Amurka tana aiki tare da Majalisar Ɗinkin Duniya kan ƙuduri

Asalin hoton, EPA
Amurka tana "ta na aiki tukuru" kan daftarin ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya na dakatar da faɗa a Gaza, in ji jami'in majalisar tsaron ta Amurka John Kirby.
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na iya kaɗa ƙuri'a kan ƙudurin nan da 'yan sa'o'i masu zuwa. An riga an jinkirta shi sau da yawa a wannan makon.
Ana ci gaba da tattaunawa ta diflomasiyya kan abubuwan wannan ƙudiri zai ƙunsa, domin kaucewa rashin amincewa daga Amurka, inda aka ce babban abin da ke ɗaure kai shi ne na duba da kuma sa ido kan kayan agajin da ke shiga Gaza.
"Har yanzu muna aiki tare da abokanmu na Majalisar Ɗinkin Duniya game da ƙudurin da kuma kan lafazin da ya ƙunsa," Kakakin majalisar tsaron Amurka John Kirby ya shaida wa manema labarai a taron manema labarai na yau da kullun na Fadar White House.




















