kama mutanen da suka tafka wannan aika-aika.

    Ya dai ce zuwa yanzu ba su kai ga kama kowa ba, sai dai tuni suka miƙa gawar Ibrahim Mohammed ga iyayensa domin yi masa sutura.

    • Yara 10 da aka yi wa kisan gilla a Najeriya
    • Yadda matasa suka sace tare da kashe wani yaro a Kano
  16. Ana makokin kwana uku a Ondo kan mutuwar Akeredolu

    Gwamnatin jihar Ondo ta ayyana makokin kwana uku domin alhinin mutuwar Rotimi Akeredolu wanda ya rasu da sanyin safiyar jiya, Laraba.

    Mutuwar Akeredolu ta sa aka rantsar da mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa a matsayin gwamna.

    Sabon gwamnan ya ba da umarnin sassauto da tutocin Najeriya a sassan jihar domin jimamin mutuwar marigayin.

    Matakin na ƙunshe ne cikin sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ebenezer Adeniyan ya fitar.

    Akeredolu ya rasu yana da shekara 67, bayan ya shafe lokaci yana fama da cutar kansar jini da ta mafitsara.

    • Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya rasu
    • An rantsar da Aiyedatiwa a matsayin cikakken gwamnan Ondo
  17. An ɗaure ƴan fafutukar Hong Kong shekara shida a kurkuku kan kitsa harin ta'addanci

    An yanke wa wasu masu fafutuka uku ƴan Hong Kong hukuncin shekara shida a gidan yari saboda samun su da hannu a kitsa wani hari da aka daƙile kan gine-ginen gwamnati.

    Mutanen uku tun da farko an tuhume su da "haɗa baki wajen aikata ta'addanci" ƙarƙashin dokar tsaro ta ƙasa.

    Suna daga cikin ƴan ƙungiyar Returning Vailant da ta kitsa lamarin a 2021 bayan zanga-zangar neman rajin kafa dimokraɗiyya.

    An kama su ne a Yulin 2021, kafin su aiwatar da ƙudirinsu.

    Kotun ta samu bayanai cewa Ho Yu-wang da Kwok Man-hei da Cheung Ho-yeung sun tsara su haɗa bama-bamai ta hanyar amfani da abin fashewa TATP tare da dasa su a gine-ginen gwamnati da dama har da ofisoshin gwamnati da ofisoshin ƴan sanda da kotuna da kuma tashoshin jiragen ƙasa.

    Sun yi niyyar wanzar da ƙudirinsu tsakanin 1 ga watan Afrilu da 5 ga watan Yulin 2021 amma aka kama su kafin su haɗa bama-baman, kamar yadda kotun ta samu bayanai.

    Masu gabatar da ƙara sun ce Ho wanda yake shekara 17 lokacin da ya shiga hannu shi ne ke da "alhakin haɗa abubuwan fashewar".

    Ya amsa laifin tuhumar ta'addanci inda kuma aka yanke masa shekara shida a gidan yari sannan kuma kotu ta ayyana shi a matsayin jagoran ƙungiyar.

    Cheng mai shekara 23, shi ma an yanke masa shekara shida a kurkuku yayin da Kwok ɗan shekara 21 aka ba shi hukuncin wata 30 a gidan yari. Dukkansu sun amsa laifin "haɗa baki domin ta da abubuwan fashewa".

    Alƙalin babbar kotu Alex Lee ya ce ya amince cewa yamutsin da aka samu yayin gangamin masu rajin a kafa dimokraɗiyya na iya sauya ra'ayin nutsattsu su zama fitinannu", a cewar rahoton Reuters.

    A watan Mayu aka yanke wa mutum huɗu hukunci saboda hannun da suke da shi.

  18. 'Mutanen da suka mutu a hare-haren Filato sun kai 195'

    Shugaban ƙaramar hukumar Bokkos a Filato ya ce mutum 148 aka kashe a hare-haren da ƴan bindiga suka kai a jajiberin kirsimeti a yankin.

    Hakan in ji jaridar Vanguard, na zuwa daidai lokacin da adadin mutanen da suka mutu sanadin hare-haren a ƙananan hukumomi uku na jihar ya kai 195.

    Daga cikin adadin, an kashe mutum 148 a ƙaramar hukumar Bokkos dai 19 a ƙaramar hukumar Mangu da wasu 27 a Barkin Ladi.

    An kuma ƙona gidaje 1,290 a Bokkos sai gida ɗaya a Mangu da shi ma aka ƙona sai dai har yanzu ba a kai ga sanin yawan gidajen da aka ƙona ba a Barkin Ladi.

    Fiye da mutum 10,000 ne suka ɗaiɗaita sakamakon hare-haren na ƴan bindiga a yankunan Bokkos da Barkin Ladi.

    • An kashe 'fiye da mutum 140' a wani hari a Filato
    • Ana bincike kan 'likitan' da ake zargi da cire wa marasa lafiya ƙoda a Jos
  19. Mutane za su ƙara shiga wahala a wasu yankunan arewacin Najeriya - Bankin Duniya

    Bankin Duniya ya yi hasashen za a ci gaba da samun taɓarɓarewar matsalar tsaro da rikicin ƴan bindiga da matsin rayuwa a ƙananan hukumomin jihohin Borno da Kaduna da Katsina da Sokoto da Yobe da Zamfara da kuma Adamawa har zuwa watan Mayun 2024.

    Hasashen bankin na zuwa ne daidai lokacin da ya bayyana cewa rashin nagartattun tsare-tsaren tattalin arziki sun haifar da raguwar samun amfanin gona a Najeriya.

    Wannan dai zai shafi batun samar da hatsi a ƙasar. Bankin duniyar ya bayyana haka ne a rahoton baya-bayan nan da ya fitar game da samun wadataccen abinci.

    Ƙiyasin hatsin da ake sa ran nomawa a Afirka ta Yamma da ta Tsakiya a bana ya kai sama da tan miliyan 76, an samu ragin kashi biyu cikin 100 daga kakar da ta gabata, sai dai an samu ƙarin kashi uku cikin 100 na matsakaicin adadin a cikin shekara biyar.

    Ana sa ran koma-bayan zai fi tasiri ne a ƙasashen Chadi da Mali da Nijar da kuma Najeriya.

    A rahoton na baya-bayan nan, bankin duniyar ya ce a tsakanin watan Agusta da Nuwamba, ƙasashe da dama marasa ƙarfin tattalin arziki sun yi fama da hauhawar farashi.

  20. Gobarar tankar mai ta halaka mutum 40 a Liberia

    Kafar yada labaran Liberia ta sanar da mutuwar mutane 40, wasu sama da 30 sun jikkata a lokacin da wata tankar mai ta kama da wuta, kamar yadda wani jami'in lafiya ya shaida.

    Francis Kateh, ya ce tankar man ta yi alkantara daga bisani ta fada wani rami a kan titin Totota da ke yankin Lower Bong, mai nisan kilomita 130 daga babban birnin kasar Monrovia, kuma mutane da dama sun jikkata.

    Kateh ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP zai yi wuya a gano musabbabin hatsarin, sakamakon yawancin wadanda suka mutu sun kone kurmus sai tokarsu.

    ''Tawagar jami'anmu na kan hanyar zuwa inda lamarin ya faru, za su shiga gida-gida domin duba wadanda suka bata.''

    Rahotanni sun bayyana an garzaya da gwamman mutane asibiti sakamakon mummunar kunar da suka samu, kuma Mr Kateh ya ce adadin wadanda suka mutu ka iya zarta 40 nan gaba.

    Ganau sun ce wasu daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, sun kone ko mutu ne sakamakon kokarin kwasar ganimar man fetur da ke zuba daga tankar wanda su ne suka kara hudawa domin kwasar ganimar.