Kotun ƙoli za ta sanar da ranar bayyana hukunci kan zaɓen gwamnan Kano

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba and Haruna Kakangi

  1. Amurka tana aiki tare da Majalisar Ɗinkin Duniya kan ƙuduri

    John Kirby

    Asalin hoton, EPA

    Amurka tana "ta na aiki tukuru" kan daftarin ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya na dakatar da faɗa a Gaza, in ji jami'in majalisar tsaron ta Amurka John Kirby.

    Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na iya kaɗa ƙuri'a kan ƙudurin nan da 'yan sa'o'i masu zuwa. An riga an jinkirta shi sau da yawa a wannan makon.

    Ana ci gaba da tattaunawa ta diflomasiyya kan abubuwan wannan ƙudiri zai ƙunsa, domin kaucewa rashin amincewa daga Amurka, inda aka ce babban abin da ke ɗaure kai shi ne na duba da kuma sa ido kan kayan agajin da ke shiga Gaza.

    "Har yanzu muna aiki tare da abokanmu na Majalisar Ɗinkin Duniya game da ƙudurin da kuma kan lafazin da ya ƙunsa," Kakakin majalisar tsaron Amurka John Kirby ya shaida wa manema labarai a taron manema labarai na yau da kullun na Fadar White House.

  2. Netanyahu ya ce wa 'yan Hamas 'ku miƙa wuya ko ku mutu'

    ...

    Asalin hoton, REUTERS

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce yaƙin Gaza ba zai ƙare ba har sai Isra'ila ta cimma dukkanin manufofinta.

    "Zaɓin da na bai wa Hamas abu ne mai sauƙi: mika wuya ko mutu," in ji shi. "Ba su da wani zaɓ - kuma ba za su samu -wani zabi ba. Kuma bayan mun kawar da Hamas, zan yi amfani da dukkan karfina don ganin cewa Gaza ba ta sake yin barazana ga Isra'ila ba - ko Hamastan ko Fatahstan."

    An fassara kalaman na sa ne daga sanarwar da ya fitar a harshen Hebrew.

    Hamastan da Fatahstan sun yi nuni da ƙungiyoyin Falasdinawa guda biyu: Hamas, ƙungiyar Falasdinawa da ke da iko a Gaza tun 2007 - da kuma jam'iyyar siyasa Fatah, wacce ita ce jam'iyya mai mulkin yankin yamma da gaɓar kogin Jordan kuma wanda ke mummunar adawa da Hamas.

    Har yanzu ba a san yadda yankin da mazaunanta miliyan biyu za su kasance ba bayan kawo ƙarshen yakin.

  3. Faransa ta ƙi miƙa ɗan uwan ​​tsohon shugaban Burkina Faso

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Faransa ta soke wata doka da ta ba da izinin miƙa ɗan uwan ​​tsohon shugaban Burkina Faso zuwa ƙasarsa ta haihuwa.

    Paul François Compaoré, wanda ɗan'uwansa Blaise ya kasance shugaban ƙasa daga 1987 zuwa 2014, ana zarginsa da kashe wani ɗan jarida a 1998.

    Taɓarɓarewar dangantaka tsakanin gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso da tsohuwar mulkin mallaka, Faransa, ya haifar da korar jami'an diflomasiyya - ciki har da jakadan Faransa, tare da dakatar da wasu kafafen yaɗa labaran Faransa.

    Tun da farko dai an kama wasu ma'aikatan fasaha guda huɗu na Faransa da ke ɗauke da fasfo da biza na diflomasiyya a Ouagadougou babban birnin ƙasar.

  4. Angola na shirin ficewa daga ƙungiyar OPEC

    OPEC

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin Angola ta ce za ta fice daga ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC, sakamakon taƙaddamar kason man da ake hakowa.

    Hakan ya biyo bayan shawarar da ƙungiyar OPEC ta yanke a watan jiya na ƙara rage yawan ɗanyen mai da ake fitarwa lamarin da zai rage yawan man da Angola ke fitarwa zuwa ganga miliyan 1.1 a kowace rana, wanda zai yi nuni da raguwar yawan man da ake haƙowa a ƙasar.

    Da yake sanar da matakin, ministar mai Diamantino Azevedo ya ce Angola ba ta taka wata rawar a azo-a-gani a ƙungiyar , kuma lokaci ya yi da ƙasar za ta mai da hankali kan manufofinta.

    Angola ta kasance memba a ƙungiyar OPEC tsawon shekaru 16.

  5. Sarkin Jordan ya yi gargaɗin 'mummunan sakamako' idan rikicin Gaza ya ci gaba

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sarki Abdallah na Jordan ya ce yaƙin da Isra'ila ke yi a zirin Gaza zai haifar da mummunar illa a yankin baki ɗaya.

    Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya rawaito cewa da yake magana da shugaban Faransa Emmanuel Macron, Sarkin ya ƙara da cewa dole ne duniya ta matsa ƙaimi wajen tabbatar da tsagaita wuta cikin gaggawa.

    Abdullah ya kuma yi gargadi game da tashin hankalin gabar yamma da kogin Jordan, inda yahudawa 'yan kama-wuri-zauna ka kai hare-hare kan Falasɗinawa a yankin.

    Ya kuma yi magana kan yadda ake cin mutuncin wurare masu tsarki na musulmi da kiristoci a birnin Ƙudus, lamarin da zai iya ƙara ruruta wutar rikicin.

  6. Ɗan bindiga ya harbe mutum 10 a Czech

    Buɗe wuta

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum goma ne suka mutu sannan gommai suka jikkata bayan da wani ɗan bindiga ya buɗe musu wuta a wata jami'a da ke tsakiyar Prague, babban birnin Jamhuriyar Czech, in ji ƴan sanda.

    Ƴan sanda sun ce an samu nasarar kashe ɗan bindigar, kuma ana kwashe mutane daga cikin ginin.

    A wani sako da shugaban ƙasar Petr Pavel, ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ya kaɗu matuka da jin labarin al'amarin da ya faru a Prague, inda ya kuma mika ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda aka kashe.

    Ya kuma gode wa mazauna birnin saboda bin umarnin jami'an tsaro.

    Zuwa yanzu an aika motocin ɗaukar marasa lafiya zuwa birnin domin kai ɗauki da kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.

    Czech

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Wani jami'in kai ɗaukin gaggawa rike da gadon ɗaukar marasa lafiya yayin da ya isa wajen da lamarin ya faru
    Czech

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Jami'an bayar da agaji ke shirin taimakawa waɗanda suka jikkata
  7. Matatar man Port Harcourt ta fara aiki

    ....

    Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

    A ranar Alhamis din nan ne gwamnatin Najeriya ta tabbatar da fara aiki a kamfanin tace man fetur na Fatakwal da ke jihar Ribas.

    Ta sanar da cewa, cibiyar ta fara aiki ne a ranar 20 ga watan Disamba, 2023, sakamakon kammala ɓangaren farko na gyaran da ake yi wa matatar , inda ta ƙara da cewa za a fitar da tataccen man fetur daga matatar bayan hutun Kirsimeti.

    A farkon shekarar ne dai gwamnatin ta sha alwashin cewa matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki kafin karshen shekarar 2023.

    Ci gaban yana zuwa ne bayan matatar ta kwashe shekaru ba ta aiki.

    Hudu daga cikin matatun mai na Najeriya a Fatakwal da Warri, da Kaduna suna da karfin sarrafa ganga 445,000 a kowace rana. Amma an rufe su duka a 2019.

  8. Dole ne masu amfani da Tekun Maliya su kare shi - Masar

    Bahar Rum

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Tekun ya kasance hanya mai muhimmanci ga ƙasashe da dama da ke yin hada-hada a ciki da kuma wajen Gabas Ta Tsakiya

    Hukumomi a Masar sun ce ƙasashen da ke kusa da Tekun Maliya na da nauyin da ya rataya a wuyansu na kare shi da kuma samar da yanayi mai kyau ga jiragen ruwa.

    A ranar Talata, Amurka ta sanar da naɗa kwamitin haɗaka mai mambobi 10 da niyyar kare matsinta a Tekun Maliya daga hare-haren ƴan tawayen Houthi daga Yemen.

    Sai dai Masar da Saudiyya ba su shiga cikin haɗakar Amurkan ba.

    A ranar Alhamis, Girka ta ce za ta aika jirgin ruwan yaƙi zuwa wajen domin kare mutane.

    Jiragen ruwa mallakar Girka na da kashi 20 na hada-hadar kasuwanci da ake yi a dun

    Girka na da kashi 20 na hada-hadar kasuwanci da ake yi ta ruwa a faɗin duniya.

  9. Hamas ta harba rokoki zuwa Isra'ila

    Hamas ta yi ruwan rokoki a faɗin Isra'ila daga Zirin Gaza, kamar yadda ƙungiyar ta bayyana a shafinta na Telegram, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    An garzaya da Isra'ilawa zuwa wuraren kariya yayin da aka yi ta jin ƙarar jiniya a Tel Aviv da sauran birane daban-daban a faɗin ƙasar.

    Wani mai ɗaukar hoto na kamfanin Reuters, ya ga lokacin da Hamas ke harba rokoki a Tel Aviv - babban birnin kasuwanci.

    Babu wanda aka ruwaito cewa ya jikkata yayin da jirgi maras matuki na Isra'ila ya lalata rokoki da dama.

  10. Majalisar dattawa ta amince da naɗin alkalai 11 na Kotun Koli

    Majalisar dattawa

    Asalin hoton, Nigerian Senate/X

    A yau Alhamis, Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da naɗin alkalai 11 na Kotun Koli.

    Kwamitin majalisar kan harkokin shari'a da kare hakkin ɗan adam wanda Sanata Tahir Munguno ya jagoranta ne ya tantance dukkan alkalan 11 a ranar Laraba tare da gabatar da rahotonsa gaban ƴan majalisar.

    Tun da farko, shugaba Tinubu ne ya aika sunayen alkalan inda ya buƙaci da ta amince da naɗinsu, waɗanda kuma ƙungiyar shari'a ta ƙasa ta bayar da shawarar a naɗa su domin cike guraben alkalan da suka mutu da kuma waɗanda suka ajiye aiki.

    Cikin sabbin alkalan da aka amince da naɗinsu akwai mai shari'a Haruna Tsammani, wanda ya jagoranci zaman kotun sauraron korafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

    Sauran sun haɗa da mai shari'a Moore Adumein, mai shari'a Jummai Sankey, mai shari'a Chidiebere Uwa, da kuma mai shari'a Chioma Nwosu-Iheme.

  11. 'Ba za mu ƙara sakin ƴan Isra'ila da muke garkuwa da su ba sai an tsayar da yaƙi'

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Hamas ta ce ba za ta ƙara sakin ƴan Isra'ila da take garkuwa da su ba har sai an tsayar da yaƙi.

    Hamas ɗin ta ce ƙungiyoyin Falasɗinawa sun dakatar da shirin sakin ƙarin mutane har sai Isra'ila ta amince ta kawo karshen yaƙi a Gaza.

    A wani sako cikin harshen Larabci da Hamas ta fitar a shafin Telegram, ta ce: "Akwai matakin da Falasɗinawa suka ɗauka na ƙasa baki-ɗaya cewar babu wata tattaunawa kan musayar fursunoni da waɗanda ake garkuwa da su har sai bayan Isra'ila ta amince ta kawo karshen yaƙi."

    Ba a dai san wasu ɓangarori ne na Falasɗinawa be ke da alaka da wannan sanarwa.

    Islamic Jihad, wata karamar ƙungiya a Zirin Gaza, ita ma tana rike da wasu ƴan Isra'ila.

    Ana ci gaba da tattaunawa don cimma sabon yarjejeniya kan yaƙin a Alkahira, babban birnin Masar, duk da cewa tattaunawa da aka yi da farko ba ta cimma komai ba, inda aka ruwaito Hamas na cewa ba za su amince da wata yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin-gadi ba.

    Lokacin da aka tsagaita wuta na kwanaki shida a watan Nuwamba, an saki ƴan Isra'ila 105 da ake garkuwa da su bayan musaya da Falasɗinawa da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila.

    An yi imanin cewa har yanzu akwai ƴan Isra'ila 120 da ake rike da su a Gaza.

    Isra'ila ta sha kin amincewa da yarjejeniyar tsagaita na dindindin da Hamas, inda ministan tsaron Isra'ila Itamar Ben Gvir, ya ce tsagaita wuta kafin karya lagon Hamas da kuma mayar da dukkan waɗanda ake garkuwa da su da cewa zai zama gazawa.

  12. 'Za a ci gaba da ciyar da ɗalibai don rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta'

    ..

    Asalin hoton, FACEBOOK/BOLA TINUBU

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ba da umarnin sake maido da tsarin ciyar da ɗaliban makaranta domin magance ƙalubalen rashin zuwan yara makaranta.

    Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ne ya dakatar da tsarin bayan shafe shekaru ana tafiyar da shi.

    Sai dai a yanzu shugaba Tinubu ya ba da umarnin a farfaɗo da tsarin saboda zai taimaka wajen magance matsalolin da suka shafi ilimi.

    Ya ce idan ba a magance matsalar ba, zai yi matuƙar wahala a iya rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

    Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a wani taron yini ɗaya da aka yi.

    Ministan ya ce an yi taron ne domin samar da hanyoyin aiwatar da dukkanin tsare-tsaren da za su magance duk wasu ƙalubale da kuma yadda hukumomi daban-daban za su taimaka wajen rage matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.

  13. Yadda haɗarin mota ya yi ajalin ɗan wasa da koci a Algeria

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani haɗarin mota da ya faru a Algeria ya halaka ɗan wasa da kocin ƙungiyar ƙwallon kafa ta Mouloudia Club El Bayadh lamarin da ya tilastawa hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar ɗage dukkan wasannin da aka tsara bugawa.

    Kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya ce mai tsaron ragar ƙungiyar Zakaria Bouziani mai shekara 27 da mataimakin koci, Khalid Muftah sun mutu sanadin haɗarin.

    Ƴan wasan na hanyar zuwa Tizi Ouzou domin buga wasa da JS Kabylie ranar Juma'a lokacin da motar ɗauke da tawagar ƴan wasan ta yi haɗari kusa da birnin Tiaret da ke arewa maso yammacin Algeria, a cewar kafafen yaɗa labaran ƙasar.

    Shugaban Algeria, Abdelmajid Tebboune ta ce cikin wata sanarwa cewa ya samu rahoton ibtila'in tare da miƙa ta'aziyya ga iyalan ƴan wasan da suka rasa ransu.

    Ƙungiyar a saƙon da ta wallafa a shafukan sada zumunta ta ce sauran ƴan wasan da suka ji rauni ba sa cikin wani mummunan yanayi.

    A cewar sanarwar, hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar ta yanke shawarar dakatar da duk wasannin da aka shirya yi a ƙarshen mako.

  14. RSF ta yi iƙirarin ƙwace iko da wani gari a jihar Gezira

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Dakarun RSF sun yi iƙirarin ƙwace wani gari da wani sansanin sojoji da ke Gezira a Sudan.

    A wani saƙo ta shafin X, ƙungiyar ta ce ta "ƴantar da sansanin sojojin Sudan a garin al-Hasaheisa.

    Hakan na zuwa ne ƴan kwanaki bayan da ƙungiyar ta ƙwace iko da Wad Madani, sakamakon kwanakin da aka shafe suna yaƙi da sojojin Sudan.

    Wani kwamitinn ƙungiyar likitocin Sudan ya ce an kashe mutum 300, wasu gommai sun jikkata yayin rikici a birnin Wad Madani.

    Mutum 300,000 sun tsere daga Wad Madani tun fara rikicin a makon da ya gabata, a cewar hukumar kul;a da ƴan gudun hijra ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Ƙwace iko da jihar Gezira a Kudancin Khartoum, babban birnin Sudan zai bai wa RSF damar nausawa jihohin da ke ƙarƙashin sojoji a gabashi da tsakiya da kuma kudu maso gabashin ƙasar, kamar yadda masu sharhi suka bayyana.

  15. 'An mayar da mata tamkar ganimar yaƙi a Sudan'

  16. Kotu ta wanke Ba’amurke daga laifin kisa bayan shafe shekaru 48 a gidan yari

    ...

    Asalin hoton, NEWS9, OKLAHOMA CITY KWTV

    Mai shari'a a Oklahoma ta wanke wani mutum da ya shafe kusan rabin ƙarni a gidan yari saboda kisan kan da aka yi a 1974, hukunci mafi tsawo da aka taɓa yankewa a Amurka.

    An saki Glynn Simmons mai shekara 70 cikin watan Yuli lokacin da wani alƙali ya ba da umarnin a sake shari'a.

    Sai dai wani lauyan gudunar ya ce babu isassun hujjoji da za su buƙaci hakan.

    Mai shari'a ta gundumar Oklahoma,Amy Palumbo ta wanke Mr Simmons daga laifin.

    "Wannan kotun ta samu gwamsasshiyar hujjar cewa ba Mr Simmons bane ya aikata laifin da ya sa aka same shi da laifi har aka yanke masa hukunci aka kuma kulle shi," kamar yadda ta faɗa a hukuncin da ta yanke.

    "Wannan darasi ne na juriya da jajircewa," in ji Mr Simmons bayan hukuncin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito. "Kar ku yadda wani ya ce hakan ba za ta taɓa faruwa ba, saboda lalle zai iya faruwa."

    Mr Simmons ya shafe shekara 48 da wata ɗaya da kwana 18 a gidan yari saboda kisan Carolyn Sue Rogers lokacin wani fashi a kantin sayar da barasa a wata unguwa da ke Oklahoma. Hakan ya sa ya zama fursunan da aka wanke wanda ya fi daɗewa a gidan yari, a cewar hukumar da tattara bayanan mutanen da aka wanke daga laifi.

    Mr Simmons yana shekara 22 lokacin da aka same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin kisa a 1975.

    Daga baya an yi sassauci a hukuncin inda ya koma zaman dindindin a gidan yari saboda matakin da kotun ƙolin Amurka ta yanke kan hukuncin kisan.

  17. Kotun ƙoli za ta sanar da ranar yanke hukuncin ƙarshe kan zaɓen gwamnan Kano

    ..

    Kotun ƙoli ta ce za ta sanar da ranar da za ta yanke hukuncin ƙarshe kan shari'ar gwamnan Kano tsakanin gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP da Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC.

    Kotun ta bayyana haka ne a yau Alhamis bayan zaman da ta yi na farko kan ƙarar da gwamna Abba Kabir ya shigar gabanta.

    Gwamnan na jam'iyyar NNPP ya shigar da ƙarar domin ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya tabbatar da hukuncin kotun sauraran ƙararrakin zaɓe da ta soke nasararsa tare da bayyana Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

    A zaman kotun na yau Alhamis, Mai shari'a John Okoro, wanda shi ne jagoran alƙalan, ya buƙaci ɓangarorin da ke cikin shari'ar su samu matsaya kan ɗaya daga cikin ƙorafe-ƙorafe tara da aka ɗaukaka ƙara a kai, wanda hukuncin da za a yanke kan sa zai shafi sauran ƙorafe-ƙorafen takwas.

    Daga nan ne aka cimma matsaya kan cewa ƙorafin da za a saurara shi ne wanda ake ƙalubalantar kasancewar gwamna Abba Kabir ɗan jam'iyya ko kuma a'a.

    A watan Nuwamba ne Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, babban birnin Najeriya ta bai wa tsohon mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna kuma dan takarar APC nasara a hukuncin da ta yanke game da zaɓen gwamnan jihar Kano.

    Tun bayan hukuncin ake zaman ɗar-ɗar a jihar ta Kano, inda mutane suka rinƙa fitowa suna zanga-zangar nuna adawa da hukuncin.

    A cikin watan Maris na 2023 ne Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri'u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri'u 890,705.

  18. Babu sauran asibitocin da ke aiki a arewacin Gaza – WHO

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce babu wani asibiti da ke aiki a arewacin Gaza saboda rashin man fetur da ma'aikata da kuma magunguna.

    "Babu sauran asibitin da ke aiki a arewacin Gaza," in ji wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya a Gaza, Richard Peeperkorn,

    Asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya sun shiga wani yanayi sakamakon ƙaruwar yaƙi a sassan Gaza yayin da kuma suke fama da ƙarancin magunguna da rashin wutar lantarki.

    Bayan ziyarar da suka kai asibitin Al-Ahli, tawaga daga Hukumar Lafiya da Majalisar Ɗinkin duniya ta ba da rahoton asibitin ya cika da mutanen da ke buƙatar kulawar gaggawa, ga kuma gawawwaki yashe sahu-sahu.

    A wani saƙo ta shafin X, Shugaban hukumar lafiya ta Duniya, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce asibitin ne na ƙarshe da ke yin tiyata a arewacin Gaza amma a yanzu ɗakunan tiyatar ba sa aiki.

  19. Za mu hukunta likitocin da ke safarar ƙoda a Najeriya – Gwamnati

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta bayar da tabbacin ɗaukan mataki kan likitoci da sauran mutanen da ke da hannu a harkar safarar ƙoda.

    Jami'ar yaɗa labarai ta ma'aikatar lafiya ta ƙasar, Ms Patricia Deworitshe ce ta bayar da tabbacin cikin wata sanarwa da aka fitar jiya Laraba a Abuja, babban birnin Najeriya.

    A cewar jami'ar, gwamnati ta sanar da ƙudirinta na ladabtar da duk wanda aka kama da hannu a safarar ƙoda bayan rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa kan yadda ake yin harkar a ɓoye.

    Ta ce "ma'aikatar ta yi tir da irin wannan mummunar ɗabi'a ta safarar ƙoda kamar yadda rahoton na Daily Trust ya bayyana.

    Ma'aikatar lafiyar ta kuma tunatar da mutane game da sashe na 51 zuwa 56 na dokar lafiya ta ƙasa da ya haramta safarar ƙodar.

    "Mutanen da suka ƙi bin dokar sun aikata laifi kuma za su iya fuskantar biyan tarar naira miliyan ɗaya ko zama gidan yari ko ma duka biyun.

    Ms Patricia Deworitshe ta ce hukumar kula da aikin likitoci ta Najeriya tana duba zarge-zargen da aka yi kan likitoci da suke wannan ta'adar.

    Deworitshe ta ƙara da cewa kamata ya yi bayar da gudummawar ƙoda ya zama bisa masaniyar wanda zai ba da ƙodar tasa, kuma bisa shawarar likita.

  20. An soma ƙirga ƙuri'un da aka jefa a zaɓen Congo, Emery Makumeno daga Kinshasa

    ..

    Asalin hoton, Emery Makumeno/BBC

    An soma ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa a Kinshasa, babban birnin Congo bayan babban zaɓen da ke cike da jinkiri da iƙirarin tafka maguɗi.

    Babbar jami'ar hukumar zaɓe, Marie-France ta shaida wa BBC cewa "Ina rumfar zaɓe ta Mwinda Mopela wadda ta kasance a buɗe har zuwa safiyar Alhamis. Ta ce an samu rashin hasken wutar lantarki sannan mutane sun yi ta jira kan dogayen layuka yayin da ake ƙoƙarin sauya wasu kayan aiki da suka lalace.

    Wannan ne karon farko tun shekarar 2006 da zaɓe ya shiga rana ta biyu a wasu yankunan Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo.

    "Masu zaɓe za su ci gaba da kaɗa ƙuri'a a rumfunan zaɓen da ba a buɗe ba ranar Laraba , in ji Patricia Nyesa, wata jami'a daga hukumar zaɓen ƙasar.

    Akwai fiye da cibiyoyin zaɓe 75,000 a sassan ƙasar da ta ninka girman Faransa sau huɗu.

    ...

    Asalin hoton, Mbelechi Msochi/BBC