An gurfanar da Hafsat 'Chuchu' a kotu bisa zargin kashe Nafi'u a Kano

Wannan shafi ne da ke kawo labaran abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya daban-daban.

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Fiye da mutum 20 sun mutu sakamakon fashewar bututun mai a Ribas

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata fashewa da ta faru bayan fasa wani bututun ɗanyen mai da ke ƙarƙashin ƙasa a ƙaramar hukumar Ogba/Egebema/Ndoni da ke jihar Ribas ta halaka aƙalla mutum 20.

    Lamarin ya faru ne a ƙarshen makon daya gabata a ƙaramar hukumar da ke zama ɗaya daga cikin cibiyoyi masu arzikin mai da iskar gas a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.

    Rahotanni na cewa an kwantar da mutanen da suka samu ƙuna a asibitoci da dama a garin.

    Zuwa yanzu, babu tabbacin abin da ya jawo fashewar da ta haddasa gobara da kuma adadin mutanen da suka mutu.

    Shugaban matasan yankin ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da matasan suke raba ɗanyen man da aka sato a jarkoki.

    Wani ɗan jarida ya tabbatar cewa gobarar ta tashi lokacin da matasan suke rige-rigen kwasar ɗanyen man daga wani bututu da ke ƙarƙashin ƙasa a lokacin da gobarar ta tashi.

    • 'Mutum 15 ne suka mutu a fashewar bututu a Lagos'
  2. Ɗan majalisa na neman a sa dokar ta-ɓaci a Kudancin Taraba kan matsalar tsaro

    Wani ɗan majalisar dattawa daga Taraba ya yi kira ga shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a yankinsa na kudancin jihar da yake wakilta saboda matsalar tsaro ta dalilin ayyukan ƴan bindiga ke ci gaba da yin ƙamari a yankin.

    Sanata David Jimkuta ya shaida wa BBC cewa sama da mutum 700 aka kashe cikin watanni shida zuwa bakwai a yankin sannan al'amarin ya shafi garuruwa 62 abin da ya tarwatsa al'ummar yankin.

    Ya ce abu ne na tashin hankali saboda "masifa da bala'i, idan kana ganin cewa kaɗan ne, gobe zai zo ya fi ƙarfinka domin mun ga abin da ya faru a Maiduguri - kamar da wasa yau an fi shekara 10 ana fafatawa."

    A cewar Sanatan, mutanen yankin kudancin Taraba yanzu sun koma kwana a makarantu, wasu a majami'u saboda rashin tsaro a yankunansu.

    "Ga hare-hare kullum, na faɗa a gaban majalisa, na kawo kuka a kan waɗanda aka yanka su, ban da waɗanda aka kashe a watan Nuwamba." in ji Sanatan.

    Ya ce bai kamata gwamnati ta bari lamarin ya ƙazance ba har sai lokaci ya ƙure.

    Ga ƙarin bayani cikin hirar da Abdou Halilou ya yi da ɗan majalisar.

    Bayanan sautiHirar Sanata David Jimkuta kan kashe-kashe a Kudancin Taraba
    • Yadda aka sace sarki da fadawansa a Taraba
    • Gashaka Gumti: Abin da ba ku sani ba game da Gandun daji mafi girma a Najeriya
  3. An kashe Falasɗinawa 241 a Gaza cikin kwana guda – Hamas

    ...

    Asalin hoton, NURPHOTO VIA GETTY IMAGES

    Ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce aƙalla mutum 241 aka kashe cikin kwana guda yayin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da kai samame a yankin.

    Shugaban Falasɗinu Mahmoud Abbas ya kira yaƙin a matsyin gagarumin laifi kan al'ummarsa.

    Shugaban rundunar sojin Isra'ila, chief Herzi Halevi ya ce yaƙin da ake da Hamas zai ci gaba har tsawon "ƙarin wasu watanni".

    Da sanyin safiyar yau Laraba an ji ƙarar abubuwan fashewa daga Zirin Gaza.

    A Gabar Yamma da Kogin Jordan kuwa, majiyoyi daga likitoci a Falasɗinu sun ce Falasɗinawa shida aka kashe a luguden wutar da Isra'ila ta shafe dare tana yi a sansanin ƴan gudun hijra na Nur Shams da ke Tulkarem.

    Ma'aikatar lafiya a Gaza ya ce mutum 382 aka raunata cikin sa'a 24 da ta gabata.

    A cewar ma'aikatar, aƙalla Falasɗinawa 20,915 aka kashe - akasari yara da mata - cikin sama da mako 11 da ake yaƙin.

    Kawo yanzu ba a iya tabbatar da iƙirarin girman ɓarnar da ɓangarorin biyu suke yi ba.

    A ranar 7 ga watan Oktoba ne aka soma yaƙin bayan da Hamas ta kai hare-hare kan yankuna cikin Isra'ila.

    An kashe wasu mutum 1,200, galibi farar hula. An kuma yi garkuwa da mutum 240 a Gaza sai dai an saki wasu daga cikinsu daga bisani.

    • Mene ne tukwicin zaman lafiya a yaƙin Isra'ila da Hamas?
    • Halin da yaran Gaza ke ciki: An raunata su kuma an kashe iyayensu
  4. Assalamu Alaikum!

    Jama'a assalamu alaikum. Barkanmu da bukukuwan ƙarshen shekara.

    Kamar kullum, a yau ma wannan shafi na kai tsaye, zai ci gaba da wallafa muku labarai da rahotanni na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da kuma sauran ƙasashen duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa tare da mu. Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da X da kuma Instagram domin kallon wasu bidiyon.